Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace shekara.
A cikin wata sanarwa da hukumar Yawon Buɗe Ido Ta ƙasar (Qatar Tourism) ta fitar, ta bayyana cewa, a watan Janairun 2023, an samu masu ziyarar ƙasa da ƙasa 340,000, wadda ya ƙaru da kashi 295 na duk shekara (year-on-year), yayin da a watan Fabrairu aka ba da rahoton masu ziyara 389,000, wadda ya kai kashi 406 na duk shekara (year-on-year), in ji sanarwar da Qatar Tourism ta fitar.
Tun bayan watanni Nuwamba da Disamba da aka gudanar da Gasar Cin Kofin Duniya ta Fifa (Qatar 2022), Fabrairu ita ce ta kasance mafi yawan adadin masu zuwa Qatar a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Berthold Trenkel, babban jami’in gudanarwa na hukumar Yawon Buɗe Ido (Qatar Tourism), ya ce, ƙasar ta na samun baƙi masu ziyara miliyan shida zuwa bakwai a duk shekara a wani ɓangare na tsarinta na shekarar 2030, in da yawon shaƙatawa yake bada kashi 12% cikin 100% na tattalin arzikin ƙasar (GDP).
Bikin ranar samun ƴancin kai ta ƙasar Kuwait da ranar kafuwar Saudiyya na watan Fabrairu 2023, ya ƙara yawan maziyartan da ke zuwa daga maƙwabtan ƙasashen yankin Gulf.
Har ila yau, akwai baƙin haure 86,000 daga ƙasar Saudi Arabiya, da 20,000 daga Kuwait, waɗanda suka haɗa kashi 73% cikin 100% na dukkan masu shigowa daga yankin ƙasashen Larabawa (Gulf Club Countries) da kashi 27% cikin 100% na dukkan baƙin haure daga ƙasashen duniya a watan Fabrairu.