KUNDI

Gouffre de Friouato: Kogo Mafi Girma da Zurfi a Duniya

Kogon Gouffre de Friouato (مغارة فريواطو), da ke Taza a Ƙasar Maroko, shi ne Kogo mafi girma kuma mafi zurfi a Duniya, domin babu wadda ya yi nasarar kai wa ƙarshensa izuwa yau.

Gaɓar cikin Kogon Gouffre de Friouato. Hoto: Tripadvisor

kimanin kilomita 30 Kudu da Birnin Taza na Ƙasar. Mafi zurfin bincike da aka gudanar ya na da kusan mita 272, amma har yanzu ba a san iyakarsa ba.

Wani masanin kimiyar Ƙasar Faransa ne ya gano wannan kogon a shekarar 1932.

Masana sun yi imanin cewa, ya na da kusan kilomita shida. Akwai alamun Kogi a ƙarƙashinsa da aka yi imanin cewar, ya na gudana kusa da mashigin kogon na Grottes du Chiker

Mutanen ƙauyen da ke kusa sun ce, an samu masu bincike da dama da suka ziyarci kogon, waɗanda wasunsu ba su dawo ba.

Jami’ar Exeter Speleological Society ta gudanar da balaguro a kogon har sau biyu a cikin 1969, don gano ƙarin wasu manyan saƙo-saƙo da ke cikin kogon.

Wannan bincike na iya zama wani abin buƙata ga masu binciken albarkatun ƙasa, haka nan, duwatsun da za a iya gani a ƙarshen mashigin sama na Grotte du Chiker; An gano wannan mashigin ne a shekarar 1969.

Bugu da ƙari, hotunan duka tsarin kogon an ɗauke su ne a cikin 1976 yayin balaguron da cibiyar Cerberus Speleological Society daga Burtaniya ta yi.

Bugu da ƙari, masu yawon buɗe ido na ziyartar Kogon daga sassa daban-daban na Duniya.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *