Moutari Mahamadou

Director African Linguistics

Moutari Mahamadou
Director African Linguistics

An haife shi a shekarar 1986, a garin Ɗangona da ke cikin gundumar Illela Oumani, Jihar Tahoua, Jamhuriyar Nijar.

Ya fara karatunsa na Firamare a garin Dangona, bayan haka ya tafi Sakandare a Bagaruwa.

Tun da lokacin da yake karatu a Sakandare hankalinsa ya fara karkata a kan karatun Hausa da niyyar wace hanya zai bi ya ba da gudunmowa da tallafawa al’umma ta hanyar faɗakarwa.

Daga nan ne ya shiga Tarayyar Nijeriya domin domin ƙara samun ilimi da gogewa a kan ƙa’idojin rubutun Hausa da kuma karatunta.

Ya share tsawon shekaru biyu a Nijeriya a ƙarƙashin kamfanin KEZUWA, wato kamfanin da fitaccen marubucin Littattafan Hausa, Isah Rasko Ɗangoma ke jagoranta.

Bayan ya samu horo da sanin makama, ya karɓi takardar shaidar; Masanin ƙa’idojin rubutun Hausa da karanta ta. Daga nan ya koma Nijar ya fara aiki a Rediyo Sarauniya FM Ƙonni, a matsayin mai koyon aikin Jarida da harshen Hausa.

Daga nan ya tafi jihar Kano a Nijeriya, inda ya yi aiki a matsayin mai tsare-tsare da gyare-gyare (Strategy and editing) a Rediyo Freedom FM.

Bayan haka ne ya shiga fagen aikin Jarida gadan-gadan, ya yi aiki a Rediyo Horizon FM, Rediyo da Talabijin Bonferey, Rediyo da Talabijin Niger24, Rediyo da Talabijin Dunia.

Yanzu haka, ya na aiki a Studio Kalangu Foundation Hirondelle.