Yawon Buɗe Ido

Madyan: Garin Annabi Shu’aib (AS)

Madyan, garin mutanen Annabi Shu’aib AS, ya na nan a Al-Bada’a, yankin Tabuk a Arewa maso Yammacin ƙasashen Larabawa a Gabashin Gaɓar Tekun Aqqba a kan Bahar Maliya.

Har ila yau, Madyan ya kasance wurin binciken kayan tarihi da ke Arewa maso Yammacin Larabawa, a yankin Tabuk, Saudi Arabiya ta yanzu. Wurin ya ƙunshi gidaje daga manyan Duwatsu wadda suka wanzu tun a shekara ta 2000 BC kafin haihuwar Annabi Isa AS.

Haka nan, ya na daga cikin wuraren da suka shahara ga Annabawa da aka aiko. Wannan wuri na musamman ya na amsa sunan Annabi Shu’aib Amincin Allah Ya tabbata a gare shi.

Bugu da ƙari, Madyan wuri ne da aka ambata a cikin Littafin Al-kur’ani da Attaura sau da dama. An kuma ambato kalmar “Madyan” sau 10 a cikin Al-kur’ani.

A bisa yaƙinin Musulmi, a nan ne aka aiko Annabi Shu’aib. Ƙabilun da suke zama a nan, ana kuma kiran su ‘Ashabu I-aykah’ domin su na fashi da kuma rashin adalci a harkokin kasuwancinsu.

Annabi Shu’aib, ya zo da saƙon Allah da fatan shiryar ga mutanen. Duk da haka, sun bijire sun ci gaba da ta’adarsu kuma daga ƙarshe girgizar ƙasa ta halaka su. Tun daga wancan lokaci har wa yau, aka yi watsi da waɗannan Gidaje da Koguna wadda babu kowa cikinsa.

Wannan Birni da aka yi watsi da shi ya ɗauki tsohon tarihin da har ma ya ri ga wanzuwar zuwan Musulunci daga Annabi Muhammad (SAW).

Masu yawon bude ido kan ziyarci wajen daga wurare daban-daban na Duniya, kuma idan kai mai son tarihi ne, to lallai ka kai masa ziyara.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Yawon Buɗe Ido

Obudu Mountain Resort: Shahararren Wurin Shaƙatawa a Najeriya

Tsaunin Obudu, (wadda a da ake kira da Obudu Cattle Ranch), wani kwari ne a rafin Oshie na tsaunukan Sankwala,
Yawon Buɗe Ido

Yawon Buɗe Ido na Samun Tagomashi a Ƙasar Masar

Harkar yawon shaƙatawa ta kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin ƙasar, wadda ta ɗauki kimanin kaso 12% na adadin