Abba Abubakar Yakubu

Abba Abubakar Yakubu
Chief Editor

Ƙwararren Ɗanjarida kuma fasihin Marubuci, wadda tun tasowarsa ya kasance ma’abocin son karance-karance da rubuce-rubuce.

Haifaffen garin Jos ne da ke Jihar Filato ta Tarayyar Najeriya. An kuma haife shi a ranar 13 ga watan Yuni na shekarar 1978.

Ya fara karatunsa daga makarantar allo, kamar yadda yake bisa al’adar Musulmi Hausawa. Daga bisani, ya shiga makarantar Firamare ta St Paul’s Township Primary School a nan cikin garin Jos, bayan ya kammala a 1990 kuma ya shiga makarantar Sakandiren Gwamnati ta GSS Jos. Ya yi karatun Diploma a ɓangaren sarrafa Kwamfuta,kafin kuma ya sake yin wata Diplomar a fannin aikin Jarida na talabijin, a NTA Television College Jos a shekarar 2010. Ya kuma yi Digirinsa na farko a Sashen Nazarin Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2016.

Abba, ya yi aiki da Jaridun Hausa daban-daban, a matsayin mai aikin rahoto mai zaman kansa, (freelance journalist), inda yake rubuta sharhi da rahotanni. Kamar irin su; jaridarY Gaskiya Ta Fi Kwabo, Nasiha, Aminiya, Al-Irshad, Blueprint Manhaja da sauransu. Ya kuma riƙe muƙamin Edita a Jaridar Zuma Times Hausa ta yanar gizo na tsawon wasu shekaru, kafin daga baya ya buɗe shafukansa na ƙashin kansa da yake wallafa rubuce-rubucensa a yanar gizo, da suka haɗa da shafin Hikima Online, Arewa Monitor, Daily Reports Hausa, da kuma Mujallar Alƙalami.

Yanzu haka, ma’aikaci ne a babbar tashar Talabijin ta ƙasa ta NTA, a ofishinsu da ke Jos. Ya kuma yi aiki a rassan tashar da ke Gombe da Jalingo, a Shiyyar Arewa Maso Gabas, a matsayin wakili, mai gabatar da shirye-shirye, da tsara labaru.

Bugu da ƙari, ya halarci kwasa-kwasai da dama a kan aikin Jarida da hulɗa da jama’a, da samar da zaman lafiya. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Ƴanjaridu ta NUJ reshen tashar NTA Jos. Sannan mamba ne a Ƙungiyar Ƙwararrun Masu Aikin Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR).

Mamba ne a ƙungiyar marubuta ta ƙasa ta Association of Nigerian Authors (ANA), mamba ne a ƙungiyoyin matasa da ci gaban al’umma daban-daban. Har ila yau, shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers Association ta Jihar Filato, da kuma ƙungiyar Marubuta ta Jos Writers Club.

Yanzu haka, shi ne Daraktan Cibiyar Gatekeepers Resource Centre, kuma Shugaban Makarantar Hausa Literary Academy.

📱+2347035131313
✉️ abbaabubakar@gmail.com

Suraj Idris Sai’d

Suraj Idris Sai’d
Staff

An haife shi a ranar 10 ga watan Oktoba, na shekarar 1990, a garin Kududdufawa da ke Jihar Kano, Nijeriya.

Ya fara karatun Firamare a garin Katsinawa sannan ya koma Jajira Firamare, inda ya kammala a shekarar 2005. Ya wuce Makarantar Sakandare ta Jajira daga 2005 zuwa 2011.

Ya yi Difiloma a Jami’ar Bayero da ke Kano daga 2011 zuwa 2013 a fannin Jarida. Sannan ya fara Digiri a 2014, ya kammala a 2017 a Jami’ar ta Bayero da ke Kano, duk a fannin Jarida.

Bugu da ƙari, ya fara karatun Digiri na biyu a National Open University, inda ya kammala daga 2022 zuwa 2024, a fannin Jarida.

Ya kuma samu shaidar Difiloma a fannin Kwamfuta, sannan ya samu takardar horon aiki daga gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA) a shekarar 2015.

Haka zalika, a fannin ilimin addini ya yi saukar Al-kur’ani tun a shekarar 2010 da sauran wasu littatafai na addini da dama.

A ɓangaren ayyuka, ya yi aiki da kafafen yaɗa labarai da dama, kamar haka; BUK Radio, da, Aminci Rediyo, da Arewa Rediyo, da Sawaba FM, da Arewa 24, da Labarai 24, da Amsal News, da Dimokuraɗiyya, da Kogin Wasanni, da kuma Mairiga’s Talk Show, dss.

Yanzu haka, shi ne Jami’in Yaɗa Labarai na kamfanin sarrafa Ƙarafa na Afuwa Welding Works and General Metal Construction. Sannan ƴa na aiki da gidan Rediyo da Talabijin na Muhasa, Kano.

📱 +2347038471566
✉️ surajnaiya0@gmail.com

Aminu Saidu Ahmad

Aminu Saidu Ahmad
Head Of ICT

Masanin na’ura a fannin tsarawa, kirkira da kuma sarrafa shafukan yanar gizo, hotunan zane (Graphics), Ɗanjarida kuma kwararre wajen ƙirƙirar Bidiyo.

Hafaffen garin Malumfashi a Jihar Katsina, an haife shi a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 1998.

Ya fara karatunsa na Firamare a Aliyu Primary School da ke Malumfashi a 2004 inda ya kammala a 2010. Daga nan ya shiga ƙaramar Sakandare Gwamnati wato GDJSS Malumfashi daga 2010 zuwa 2013, inda daga bisani ya koma Community Model Arabic College Malumfashi, inda ya kammala karatun Sakandare daga 2013 zuwa 2016.

Ya fara karatun Difloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic da ke garin Katsina a sashen nazarin aikin Jarida a shekarar 2017 zuwa 2020, sannan ya ci gaba da karatun babbar Difloma (HND) a wannan sashen daga shekarar 2022 zuwa 2024.

Ya yi aiki da gidan Rediyo na Jihar Kano a matsayin ɗalibi mai koyon sanin makamar aiki, inda daga bisani ya samar da Kafa mai zaman kanta wato Arewahub Media wacce daga bisani ta rarrabu zuwa Arewahub Media, ArewaHub Studios da kuma ArewaHub TV waɗanda duka sun ta’allaka ne wajen ƙirƙira, yaɗawa da kuma rarraba Bidiyo da rahotanni.

Haka zalika, ya na da manyan haɗin guiwa da wasu kafofin makamantan waɗannan.

Har ila yau, shi ne mamallakin kamfanin Zayn & Amness Consult waɗanda suka ta’allaka wajen karɓa da kuma yin ayyukan yanar gizo ko waɗanne iri, kuma Sakatare ne a kamfanin Dream-Co Global Solutions Ltd. waɗanda suke ƙirƙirar kayan gine-gine.

A baya-bayan nan kuma, ya zama daga cikin waɗanda suka samar da wata kafa ta Yi da Kanka wato (Self Service) mai suna Beyond Digital, wacce take ba kowa damar yin ayyuka daban-daban a kan yanar gizo.

📱+2349034803078
✉️aminusaidahmad@gmail.com

Fatima Shehu Kachan

Fatima Shehu Kachan
Associate Editor

An haife ta a ranar 12 ga watan Nuwamba a shekarar 2000, Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ta yi karatun Firamare a Louisiana de Price Academy Kaduna, yayin da ta yi Sakandare a makarantar Umar Ibn Khattab Model School.

Ta wuce Hukumar Ƙwadago da Ƙirƙira ta Tarayya (Federal Ministry of Labour and Productivity), inda ta mallaki shaidar karatun kammala Difloma a fannin Kwamfuta.

Bayan nan, ta kuma sake mallakar shaidar kammala karatun Difloma (ND) da (HND) a fanin aikin Jarida, duk a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kaduna.

A ɓangaren karatun addini kuwa; Ta yi saukar Alkur’ani mai girma a shekarar 2017, a Madarasatul Imamul Jazari Liltahafizul Qur’an wal Luggatul Arabia, Kaduna.

Ta samu damar halartar tarukan ƙarawa juna sani da nazari da bita daban-daban.

A fannin kasuwanci, ta kasance mai fafutuka inda take cikin Kwamitin Watsa Labarai na ƙungiyar NACCIMA Youth Entrepreneurs, reshen jihar Kaduna.

Ta fara aikin Jarida a shekarar 2020, inda a yanzu haka take aiki da Gidan Talabijin na Qausain TV.

✉️ fatimakachan@gmail.com

Kumsat M Hassan

Kumsat M Hassan
Head Of Programme

An haife ta a ranar 25th ga watan Fabrairu shekera ta 1988, a garin Bukuru, na Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, da ke Nijeriya.

Ta yi karatun Firamare da Sakandare a garin Bukuru, daga baya ta dawo Jihar Kaduna, inda ta ƙarasa karatun Sakandare a Kwalejin Queen Amina Kaduna.

