John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila.
An haife shi a shekara ta 1921, sannan a wannan shekarar 2024 ya shiga cikin Kundin Bajinta na Guinness, na zama mutum mafi yawan shekaru a Duniya.
Haka nan, ya samu karɓuwa a Duniya a watan Afrilun 2024 lokacin da Kundin Guinness ya ba shi kambin ‘Mutum mafi tsufa a Duniya’ a hukumance, tun bayan rasuwar Juan Vicente Pérez Mora mai shekaru 114.