Abba Abubakar Yakubu
Chief Editor
Ƙwararren Ɗanjarida kuma fasihin Marubuci, wadda tun tasowarsa ya kasance ma’abocin son karance-karance da rubuce-rubuce.
Haifaffen garin Jos ne da ke Jihar Filato ta Tarayyar Najeriya. An kuma haife shi a ranar 13 ga watan Yuni na shekarar 1978.
Ya fara karatunsa daga makarantar allo, kamar yadda yake bisa al’adar Musulmi Hausawa. Daga bisani, ya shiga makarantar Firamare ta St Paul’s Township Primary School a nan cikin garin Jos, bayan ya kammala a 1990 kuma ya shiga makarantar Sakandiren Gwamnati ta GSS Jos. Ya yi karatun Diploma a ɓangaren sarrafa Kwamfuta,kafin kuma ya sake yin wata Diplomar a fannin aikin Jarida na talabijin, a NTA Television College Jos a shekarar 2010. Ya kuma yi Digirinsa na farko a Sashen Nazarin Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2016.
Abba, ya yi aiki da Jaridun Hausa daban-daban, a matsayin mai aikin rahoto mai zaman kansa, (freelance journalist), inda yake rubuta sharhi da rahotanni. Kamar irin su; jaridarY Gaskiya Ta Fi Kwabo, Nasiha, Aminiya, Al-Irshad, Blueprint Manhaja da sauransu. Ya kuma riƙe muƙamin Edita a Jaridar Zuma Times Hausa ta yanar gizo na tsawon wasu shekaru, kafin daga baya ya buɗe shafukansa na ƙashin kansa da yake wallafa rubuce-rubucensa a yanar gizo, da suka haɗa da shafin Hikima Online, Arewa Monitor, Daily Reports Hausa, da kuma Mujallar Alƙalami.
Yanzu haka, ma’aikaci ne a babbar tashar Talabijin ta ƙasa ta NTA, a ofishinsu da ke Jos. Ya kuma yi aiki a rassan tashar da ke Gombe da Jalingo, a Shiyyar Arewa Maso Gabas, a matsayin wakili, mai gabatar da shirye-shirye, da tsara labaru.
Bugu da ƙari, ya halarci kwasa-kwasai da dama a kan aikin Jarida da hulɗa da jama’a, da samar da zaman lafiya. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Ƴanjaridu ta NUJ reshen tashar NTA Jos. Sannan mamba ne a Ƙungiyar Ƙwararrun Masu Aikin Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR).
Mamba ne a ƙungiyar marubuta ta ƙasa ta Association of Nigerian Authors (ANA), mamba ne a ƙungiyoyin matasa da ci gaban al’umma daban-daban. Har ila yau, shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers Association ta Jihar Filato, da kuma ƙungiyar Marubuta ta Jos Writers Club.
Yanzu haka, shi ne Daraktan Cibiyar Gatekeepers Resource Centre, kuma Shugaban Makarantar Hausa Literary Academy.
📱+2347035131313
✉️ abbaabubakar@gmail.com