A ranar Laraba (5/02/25) ne mabiya Addinin Kirista ke bikin Ranar Ash Wednesday – Rana mai tsarki ga Kiristoci kuma rana ta farko na azumin kwana 40 da suka ce Yesu Almasihu ya yi.
Rabaran Murtala Mati Dangora na Cocin Ecwa da ke Kano ya shaida wa Manema Labarai cewa, a wannan ranar ne mabiya addinin na Kirista musamman waɗanda ke ƙarƙashin Ɗarikar Katolika ke azumtar ranakun.
A cewarsa, Ash Wednesday Rana ce ta saduda da tuba da kuma komawa ga Ubangiji.
“Rana ce wadda za ka ga ana shafa Toka a Goshi, wannan Toka da ake shafawa a goshi alama ce ta tuba da neman gafara da neman nufin ubangiji a cikin rayuwa na waɗannan kwanaki masu tsarki guda 40.” in ji Rabaran Mati.
Ya bayyana cewa, Rana ce da ake sa ran kowane mai bi zai keɓe da addu’a zai iya cin nasara da duk hari da Iblis zai kawo a cikin rayuwa.
Me ya sa ake yin Ash Wednesday?
Malamin addinin kiristan ya ce babban dalilin da ya sa ake wannan bikin ranar shi ne a irin ranar ne Yesu ya soma azumin kwana 40.
Kuma Rana ce da ake ganin “ta alamar nasara domin kafin Yesu ya fara azumi sai da shaiɗan ya ɗauke shi zuwa cikin jeji don ya yi masa gwaji amma bai yi nasara ba”. In ji Rabaran.
Ya ƙara da cewa Rana ce ta “nasara, Rana ce da Yesu ya fi ƙarfin shaiɗan, ya yi nasara a kan gwaje-gwajen shaiɗan.”
Me ya Kamata a yi a Ranar?
Rabaran Mati Dangora ya ce a wannan Rana, ana buƙatar kowane Kirista ya duƙufa wajen yin addu’oin neman gafara da nufin ubangiji.
Ya ce, Rana ce da ya kamata kowane mai bi ya koma ga ubangiji ya nemi nufinsa a cikin dukkan lamuransa.
“Rana ce da mai bi ya kamata ya zama mai murna da farinciki da jin daɗi, ba rana ce ta takaici da baƙin ciki ba.
Yadda ake yin Azumin
Kamar yadda mabiya addinin kirsita suka ce azumin ya wajabta ne a ranaku biyu na kwana 40 – Ranar Ash Wednesday da kuma Good Friday.
Ana son mabiya a waɗannan ranakun su ci Abinci sau ɗaya a Rana.
Me ya sa ake Shafa Toka a Gaban Goshi?

Fafaroma Francis ya shafa wa mabiya da dama toka a goshi a yau. Hoto: Getty Images
A cewar mabiya, tokar da ake shafawa na nufin nuna neman yafiyar ubangiji na zunuban da mutum ya aikata.
Limanin Coci ne ke shafa wa mabiya tokar a goshi ya yi alamar Kuros.