Ta samu shaidar kammala karatun Difiloma a fannin Jarida, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

Ta kasance jajirtacciya kuma da sanin makamar aiki, wadda hakan ya ba ta damar samun karramawa da lambobin yabo daban-daban. Har ila yau ta halarci taruka da bita da kuma tarukun ƙarawa juna sani a matakai da dama.

Taron horo na kafar BBC Imedia (British Council) a shekarar 2012.

Taron Ƴanjaridu a kan gabatar da shirye-shirye na KADRAMP a shekarar 2014.

A shekarar 2014, ta halarci horo a kan gyara-gyaren muhalli. Har wa yau, ta halarci horo a kan cutar Sida (HIV) da kafar yaɗa labarai ta BBC ta shirya a shekarar 2015.

Ta karɓi Lambar Yabo ta Mace Mafi Kwazo a Gabatar da shirye-shirye a shekarar 2013.

Yanzu haka, ta na aiki da kafar yaɗa labarai ta Liberty Radio/TV, Kaduna.

✉️ mkhumsi@gmail.com

Nana Asma’u Lawal Liman

Nana Asma’u Lawal Liman
Director Operations and Evaluation

Wacce aka haifa a ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 2002, a Ƙaramar Hukumar Ƙaura-Namoda da ke jihar Zamfara a Tarayyar Najeriya.

Ta yi karatun Firamare a Nelson Mandela International School da ke garin Abuja, yayin da ta tafi Jihar Katsina inda ta yi Sakandare a makarantar Ulul-Albab Science Secondary School.

Har wa yau, ta kuma mallaki shaidar kammala karatun Diploma (ND) a fannin Ƙere-Ƙere (Civil Engineering Technology), a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Ƙaura-Namoda, Zamfara.

A ɓangaren karatun addini kuwa; Ta sauke Alkur’ani mai girma a 2019, ta kuma sake sauke wa a karo na biyu a shekara ta 2021.

Ta yi aiki da wasu Jaridun yanar gizo irinsu; One News Hausa, da Bakandamiya Reading Club.

Bugu da ƙari, Nana Asma’u (Queen-Nasmah), ta kasance shahararriyar marubuciya wacce ta yi shura a Duniyar Adabi. Yanzu haka, ita ce Shugabar ƙungiyar Moonlight Writers Association.

✉️ Asmaunanalawalliman@gmail.com

Aliyu Zubairu Kauru

Aliyu Zubairu Kauru
Director Strategy and Communications

An haifi Aliyu Zubairu a garin Kauru da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna, a ranar 20 ga watan Agustan 1995.

Ya halarci Model Primary School Kauru daga 2000 zuwa 2006, sannan ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kauru, inda ya kammala a 2013.

Ya samu shaidar kammala Diploma (ND) da (HND) a fannin aikin Jarida, 2014 zuwa 2019 a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, Zariya.

Haka nan, ya yi wa Kasa Hidima (NYSC), a Jihar Ekiti a shekarar 2021.

Ya fara Aikin Jarida a shekarar 2016 da Gidan Talabijin da Rediyon Jihar Kaduna (KSMC) ƙarƙashin Sashen Labarai da Al’amuran Yau da Kullum a matsayin ma’aikacin sa-kai, daga baya kuma a shekarar 2018 ya samu aiki a matsayin ma’aikaci na dindindin.

A cikin wannan lokaci, ya samu shaidar jajircewar aiki daban-daban daga Hukumar Gudanarwar Kafafen Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna bisa ƙwazonsa da sanin makamar aiki.

Bugu da ƙari, ya halarci kwasai-kwasai da taron ƙara wa juna sani da dama, inda ya samu kyautukar karramawa.

📱08102863264
✉️ alyzub4u@gmail.com

Moutari Mahamadou

Moutari Mahamadou
Director African Linguistics

An haife shi a shekarar 1986, a garin Ɗangona da ke cikin gundumar Illela Oumani, Jihar Tahoua, Jamhuriyar Nijar.

Ya fara karatunsa na Firamare a garin Dangona, bayan haka ya tafi Sakandare a Bagaruwa.

Tun da lokacin da yake karatu a Sakandare hankalinsa ya fara karkata a kan karatun Hausa da niyyar wace hanya zai bi ya ba da gudunmowa da tallafawa al’umma ta hanyar faɗakarwa.

Daga nan ne ya shiga Tarayyar Nijeriya domin domin ƙara samun ilimi da gogewa a kan ƙa’idojin rubutun Hausa da kuma karatunta.

Ya share tsawon shekaru biyu a Nijeriya a ƙarƙashin kamfanin KEZUWA, wato kamfanin da fitaccen marubucin Littattafan Hausa, Isah Rasko Ɗangoma ke jagoranta.

