Masarautu

Tarihin Masarautar Pindiga

Daga: Faruk Tahir Maigari ✍️

Pindiga, babban Birnin Masarautar Pindiga ne da ke Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Pindiga, gari ne mai cike da tarihi mai ban sha’awa wadda Jukunawa suka kafa a tsakanin ƙarni na 16-17. Ƙauyen ya fara ne da wasu tsirarun mutane da ke zaune a kan Dutse wadda a yanzu ya kasance Masarauta ta biyar mafi girma a jihar Gombe.

Pindiga, ita ce hedikwatar mulkin Masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin Masarautun Jihar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi a tsakankanin ƙarni na 16 zuwa ƙarni na 17.

Garin ya fara daga ɗan ƙaramin matsugunni na wasu jama’a a kan Dutse har zuwa bunƙasarsa kamar yadda yake a yau a matsayin Masarautar Sarkin-yanka mai daraja ta biyu a cikin jihar Gombe.

ASALI

Pindiga, Gari ne mai tsohon tarihi, asalin kafuwar wannan Gari ya na farawa daga lokacin da Jukunawa suka shigo yankunan baƙaƙe daga Ƙasar Yemen, a cikin ƙarni na 16 zuwa na 17.

Fitowar wannan jama’a daga Yemen, sun shigo ta Ƙasar Sudan ta yau, inda suka yada zango a garin Khartoum. Daga nan suka rankayo ta gefen Kogin Chadi, kama-kama har suka zo Dutsen Bima. Daga wannan Dutse na Bima ne suka rabu gida biyu; Kashi ɗaya daga ciki suka kama hanyarsu tiryan-tiryan har zuwa Dutsen Binga, inda suka kafa wani Gari wadda a yau ake kiransa da sunan “Yelwa.”

A cikin shekarar 1815 A.D. Sarkin Gombe Buba Yero, ya fara kai harin yaƙi a wannan gari na Binga. Dukkan yaƙuƙuwan da wannan Sarki ya yi da Jukunawan Binga, bai samu nasarar murƙushe su ba har ya bar Duniya.

Haka nan, aka ci gaba da wannan yaƙi har zuwa zamanin Sarkin Gombe Umarun Ƙwairanga, wadda ya haɗa rundunar haɗaka da ta tattara mayaƙa daga Ƙasashen Bauchi, Misau, Jama’are da kuma wasu garuruwan. Wannan runduna su suka yaƙi Jukunawan da ke wannan gari mai suna Binga; Yaƙi irin na ƙare-dangi. Ba su bar kowa ba sai waɗanda suka gudu suka sha da ƙyar.

Ragowar waɗannan mutane da suka fantsama uwa-duniya, su ne suka sake dawowa daga baya suka sake kafa wani garin a kan wani Dutse wadda shi kuma suka kira shi da suna ‘Khartoum.’ Sun zaɓi su kira shi da wannan suna don ya riƙa tuna musu da zaman da suka taɓa yi a garin ‘Khartoum’ wadda ke cikin Ƙasar Sudan ta yau.

Dutsen Khartoum

Bayan wani lokaci su na zaune a kan wannan Dutse mai suna Khartoum, sai suka ga cewa ya kamata su ƙara gaba, saboda haka sai suka ƙara taƙi gaba kaɗan, tazarar da ba ta haura kilomita ɗaya da rabi ba, suka sake kafa wani sabon garin a kan Dutsen Puli, wadda yanzu ake kiransa da suna Dutsen Jukun. Shi wannan Dutse ya na nan a bayan garin Pindiga.

Dutsen Jukun

Bayan Turawa sun ci Gombe da yaƙi, a shekarar 1903, sai suka sauko da waɗannan mutane daga kan wannan Dutse zuwa matsugunnin da a yanzu suke zaune a ciki; Wato garin Pindiga ke nan.

Wani sashen garin Pindiga daga kan Dutsen Jukun

MASARAUTAR PINDIGA

Masarautar Pindiga

Tun daga farko, a lokacin da hedikwatar mulkin wannan yanki na Pindiga ke zaune matsugunninta na farko; Garin Binga, ikonta ya malala har zuwa garin Gwana daga Kudu, ta Arewa kuma har zuwa garuruwan Kwami da Gadam. Sai kuma ta ɓangaren Yamma, inda ta dangana da garuruwan Fali da Kirfi. Da ta miƙe Gabas kuma ɗoɗar, sai da ta kai garin Gwani, sannan ta karkata zuwa Gabas-maso-Yamma inda ta kai har zuwa garuruwan Tangale da Wurkum.

