Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da su Fulanin da kansu suka kira ‘Fulfulde.’

Sannan kuma wannan kalma ta Fillanci ko Fulatanci ta na ɗaukar ma’ana ta halayyyar Fulani ta alkunya, jarumtaka, haƙuri da makamantansu.

Amma asalin sunan nasu shi Fullo ga mutum ɗaya, jam’unsa kuma Fulɓe, yaren kuma Fulfulde.

Fulani mutane ne da suka yi fice wajen kiwon Dabbobi da kuma rayuwar daji.

Duk da cewa, a yanzu akwai wasu manyan madafun iko da Fulani suke riƙe da su a Duniya, ana kuma yi musu kallon cewa, su suka fi kowace ƙabila yawan makiyaya a Duniya.

Fulani mutane ne masu zuzzurfan ilimin addinin Musulunci tare kuma da kishinsa. Sun bayar da gagarumar gudunmowa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci tare kuma da jaddada shi musamman a Ƙasar Hausa, wadda a yanzu take cikin tarayyar Najeriya.

           SUNAYEN FULANI

Fulani su na da sunaye da dama da ake kiransu da su. Ga wasu daga ciki kamar haka;

Bahaushe ya na kiran su da Fulani a jimlance, Bafulatani kuma mutum ɗaya. Kanuri su na kiransu da Fullata, su na kuma bambance iya Fulanin Borno da Fullata Borno, wato Bafulatani ko Fulanin Borno ke nan. Bature ya na kiransu da Fulani ko Fula. Bafaranshe kuma ya ce Peul ko Peulh.

Amma sunansu na asali wadda suke kiran kansu da shi, shi ne Fulɓe, jam’u ke nan, Fullo kuma mutum ɗaya, yaren kuma su na kiransa Fulfulde. Koda yake, Abdullahi Ibn Fodiyo da kuma Muhammadu Ballo sun kira su da suna Turudbbe (تُورُدبّ) a Larabce.

                  ASALI

A bisa ruwaya mafi inganci wacce ta fito daga Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, shi ne cewa, su Fulani asalinsu daga Rumawa ne ta ɓangaren kakarsu mace sannan kuma Larabawa ta ɓangaren kakansu namiji. Wannan shi ne abin da suka ce sun ji daga kakanninsu da kuma malamansu amintattu.

Akwai wani sahabin Annabi (S.A.W) mai suna Uƙubatu, shi ne ya je garin Futa-Toro (wani yanki na ƙasashen Mauritania da Senegal a yau), garin da Fulanin suke da zama a lokacin, a zamanin da Amru Ibn Aas, yake Gwamnan Masar (Egypt) a zamanin Khalifancin Umar Ibn Khaɗɗab (RA), ya kai Jihadin Musulunci amma sai Fulanin suka musulunta ba tare da an yi yaƙi ba. Daga baya kuma Sarkin nasu ya aurar da ƴarsa mai suna Ɓajjomaggu ga shi Uƙubatu Ibn Aamir ko Uƙbatu Ibn Nafi’ ko Uƙubatu ibn Yasir.

Daga baya suka haifi ƴaƴa huɗu tare waɗanda shi Uƙubatu, ya tafi ya bar su tare da mahaifiyarsu. Saboda haka, sai suka tashi da harshen mahaifiyarsu wadda shi ne Fillanci. Wannan magana ta tashi da harshen mahaifiyar su ita ce ruwayar da Abdullahi Ibn Fodiyo ya yarda da ita.

Ana iya dubawa a cikin littafinsa mai suna Tazyinul Waraƙaati shafi na 32/33.

    RABE-RABEN FULANI

An karkasa Fulani zuwa kashi uku bisa la’akari da yanayin wurin zamansu.

      MAZAUNA GARI

Su ne Fulanin da ke zaune a cikin gari da kuma birane. Su na iya zama da kowace ƙabila su koyi yarenta, da al’adunta da sana’ointa su kuma yi auratayya a duk gurin da suka samu kansu.

Akwai kyawawan misalai game da wannan a Ƙasar Hausa, Nupe da kuma Ilori ta Jihar Kwara duk a Tarayyar Najeriya.

Wannan yanayi nasu kuma yakan sabauta su, har ma su manta da asalin harshen nasu da al’adunsu. A yau, idan ka duba baki ɗayan Ƙasar Hausa, Nupe da Kwara duk sarakunansu Fulani ne in ban da Daura kaɗai.

        FULANI MAKIYAYA

Su ne Fulanin da ake yi wa laƙabi da Bororo. Fulani ne da ke yawo daga wuri zuwa wani wurin. Ba su da takamaiman wurin zama guda ɗaya. Kullum a tafe suke su na ƙoƙarin samawa dabbobinsu na kiwo wuri mafi yalwar abinci.

Su na kiwata Shanu, Awaki, Tumaki, Kaji, Zabbi da sauransu.

     MAZAUNA ƘAUYE

Su ne Fulanin da ke zaune a ƙauye, yawanci kusa da gari wasu lokutan kuma a cikin daji su na gudanar da sana’arsu ta kiwon Dabbobi da kuma sayar da Nonon Dabbobin da Man Shanu.

Haka nan, su na rayuwa iri biyu, rayuwar Makiyaya da Manoma, sannan kuma a lokaci guda su na zaune waje guda.

   ADDININ FULANI

Fulani mutane ne Musulmi duk da cewa, ba za a rasa kason da bai kai ya tsole Idanu ba da suke yin wani addinin kamar Kiristanci da sauransu.

Ana ganin kusan sama da kashi 95% na Fulani Musulmai ne.

Fulani sun bayar da gagarumar gudunmowa wajen yaɗa addinin Musulunci da kuma jaddada shi a Yammacin Nahiyar Afrika. Tun kusan Ƙarni na biyar suka musulunta a garin Futa-Toro (Mauritania/Senegal).

Fulani Wangarawa, su suka kawo karatun Al-ƙur’ani Ƙasar Kano a zamani Sarkin Kano Ali Yaji, a shekarar 1349–1385 AD.

Sannan kuma sun taimaka wajen jaddada addinin a duk faɗin Ƙasar Hausa da maƙwabtanta a zamanin Jihadin Musulunci na Shehu Usman Ɗanfodiyo, wadda aka yi a shekarar 1803–1807 AD.

ƘASASHEN DA FULANI SUKA FI ƘARFI

Ana samun Fulani a warwatse a ƙasashen Duniya, amma sun fi yawa a ƙasashen Afrika wadda suka haɗa da: Mauritania, Ghana, Senegal, Guinea, Gambia, Mali, Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Saliyo, Benin, Burkina Faso, Guinea-Bissau, Kamaru, Chad, Côte d’Ivoire, Jamhuriyar Afrika, Laberiya, Sudan, Habasha, Masar, Libya, Maroko, Aljeriya, Tunisiya, Eritrea, Rwanda, Tanzaniya da sauran abin da ba za a rasa ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

1 Comment

  1. Avatar

    Erik

    11/10/2024

    Can I simply say what a comfort to discover somebody who really
    knows what they are discussing on the internet.
    You definitely realize how to bring an issue to light and make it important.
    More and more people ought to look at this and understand this
    side of the story. I was surprised that you’re not more popular since you surely possess the gift. https://menbehealth.wordpress.com/

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun
Tarihi

Wani Yaƙi ne Mafi Tsaho a Tarihin Duniya?

Yaƙi Tsakanin Ƙasar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa. Daga: Salahuddeen Muhammad Yaƙin shekaru 100 ya