Bayan ya samu horo da sanin makama, ya karɓi takardar shaidar; Masanin ƙa’idojin rubutun Hausa da karanta ta. Daga nan ya koma Nijar ya fara aiki a Rediyo Sarauniya FM Ƙonni, a matsayin mai koyon aikin Jarida da harshen Hausa.

Daga nan ya tafi jihar Kano a Nijeriya, inda ya yi aiki a matsayin mai tsare-tsare da gyare-gyare (Strategy and editing) a Rediyo Freedom FM.

Bayan haka ne ya shiga fagen aikin Jarida gadan-gadan, ya yi aiki a Rediyo Horizon FM, Rediyo da Talabijin Bonferey, Rediyo da Talabijin Niger24, Rediyo da Talabijin Dunia.

Yanzu haka, ya na aiki a Studio Kalangu Foundation Hirondelle.

Sani Musa Daitu

Sani Musa Daitu
Director Admin and Finance

An haife shi a ranar 12 ga watan Aprilu na shekarar 1995, a garin Tsauni Daitu, da ke Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ya yi makarantar Allo a Tsangayar Malam Ɗallami a Tsauni Daitu. Ya fara karatun Firamare a LGEA Gidan Inji Daitu 1999 zuwa 2006.

Ya wuce ƙaramar Sakandare ta Gwamnati da ke Ƙofar Kibo Zariya 2007 zuwa 2009, inda daga bisani ya koma Government Technical College Soba (GTC Soba) 2009 zuwa 2014.

Bayan nan, ya wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli Zariya, inda ya karanci kimiyyar Kwamfuta da kuma Tsara birane da yankuna (Urban and Regional Planning).

Bugu da ƙari, yanzu haka ya na karantar sha’anin Siyasa da tafiyar da mulki (Policy and Governance), a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

A ɓangaren ayyuka da gwagwarmaya ya kasance jajirtacce, kuma fitacce a fannoni mabambanta. Saboda haka, ya halarci taruka daban-daban tare da samun karammawa da lambobin yabo bisa himmarsa.

Ya yi aiki a matsayin Wakili na Kasuwar Bello, inda ya kula da shiyyar Kaduna, Zariya da Funtuwa, daga 2016 zuwa 2019.

Wakilin Jaridar Amana Newspaper a Kaduna, daga bisani aka ɗaga likafarsa zuwa Mataimakin shugaban sashen labarai da al’amuran yau da kullum, 2020 zuwa 2022.

Ya yi aiki a Human Rights Network (HRN), inda ya riƙe Shugabanta na Ƙaramar Hukumar Zariya (Desk Officer) 2020 zuwa 2022. Har ila yau, shi ne Shugaban sashen bincike na Shiyya ta biyu (Zone 2) a jihar Kaduna.

Haka zalika, shi ne Sakataren Tsare-Tsaren na ƙungiyar Kaduna Young Jornalist Association. Har wa yau, Manajan Hulɗar Kasuwanci (BRM) a Bankin Moniepoint.

Ya kuma kasance tsohon Jami’in Hulɗa da Jama’a a Nigerian Association Chambers Of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, reshen jihar Kaduna.

Haka nan, shugaban kwamitin watsa labarai na ƙungiyar Arewa Consultative and Synergy Congress (ACSC) 2020 zuwa 2022. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Sakatare a ƙungiyar Giwa Youth Progressive Association (GYPA), inda ya zama Shugaba a 2015 zuwa 2019.

Yanzu haka, shi ne Daraktan Sadarwa na Al-Haroon College of Health Science and Technology Zaria, kuma Shugaban Kamfanin Tranquil Way Limited.

Mu’azu Sa’adu Muhammad P.h.D

Mu’azu Sa’adu Muhammad P.h.D
Director Arts and Culture

An haife shi, ranar 13 ga watan Maris, shekara ta 1964 a unguwar Tsauni Kudan, Ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ya zauna a Kano Ƙofar Nassarawa wajen wani Kakansa Alhaji Aliyu Gwarzo, inda ya yi karatun Allo daga shekarar 1969 zuwa 1972, ya dawo Kudan 1972.

Ya shiga Firamare 1973 zuwa 1979, ya wuce Sakandaren Gwamnati da ke Kagoro a ranar 24/11/1979 zuwa 15/09/1981, sai Sakandaren Gwamnati ta Maƙarfi 18/09/1981 zuwa 01/06/1984, (G.C.E).

Ya wuce Kwalejin Zurfafa Ilimi (C.A.S) Zariya daga 15/01/1985 zuwa 10/08/1987 (I.J.M.B), sai ya kama aiki da Hukumar Ba Da Tallafin Karatu ta Jihar Kaduna (Kaduna State Scholarship Board) a Sashen Kuɗi (Accounts Section) 09/02/1988 zuwa 15/02/1995.

