Kumsat M Hassan
Head Of Programme
An haife ta a ranar 25th ga watan Fabrairu shekera ta 1988, a garin Bukuru, na Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, da ke Nijeriya.
Ta yi karatun Firamare da Sakandare a garin Bukuru, daga baya ta dawo Jihar Kaduna, inda ta ƙarasa karatun Sakandare a Kwalejin Queen Amina Kaduna.
Ta samu shaidar kammala karatun Difiloma a fannin Jarida, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Ta kasance jajirtacciya kuma da sanin makamar aiki, wadda hakan ya ba ta damar samun karramawa da lambobin yabo daban-daban. Har ila yau ta halarci taruka da bita da kuma tarukun ƙarawa juna sani a matakai da dama.
Taron horo na kafar BBC Imedia (British Council) a shekarar 2012.
Taron Ƴanjaridu a kan gabatar da shirye-shirye na KADRAMP a shekarar 2014.
A shekarar 2014, ta halarci horo a kan gyara-gyaren muhalli. Har wa yau, ta halarci horo a kan cutar Sida (HIV) da kafar yaɗa labarai ta BBC ta shirya a shekarar 2015.
Ta karɓi Lambar Yabo ta Mace Mafi Kwazo a Gabatar da shirye-shirye a shekarar 2013.
Yanzu haka, ta na aiki da kafar yaɗa labarai ta Liberty Radio/TV, Kaduna.
✉️ mkhumsi@gmail.com