Hukumar kula da Ilimi, da Kimiyya da kuma Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ce ta ware duk Ranar 21 ga Watan Fabrairun kowace shekara, a matsayin ‘Ranar Tunawa da Harshen Uwa’ a duk faɗin Duniya.

Akwai aƙalla Harsuna 7,100 da ake magana da su a Duniya, sai dai galibinsu ba su da tsarin Rubutun Zube, domin ba a cika amfani da su shafukan sadarwa ba.
Haka nan, Hukumar raya al’adun ta UNESCO ta ce, akwai kimanin Harsuna 3,000 da ke fuskantar barazanar ɓacewa a Duniya gaba ɗaya.