Mai Martaba, Chiefdom Agom Kachia, Mr. Zamani Dogon Yaro JP, ya naɗa Alh. Abubakar Mohammed Sakainu a matsayin ‘Wakilin Rumadan Kachia.’
Taron dai, ya gudana ne a Fadar Agom Kachia da ke Kudancin Jihar Kaduna, a Tarayyar Najeriya.
Har ila yau, taron ya samu halartar shugabanni daga fannoni daban-daban, da jami’ai masu ruwa da tsaki, da hukumomin Gwamnati, da hukumomi masu zaman kansu, da ƙungiyoyin al’umma, da sauran al’umma daga sassa daban-daban na Jihar.
A yayin da yake zantawa da wakilinmu, Alh. Abubakar Mohammed Sakainu (Wakilin Rumadan Kachia), ya nuna godiyarsa ga Allah SWT, da kuma Mai Martaba Agom Kachia, bisa wannan ragamar jagoranci da ya sallaɗa masa, ya kuma yi alƙawarin gudanar da sahihin shugabannci da samar da ci gaba ga al’ummar Rumada da yake wakilta a Masarautar Kachia.

Alh. Abubakar Mohammed Sakainu (Wakilin Rumadan Kachia).
Bugu da ƙari, ya ayyana Ranar 17, ga Watan Fabrairu a matsayin “Ranar Bikin Rumada” wadda za ta dinga gudana a kowace shekara domin inganta zamantakewa, sada zumunci, kyautata alaƙa, tattauna matsaloli, samar da mafita, da kuma gabatar da al’adun gargajiya na al’ummar Rumada.

Har wa yau a nasa ɓangaren, Mai Martaba Agom Kachia, ya yi wa al’ummar Kachia fatan alheri da kuma kira ga zaman lafiya da haɗin kan juna domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Chiefdom Agom Kachia, Mr. Zamani Dogon Yaro JP.
Daga ƙarshe, an gudanar da wasannin al’adu iri daban-daban domin samar da nishaɗi, da bunƙasa al’adu, da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.