Alaƙar da ke tsakanin Jukunawan Binga da waɗannan garuruwa da aka lissafa, alaƙa ce ta addini. Ana kuma iya tantance haka daga ɗan sauran tasirin abin da ya rage na al’adu da addini daga Bolewa, Terawa, Waja, Wurkum da kuma Tangale.

Wannan tasiri na wannan gari na Jukunawa wato Binga, ya fara disashewa a cikin shekarar 1830 zuwa 1840 inda ta koma ƙarƙashin mulkin Masarautar Gombe ƙarƙashin tutar Musulunci. An ce, wannan ta faru ne sakamakon karɓo Tuta da ɗaya daga cikin ƴaƴan sarautar Gidan ya yi mai suna Hassan daga Gombe.

Bayan ya karɓi Tutar, sai ya koma gida da nufin yaƙar ɗan’uwansa mai suna Giwa wadda a lokacin shi ke sarautar Ƙasar, sai shi Giwa ya ce, ba zai yi yaƙi da ɗan’uwansa ba. Saboda haka, sai ya ƙara gaba ya kafa garin Tudun Ƙwaya wacce a yanzu take cikin Ƙaramar Hukumar Ɓilliri da Kaltungo ta jihar Gombe. Wannan kuma ya biyo bayan karɓar Musulunci da shi Hassan ya yi, shi kuma Sarki Giwa a ta nasa ɓangaren ya ƙi karɓar addinin na Musulunci.

A farkon Ƙarni na 20 kuma; Wato a shekarar 1903, lokacin da Turawa suka ci ƙasar Gombe da yaƙi, wannan ƙasa ta Pindiga ta koma ƙarƙashin mulkin Hakimin Akko a matsayin garin Dagaci.

Tun daga wannan lokaci, Pindiga take zama a matsayin garin Dagaci har zuwa shekarar 1978, inda ta samu ci gaban da ya kai ta kujerar Hakimi a zamanin Sarki Alh. Ahmadu Shu’aibu.

A cikin shekarar 2000, zamanin Alh. Abubakar Habu Hashidu, wadda shi ne Gwamnan farar hula na farko a jihar Gombe, Allah ya albarkaci wannan Gari na Pindiga da komawa Masarauta ƙarƙashin Sarkin-yanka mai daraja ta biyu, wadda Alh. Muhammad Seyoji Ahmad ya zamar mata Sarkin farko.

Mai Martaba Sarkin Pindiga
Alh. Muhammad Seyoji Ahmad

Ke nan a taƙaice, garin Pindiga, gari ne da Jukunawa suka kafa shi a Ƙarni na 16 zuwa na 17.

Hatimin Masarautar Pindiga

Wannan Gari dai, ya fara ne daga matsugunninsa na farko mai suna ‘Binga‘ wadda yanzu ake kiransa da Yelwa, sannan bayan yaƙi ya fatattaka garin aka sake kafa wani a kan Dutsen Khartoum, sai kuma aka sake matsawa gaba aka sake kafa wani da aka kira shi da Puli, wadda yanzu kuma ake kiransa da Dutsen Jukunawa, sannan aka gangaro ƙasa aka kafa wannan gari na Pindiga wadda ya zama hedikwatar mulkin Masarautar Pindiga, wacce aka samar da ita a zamanin mulkin Gwamnan farar hula na farko Alh. Abubakar Habu Hashidu, a shekarar 2000, wacce kuma Sarkin-yanka mai daraja ta biyu, Alh. Muhammad Seyoji Ahmad, ya zamar mata Sarkin-yanka na farko kuma har yanzu yake bisa kujerar Sarauta.

Mai Martaba Sarkin Pindiga, Alh. Muhammad Seyoji Ahmad

MADOGARAR WANNAN TARIHIN

Rumbum Ilmi, Wikipedia, Northen Nigerian Publishing Company. (1970). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.

Okunna, E da Gausa, S. (2014). Adapting the Jukun Traditional Symbols for Textile Design and Production. Mgbakoigba: Journal of African Studies. Vol. 3. July, 2014

Tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad a ranar 13/02/2017 a Pindiga, Fadar Masarautar Pindiga.

Tattaunawa da Galadiman Pindiga, Alhaji Gambo Garba, a Gidansa da ke Gombe, a ranar 13/02/2017.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Masarautu

Tarihin Masarautar Katsina

Wannan rubutu da ake karantawa zai ba mu ƙarin haske game da wannan gari na Katsina. Katsina, babbar Masarauta ce,
Masarautu

Masarautar Katsinar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar

Masarautar Katsinar Maraɗi, babbar Masarauta ce mai daɗaɗɗen tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa