Tafasa wacce a ka sani a Ƙasar Hausa wata ƙaramar Bishiya ce da ke da ganye Launin Kore da Fure da ƙananan ƴaƴa a jikinta.
Ita dai wannan bishiyar, ana samunta a wurare da dama a Ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya musamman a Jihohin Arewacin Ƙasar.
Tafasa ta kasance muhimmiyar Tsiri wacce take da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan’Adam, domin ana amfani da kuma sarrafa ta, ta hanyoyi daban-daban.
Haka nan, ana amfani da Ganye da Ƴayan don yin magani. Tafasa maganin Laxative ne da FDA ta amince da shi a kowane mataki.
Haka nan, ana amfani da ita don magance Ulcer da kuma Cushewar Ciki (Senna), da kuma amfani da don maganin Ciwon Ciki (IBS), da Ciwon Basir, da kuma rage Ƙiba.
Shayin Tafasa ya na ɗauke da ‘Anthraquinone,’ wanda aka sani da tasirin ‘Laxative’ mai ƙarfi. Waɗannan Anthraquinone ya na da Tasiri sosai a tsaftace Hanji, wanda yake da kyau ba kawai don ba da tsarin narkewa Abinci ba, amma har ma da shirya Hanji don hanyoyin kamar; colonoscopy.

A Ƙasar Indiya, masu maganin ‘Ayurvedic Herbal Medicines’ sun ɗauki lokaci mai tsawo su na amfani da Tafasa don yin maganin wasu kebaɓɓun rashin lafiya kamar haka:
Amfani, Muhimmanci, da Tasirin Tafasa ga Lafiyar Jikin ɗan’Adam
Maganin makanta ko matsalar da ta shafi ta gani. Baya ga wannan, matsala ta barazanar makanta, Tafasa na ƙara lafiyar Ido kama daga Yara har zuwa tsofaffi.
A don haka, sai a juri yin miyar Tafasa ana ci a Abinci domin inganta lafiya Idanu.
Wani bincike da wasu Masana Tsirran Itatuwa suka yi sun tabbatar da cewa, Tafasa na maganin wasu cutukan da ke shafuwar babbar hanzanya (Colon) da kuma taurin bahaya (constipation).
Tafasa ta na maganin zafin ciki (internal heat) da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.
Tafasa ta na rage ƙiba, don haka wannan wata dama ce ga masu Tumbi waɗanda ke buƙatar rage nauyi; sai a nemi Ganyen Tafasa a dake a tare da Gero a yi Fura a sha.
Ana amfani da Saiwar Tafasa, idan suka bushe sai a dake, su koma gari don maganin cizon Maciji.

Ana amfani da garin Ganyen Tafasa don warkar da Gyambon Ciki (ulcers).
Tafasa na maganin tsutsotsin ciki (intestinal worms).
Tafasa na maganin cutukan Fata kamar su; Ƙanzuwa da Maƙero da Ƙuraje masu ƙaiƙayi ga jiki.
Tafasa na saukar da yawan zafin jiki da hauhawar jini.
Tafasa na ɗauke da Sinadari mai suna Chrysophanic acid da Sinadarin Anthrone masu kashe ƙwayar cuta ta Fungi (wata cuta ce mai kama Kaji).
Ganyen Tafasa na inganta lafiyar Hanta (improves Liver function).
Ana amfani da Ganyen Tafasa ga Yara ƙanana a lokacin da suka soma Haƙora (childhood Teething).
Ganyen Tafasa na maganin Zazzaɓi da Ciwon Gaɓoɓin Jiki (sai a nemo Ganyen a tafasa a yi surace da ruwan ko a yi wanka da shi da sanyin Safiya ko Yamma).
Ganyen tafasa na wanke (flushin) wasu sinadaran da ke gurɓata ciki (toxins).
Ƴaƴan Tafasa na maganin cutukan sanyi kamar Tari, da Mura, musamman ga waɗanda ba sa jure sauyin yanayi kamar a lokacin Sanyi.

Wanda ya ci wani abu ko ya sha wani abu da ke da alaka da Guba (Poison) za a iya amfani garin Ƴaƴan Tafasa, nan ke zai amayar da wannan gubar a cikin lokaci kuma ba za ta illata shi ba.
Ganyen tafasa na maganin Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria).
Ganyen Tafasa na warkar da cutukan Jini (Blood disoders).
Ganyen Tafasa na maganin cutukan Ciki.
Ana amfani da garin Ƴaƴan Tafasa a markaɗe da mai sai a shafa a rauni ko kuma ƙunar Wuta.

Mai fama da Basir mai haifar da zubar jini (Bloody diarrhoea), sai ya tafasa Ganyen Tafasa ya marmasa Gishiri a ruwan ya rinƙa tsuguno a ciki na Mintuna goma ko fiye a duk san da ya je bahaya.
Mai fama da Tari sai ya ya markaɗe ganyen a ruwan zafi ya dinga sha.
Nauyi ko ciwon mara a lokacin al’ada sai a yi amfani da Tafasa.
Gargaɗi: Mai fama da gudawa ba zai sha Tafasa ba. Bugu da ƙari, Mace mai ciki ta kiyayi yadda ake amfani da Tafasa. Sannan, mai Ciwon Hanta shi ma ya kiyaye!