An Soke Daular Musulunci a Ƙasar Turkiyya

A Rana mai Kamar ta Yau, uku ga Watan Maris, na Shekarar 1924, wadda ya yi daidai da 27 ga Watan Rajab 1342 bayan Hijra, aka soke Daular Musulunci mai shekaru 407, a ƙarkashin Shugabancin Kemal Ataturk lokacin da aka hamɓarar da Halifa Abdülmejid II na Daular Usmaniyya.
Nan take Mustafa Kemal Pasha, ya yi amfani da damarsa. A kan shirinsa ne Majalisar Dokokin Ƙasar ta soke Daular Khalifanci a Ranar uku ga Watan Maris, 1924.
An tura Abdülmejid zuwa Gudun Hijira tare da sauran ƴan Majalisar Daular Usmaniyya. An kawo ƙarshen Mulkin Daular Usmaniyya sakamakon raba Daular bisa umarnin (League of Nations)
Margaret Thatcher: Firaministan Ingila Mace ta Farko

A Rana mai Kamar ta Yau, Uku ga Watan Maris, na shekarar 1979, Margaret Thatcher ta lashe zaɓen gama-gari na Birtaniya.
Washegari, ta zama Mace ta farko a matsayin Firaminista a Birtaniya a tarihi.
An zaɓe ta a matsayin a shekarar 1979, inda ta jagoranci Jam’iyyar Conservative tun 1975, kuma ta sake lashe zaɓen fidda-gwani a 1983 da 1987.
Bugu da ƙari, ta samu karɓuwa sosai a Kafafen Yaɗa Labarai a matsayin Mace ta farko da ta zama Firaiministar Birtaniya. Ta sauka a lokacin da ta janye daga zaɓen shugabancin Conservative a 1990.
Jirgin Sama mai Amfani da Hasken Rana

A Rana mai Kamar ta Yau, uku ga Watan Maris, na shekarar 2013, wani Jirgin Sama da Ƙasar Switzerland ta ƙera mai amfani da Hasken Rana, ya sauka a Hawaii bayan da ya kammala wata doguwar tafiyar zagaya Duniya da ba a taɓa yin irinta ba.
Tafiyar da ya yi ta kan Tekun Pacific ta kasance mafi hatsari. Jirgin, wanda ya yi tafiyar nisan kilomita dubu 35, ya yi wannan shawagi ne ba tare da ko ɗigon Mai ba.
Haka nan, matuƙin Jirgin na Solar “Impulse 2,” Andre Borschberg, ya kafa sabon tarihin wanda ya yi tafiya mafi nisa wacce ta doke tarihin da Ba’amurken nan Steve Fosset ya kafa a baya.
A lokacin ya na shawagin, Borchberg ya ɗan gyan-gyaɗa na tsawon Mintuna 20 a cikin Jirgin yayin da jirgin yake sarrafa kansa.
Da farko dai, Jirgin ya tashi ne daga Nagoya, da ke Ƙasar Japan a Ranar Litinin, bayan yada zango na babu shiri na tsawon wata guda.
Wasu masana kimiyya ƴan Ƙasar Switzerland ne suka fara ƙirƙiro wannan Jirgi, wato Borschberg da Bertrand Piccard, sun kuma kwashe shekaru 12 ne su na ƙera wannan Jirgi.
Jirgin wanda yake da fukafiki na Jirgi samfurin Boeing 747, amma nauyinsa bai wuce na motar-shiga ƴar tsaka-tsaki ba.
Baturan jirgin su suke tattarawa su kuma adana ƙarfin Rana, domin jirgin ya sami sukunin tashi Dare da Rana.