Ranar takwas ga Watan Maris, na kowace shekara, ita ce Ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin ‘Ranar Mata ta Duniya.’
Dalilin ware wannan Rana a matsayin Ranar Mata, ya na komawa ne zuwa ga abin da ya faru a Ranar takwas ga watan Maris na shekarar 1857, a lokacin da wasu Mata ma’aikata a wata ma’aikatar sarrafa Tufafi da ke birnin New York na Ƙasar Amurka suka yi zanga-zanga, kan ƙarancin albashi da kuma bautar da su da ayyuka masu wahala.
Haka nan, Jami’an Tsaro sun kai musu farmaki, kuma sun yi nasarar watsa zanga-zangar, amma fafutukar ta ci gaba da wanzuwa, har ta kai ga ƙirƙirar ƙungiyar farko ta Mata ma’aikata a Ƙasar Amurka.
Sannan, a Ranar takwas ga watan Maris na shekarar 1908, Mata kimanin 15,000, sun yi tattaki a birnin na New York, domin neman a rage musu adadin awannin da suke shafe wa lokacin aiki, da gyara musu albashi, da ba su damar kaɗa ƙuri’u a zaɓuka da kuma kawo ƙarshen bautar da ƙananan Yara.
A sa’ilin da suke tattakin, su na ɗauke da kwalaye da aka zana ‘Biredi da Fure’ a jikinsu, wanda biredin ya na nufin samar musu da ƴanci da tsaro na tattalin arziki, shi kuma furen ya na nufin inganta rayuwarsu.
An ce, Mutane da dama sun rasa rayukansu a wajen wannan gwagwarmaya.
Sa’annan, a watan Mayu na shekarar 1908, Jam’iyyar Socialist Party of America, ta ayyana Ranar Lahadin ƙarshe na watan Fabrairu a matsayin ‘Ranar Mata ta Ƙasa.’ Bikin Ranar Mata ta Ƙasa na farko a Amurka ya gudana a Ranar 28 ga watan Fabrairu na 1909.
Ita kuma ‘Ranar Mata ta Duniya’ an gabatar da ita ne a wani taro da Mata ƴan gwagwarmaya suka yi a Copenhagen na Ƙasar Denmark, wadda wata ƴar gwagwarmaya ƴar Ƙasar Jamus mai ra’ayin Gurguzu wato Clara Zetkin, ta buƙaci a ƙirƙiri ranar biki ta matan Duniya domin girmama gwagwarmayar masu yajin-aiki na Ƙasar Amurka, a nan take Mata ƴan gwagwarmaya sama da 100 daga Ƙasashe 17 suka rattaɓa hannu.
Duk da cewa, a lokacin wannan taro ba a ayyana ranar bikin ba, amma bikin farko an yi shi a Watan Maris cikin ranaku mabambanta.
A 1911 a Austria da Denmark da Jamus da Switzerland an yi bikin a Ranar 19 ga Maris, wanda sama da Mutane Miliyan Ɗaya suka yi tattaki, galibinsu mata. Ba a jima ba, sai Annobar Gobara ta faru a kamfanin Triangle Waist Company, a birnin New York a 25 ga Watan Maris na wannan shekara (1911), wadda ta yi sanadiyyar mutuwar Baƙin Haure ma’aikata 146.
Abin da ya faru, ya sake jawo hankali kan irin danniya da ake yi a Ma’aikatu, kuma ya sake ƙarfafa ƙungiyoyin Mata ma’aikata da kuma ƙungiyar ƙasa-da-ƙasa ta Mata ma’aikatan Tufafi, wanda hakan ya haifar da gagarumar zanga-zanga.
Haka abubuwa suka ci gaba da faruwa har zuwa lokacin da aka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan kammala Yaƙin Duniya na biyu. Sai Majalisar ta ware Ranar takwas ga Watan Maris na kowace shekara a matsayin Ranar Mata ta Duniya, wadda hakan ya na haska Ranar gangamin Mata na farko a Ƙasar Amurka, a takwas ga watan Maris, 1857.