Mu’azu Sa’adu Muhammad P.h.D

Director Arts and Culture

Mu’azu Sa’adu Muhammad P.h.D
Director Arts and Culture

An haife shi, ranar 13 ga watan Maris, shekara ta 1964 a unguwar Tsauni Kudan, Ƙaramar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, Nijeriya.

Ya zauna a Kano Ƙofar Nassarawa wajen wani Kakansa Alhaji Aliyu Gwarzo, inda ya yi karatun Allo daga shekarar 1969 zuwa 1972, ya dawo Kudan 1972.

Ya shiga Firamare 1973 zuwa 1979, ya wuce Sakandaren Gwamnati da ke Kagoro a ranar 24/11/1979 zuwa 15/09/1981, sai Sakandaren Gwamnati ta Maƙarfi 18/09/1981 zuwa 01/06/1984, (G.C.E).

Ya wuce Kwalejin Zurfafa Ilimi (C.A.S) Zariya daga 15/01/1985 zuwa 10/08/1987 (I.J.M.B), sai ya kama aiki da Hukumar Ba Da Tallafin Karatu ta Jihar Kaduna (Kaduna State Scholarship Board) a Sashen Kuɗi (Accounts Section) 09/02/1988 zuwa 15/02/1995.

Ya wuce ƙaro karatu Digirin farko a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato, 30/7/1994 zuwa 31/05/1998 (B.A Hausa).

Ya koma Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna (Ministry of Education) a Sashen Mulki (Admin. Section) 15/02/1995 har zuwa 2003.

Bugu da ƙari, ya wuce ƙaro ilimi Digiri na biyu (Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato) 12/09/2003 zuwa 07/09/2007 (M.A. Hausa).

Daga bisani, ya koma Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna 18/12/2003 a matsayin Malami. A ranar 31/1/2010 ya yi ritaya don ƙashin kansa, ya na da shekaru 22 a aikin Gwamnati.

Ya yi aikace-aikacen wucin gadi na koyarwa a; Sashen Remidial (KASU) Jami’ar Jihar Kaduna 2007-2008. Kwalejin Adeyemo (Ademeyo College) Kaduna 2009-2010. Kwalejin Shabab (Shabab College of Arabic and Islamic Studies) U/Dosa Kaduna 2006-2010. Kwalejin Albidaya (Albidaya College) Kaduna 2013-2014.

Ya yi sana’ar Tela na tsawon shekaru 30, 1977-2007. Ya koma ƙaro ilimi Digiri na Uku P.h.D Hausa daga 2011 zuwa 2015 a Jami’ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato.

Ya rubuta Littattafai, da Waƙoƙi, da Muƙalu da dama, ga wasu daga ciki; Bahaushiyar Al’ada, Bashi a Musulunci, Maraya da Maraici, Mace Babbar Halitta, Namiji Ikon Allah, Haƙƙoƙi Abin Kulawa, Tarihin Garin Kudan, Tsufa Rigar Ƙaya, Ziyara a Musulunci, Zuciya Sarauniya Ce, Ƙuruciyar A Al’adar Bahaushe, Sana’a Sa’a, dss.

A yanzu haka shi ne Shugaban Sashen Nazarin Harshen Hausa, a Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa, Jihar Jigawa, Nijeriya.

📱+2347030803404
✉️ muazusaadukudan299@gmail.com