Salahuddeen Muhammad

Director General/CEO

Ɗanjarida, Marubuci, mai manufar bunƙasa Harshen Hausa da al’adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

An haife shi a ranar 11 ga watan Oktoba a shekara ta 1997, a garin Barnawa ta Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ya yi karatun addini a makarantar Nasrul Islam Barnawa, kafin ya shiga Firamare ta Funmi Primary School a shekarar 2004-2009, ya wuce Sakandaren Gwamnati ta Aliyu Makaman Bida 2009-2012, sai Sakandaren Gwamnati ta Rafin Guza, Kawo Kaduna, 2012-2015.

Ya wuce Kwalejin Zurfafa Ilimi (C.A.S) Zariya a 2015-2017 (I.J.M.B), inda kuma ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina a 2017-2019, inda ya yi Difloma (ND) a fannin koyon aikin Jarida. Ya yi Digirinsa na farko a sashen aikin Jarida a Jami’ar Jihar Kaduna. Har ila yau, ya na ci gaba da ɗabbaƙa karatunsa.

Ya halarci kwasa-kwasai da dama a kan aikin Jarida da hulɗa da jama’a, ya kuma taɓa riƙe muƙamin Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar Arewa Consultative and Synergy Congress (ACSC) 2018-2021.

Haka nan, ya riƙe muƙamin Babban Jami’an yaɗa labarai da Hulɗa da Jama’a (Head Of Media and Publicity) na ƙungiyar ɗalibai masu karatun aikin Jarida (MACOSA) na Jami’ar Jihar Kaduna 2023-2024, kuma ya kasance mamba a ƙungiyar Kaduna Young Jornalist Association.

Haka kuma, ya yi aiki da Jaridu daban-daban a matsayin mai zaman kansa (Freelance Journalist), inda yake rubuta sharhi da aika rahoto.

Bugu da ƙari, ya yi ayyuka a kafafen yaɗa labarai da dama kamar su; Amsal News, Daily Facts Newspaper, dss, inda ya samu karramawa da lambobin yabo a fannoni daban-daban na wasu ayyuka da ya gabatar.

Yanzu haka, shi ne Mataimakin Sakatare (Deputy Secretary-General) a ƙungiyar Nigerian Association of Chambers of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, reshen Jihar Kaduna.

Har wa yau, shi ne Sakataren kamfanin Tranquil Way Limited.

📱+2348036202002
✉️ muhammadsalahuddeen@yahoo.com