Sani Musa Daitu
Director Admin and Finance
An haife shi a ranar 12 ga watan Aprilu na shekarar 1995, a garin Tsauni Daitu, da ke Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, Nijeriya.
Ya yi makarantar Allo a Tsangayar Malam Ɗallami a Tsauni Daitu. Ya fara karatun Firamare a LGEA Gidan Inji Daitu 1999 zuwa 2006.
Ya wuce ƙaramar Sakandare ta Gwamnati da ke Ƙofar Kibo Zariya 2007 zuwa 2009, inda daga bisani ya koma Government Technical College Soba (GTC Soba) 2009 zuwa 2014.
Bayan nan, ya wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli Zariya, inda ya karanci kimiyyar Kwamfuta da kuma Tsara birane da yankuna (Urban and Regional Planning).
Bugu da ƙari, yanzu haka ya na karantar sha’anin Siyasa da tafiyar da mulki (Policy and Governance), a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).
A ɓangaren ayyuka da gwagwarmaya ya kasance jajirtacce, kuma fitacce a fannoni mabambanta. Saboda haka, ya halarci taruka daban-daban tare da samun karammawa da lambobin yabo bisa himmarsa.
Ya yi aiki a matsayin Wakili na Kasuwar Bello, inda ya kula da shiyyar Kaduna, Zariya da Funtuwa, daga 2016 zuwa 2019.
Wakilin Jaridar Amana Newspaper a Kaduna, daga bisani aka ɗaga likafarsa zuwa Mataimakin shugaban sashen labarai da al’amuran yau da kullum, 2020 zuwa 2022.
Ya yi aiki a Human Rights Network (HRN), inda ya riƙe Shugabanta na Ƙaramar Hukumar Zariya (Desk Officer) 2020 zuwa 2022. Har ila yau, shi ne Shugaban sashen bincike na Shiyya ta biyu (Zone 2) a jihar Kaduna.
Haka zalika, shi ne Sakataren Tsare-Tsaren na ƙungiyar Kaduna Young Jornalist Association. Har wa yau, Manajan Hulɗar Kasuwanci (BRM) a Bankin Moniepoint.
Ya kuma kasance tsohon Jami’in Hulɗa da Jama’a a Nigerian Association Chambers Of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, reshen jihar Kaduna.
Haka nan, shugaban kwamitin watsa labarai na ƙungiyar Arewa Consultative and Synergy Congress (ACSC) 2020 zuwa 2022. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Sakatare a ƙungiyar Giwa Youth Progressive Association (GYPA), inda ya zama Shugaba a 2015 zuwa 2019.
Yanzu haka, shi ne Daraktan Sadarwa na Al-Haroon College of Health Science and Technology Zaria, kuma Shugaban Kamfanin Tranquil Way Limited.