Manufar ita ce; Gina nagartattun tsari ta hanƴar raya al’adu, ɗabbaƙa tarihi, da kuma bunƙasa yawon buɗe ido, don maido da hanyoyi na sadarwa masu wanzar da ci gaban al’umma.
Taskar Nasaba, ta wanzu ne don sake duba labaran Afirka don taskacewa, alkintawa, fassarawa, baddalawa, warkarwa, sabuntawa da sake fasali ta hanyar zamani. Ta kuma kasance ne don tunatarwa da ƙarfafa guiwa, domin gyara labara marasa tushe da haifar da bege da canji ga makomar Afirka.
Mun ƙuɗiri aniyar ganin martabar nahiyar ta dawo, kuma ta hanyar yin hakan za mu iya canja yadda ake ji ko gani game da Afirka a yau.
Lokaci ya yi da mafi kyawun Afirka zai bayyana, ta hanyar nuna martabobinta da kuma bunƙasa su.