Fatima Shehu Kachan
Associate Editor
An haife ta a ranar 12 ga watan Nuwamba a shekarar 2000, Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna, Nijeriya.
Ta yi karatun Firamare a Louisiana de Price Academy Kaduna, yayin da ta yi Sakandare a makarantar Umar Ibn Khattab Model School.
Ta wuce Hukumar Ƙwadago da Ƙirƙira ta Tarayya (Federal Ministry of Labour and Productivity), inda ta mallaki shaidar karatun kammala Difloma a fannin Kwamfuta.
Bayan nan, ta kuma sake mallakar shaidar kammala karatun Difloma (ND) da (HND) a fanin aikin Jarida, duk a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kaduna.
A ɓangaren karatun addini kuwa; Ta yi saukar Alkur’ani mai girma a shekarar 2017, a Madarasatul Imamul Jazari Liltahafizul Qur’an wal Luggatul Arabia, Kaduna.
Ta samu damar halartar tarukan ƙarawa juna sani da nazari da bita daban-daban.
A fannin kasuwanci, ta kasance mai fafutuka inda take cikin Kwamitin Watsa Labarai na ƙungiyar NACCIMA Youth Entrepreneurs, reshen jihar Kaduna.
Ta fara aikin Jarida a shekarar 2020, inda a yanzu haka take aiki da Gidan Talabijin na Qausain TV.
✉️ fatimakachan@gmail.com