Aminu Saidu Ahmad
Head Of ICT
Masanin na’ura a fannin tsarawa, kirkira da kuma sarrafa shafukan yanar gizo, hotunan zane (Graphics), Ɗanjarida kuma kwararre wajen ƙirƙirar Bidiyo.
Hafaffen garin Malumfashi a Jihar Katsina, an haife shi a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 1998.
Ya fara karatunsa na Firamare a Aliyu Primary School da ke Malumfashi a 2004 inda ya kammala a 2010. Daga nan ya shiga ƙaramar Sakandare Gwamnati wato GDJSS Malumfashi daga 2010 zuwa 2013, inda daga bisani ya koma Community Model Arabic College Malumfashi, inda ya kammala karatun Sakandare daga 2013 zuwa 2016.
Ya fara karatun Difloma a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic da ke garin Katsina a sashen nazarin aikin Jarida a shekarar 2017 zuwa 2020, sannan ya ci gaba da karatun babbar Difloma (HND) a wannan sashen daga shekarar 2022 zuwa 2024.
Ya yi aiki da gidan Rediyo na Jihar Kano a matsayin ɗalibi mai koyon sanin makamar aiki, inda daga bisani ya samar da Kafa mai zaman kanta wato Arewahub Media wacce daga bisani ta rarrabu zuwa Arewahub Media, ArewaHub Studios da kuma ArewaHub TV waɗanda duka sun ta’allaka ne wajen ƙirƙira, yaɗawa da kuma rarraba Bidiyo da rahotanni.
Haka zalika, ya na da manyan haɗin guiwa da wasu kafofin makamantan waɗannan.
Har ila yau, shi ne mamallakin kamfanin Zayn & Amness Consult waɗanda suka ta’allaka wajen karɓa da kuma yin ayyukan yanar gizo ko waɗanne iri, kuma Sakatare ne a kamfanin Dream-Co Global Solutions Ltd. waɗanda suke ƙirƙirar kayan gine-gine.
A baya-bayan nan kuma, ya zama daga cikin waɗanda suka samar da wata kafa ta Yi da Kanka wato (Self Service) mai suna Beyond Digital, wacce take ba kowa damar yin ayyuka daban-daban a kan yanar gizo.
📱+2349034803078
✉️aminusaidahmad@gmail.com