Ya wuce ƙaro karatu Digirin farko a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato, 30/7/1994 zuwa 31/05/1998 (B.A Hausa).

Ya koma Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna (Ministry of Education) a Sashen Mulki (Admin. Section) 15/02/1995 har zuwa 2003.

Bugu da ƙari, ya wuce ƙaro ilimi Digiri na biyu (Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato) 12/09/2003 zuwa 07/09/2007 (M.A. Hausa).

Daga bisani, ya koma Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna 18/12/2003 a matsayin Malami. A ranar 31/1/2010 ya yi ritaya don ƙashin kansa, ya na da shekaru 22 a aikin Gwamnati.

Ya yi aikace-aikacen wucin gadi na koyarwa a; Sashen Remidial (KASU) Jami’ar Jihar Kaduna 2007-2008. Kwalejin Adeyemo (Ademeyo College) Kaduna 2009-2010. Kwalejin Shabab (Shabab College of Arabic and Islamic Studies) U/Dosa Kaduna 2006-2010. Kwalejin Albidaya (Albidaya College) Kaduna 2013-2014.

Ya yi sana’ar Tela na tsawon shekaru 30, 1977-2007. Ya koma ƙaro ilimi Digiri na Uku P.h.D Hausa daga 2011 zuwa 2015 a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato.

Ya rubuta Littattafai, da Waƙoƙi, da Muƙalu da dama, ga wasu daga ciki; Bahaushiyar Al’ada, Bashi a Musulunci, Maraya da Maraici, Mace Babbar Halitta, Namiji Ikon Allah, Haƙƙoƙi Abin Kulawa, Tarihin Garin Kudan, Tsufa Rigar Ƙaya, Ziyara a Musulunci, Zuciya Sarauniya Ce, Ƙuruciyar A Al’adar Bahaushe, Sana’a Sa’a, dss.

A yanzu haka shi ne Shugaban Sashen Nazarin Harshen Hausa, a Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa, Jihar Jigawa, Nijeriya.

📱+2347030803404
✉️ muazusaadukudan299@gmail.com

Salahuddeen Muhammad

Ɗanjarida, Marubuci, mai manufar bunƙasa Harshen Hausa da al’adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

An haife shi a ranar 11 ga watan Oktoba a shekara ta 1997, a garin Barnawa ta Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ya yi karatun addini a makarantar Nasrul Islam Barnawa, kafin ya shiga Firamare ta Funmi Primary School a shekarar 2004-2009, ya wuce Sakandaren Gwamnati ta Aliyu Makaman Bida 2009-2012, sai Sakandaren Gwamnati ta Rafin Guza, Kawo Kaduna, 2012-2015.

Ya wuce Kwalejin Zurfafa Ilimi (C.A.S) Zariya a 2015-2017 (I.J.M.B), inda kuma ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina a 2017-2019, inda ya yi Difloma (ND) a fannin koyon aikin Jarida. Ya yi Digirinsa na farko a sashen aikin Jarida a Jami’ar Jihar Kaduna. Har ila yau, ya na ci gaba da ɗabbaƙa karatunsa.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama a kan aikin Jarida da hulɗa da jama’a, ya kuma taɓa riƙe muƙamin Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar Arewa Consultative and Synergy Congress (ACSC) 2018-2021.

Haka nan, ya riƙe muƙamin Babban Jami’an yaɗa labarai da Hulɗa da Jama’a (Head Of Media and Publicity) na ƙungiyar ɗalibai masu karatun aikin Jarida (MACOSA) na Jami’ar Jihar Kaduna 2023-2024, kuma ya kasance mamba a ƙungiyar Kaduna Young Jornalist Association.

Haka kuma, ya yi aiki da Jaridu daban-daban a matsayin mai zaman kansa (Freelance Journalist), inda yake rubuta sharhi da aika rahoto.

Bugu da ƙari, ya yi ayyuka a kafafen yaɗa labarai da dama kamar su; Amsal News, Daily Facts Newspaper, dss, inda ya samu karramawa da lambobin yabo a fannoni daban-daban na wasu ayyuka da ya gabatar.

Yanzu haka, shi ne Mataimakin Sakatare (Deputy Secretary-General) a ƙungiyar Nigerian Association of Chambers of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, reshen Jihar Kaduna.

Har wa yau, shi ne Sakataren kamfanin Tranquil Way Limited.

📱+2348036202002
✉️ muhammadsalahuddeen@yahoo.com