Kimiyya Da Fasaha

Shu’umar Alaƙa Tsakanin Mutane da Ƙirƙirarriyar Basira

“A matsayina na mai sha’awar wannan batu sanda nake ƙarami, wannan Fim ya sa na ni zumuɗi”

Daga: Matthew Chan-piu

Sauyin AI ya ri ga ya iso, har ya mamaye rayuwarmu, ya na shigewa dukkan lamuranmu. Hoto: Reuters

A tunani irin na Duniyar da fasahar na’urori ta yi katutu, ana kallon fim ɗin ‘Terminator’ a matsayin wani babban misali. Sunan cibiyar Duniyar Skynet, inda fasahar Ƙirƙirarriyar Basira ta kankane ƙarƙashin jagorancin Cyberdyne Systems.

Skynet, wanda asali aka shirya shi don ya ƙarfafa kariyar cibiyar Tsaro ta Sama, wato ‘Strategic Air Command,’ daga baya ta girmama har ta fara iko da Duniyar da ba a yi zato ba.

Ta karɓe iko da Duniyar halittun ‘Cyberdyne,’ sannan ta gano cewa, waɗanda suka ƙirƙire ta su ne manyan haɗari gare ta. Skynet ya ƙaddamar da Yaƙin Ƙare-dangi da burin gwagwarmayar neman mulki tsakanin ɗan’adam da Injina.

A matsayina na mai sha’awar wannan batu sanda nake ƙarami, wannan Fim ya sa na ni zumuɗi. Wannan kimiyya da aka nuna a adabin Fasahar Kimiyya, da kuma yadda aka nuna ta a Fim, da masu ƙirƙirar sun nuna yadda alaƙa za ta iya kasancewa da mu da Ƙirƙirarriyar Basira.

An nuna Duniyar da ake tunanin za ta zo, amma a zamani mai nisa. Sai dai kuma, a yau ga mu muna dab da wannan gagarumin sauyi. Sauyin AI ya ri ga ya iso, har ya mamaye rayuwarmu, ya na shigewa duka lamuranmu.

Ana tsaka da wannan batu, wata Fasahar Ƙirƙirarriyar Basira da ta yi fice yanzu ita ce – Chat GPT, ta farko a fagenta na nuna ci gaban ɗan’Adam. Ta na nuni da irin ci gaban da zai faru a gaba, a matafiyar ginuwar fasahar AI, Chat GPT ya yi zarrar da za ta daɗe ana jin ɗuriyarta.

A ƙidayar ci gaban AI, Chat GPT zai samu matsayi na musamman tamkar wani abin tsafi. Zai zamo mafari, jagora, kuma wanda ya assasa wautar ci gaba kuma ya nuna ƙarfin basirar ɗan’Adam.

Chat GPT manuniya ce ta sirrin ci gaban AI, Amma gamayyar waɗannan fasahohi da Basirar ɗan’Adam za su wuce wanda ake da su yanzu. Abu da zai faru daidai da tafiyar zamani.

A fagen tarihi, da kuma tarihin adabi, an yi ta ganin ana mayar da hankali kan ƙarfin injina da suke kwaikwayon ɗan’Adam. Mun samo sirrin abin da yake burge mu a Adabin Gargajiya. Tunanin na’urori masu magana da harshen ɗan’Adam, kuma su na gogayya da ɗan’Adam wani jigo ne da ya yi ta bayyana.

Amma kuma, an yi zaton wannan tunani ya yi wuri, har sai da aka ga zuwan Chat GPT wanda ya rusa duka wata tababa. A yau, muna iya bin tafarkin da ba a taba bi a baya ba. Abin da muke iya yi da AI ya sha kan tunani.

Duk wata mu’amala da Chat GPT da martanin da yake bayar wa, ya na kai mu fagen rushe katangar da ke raba mu da shigar da Ƙwaƙwalwar ɗan’Adam cikin Na’urori. Amma ya za mu sarrafa wannan ci gaba?

Labarin da aka nuna a Fim ɗin ‘Terminator’ na gargaɗi ne, kuma ya na nuna mana ƙarfin da haɗarin saka wa abubuwan da muke ƙirƙira wata basira. A irin wannan yanayin, dukkanmu za mu gajiya amma kuma za mu iya shiga haɗari.

Batun Chat GPT’s mafari ne kawai, kuma alama ce ta abin da zai biyo baya na Ƙirƙirarriyar Basira ba shi da iyaka. Ya na nuna mana cewa mu yi nazari kan iyakokin ginin Kwamfuta da ladubban aikinta, da nauyin da ke kan ɗan’Adam na mutuntaka.

A yayin da muke ƙarfin halin rungumar wannan sabuwar Duniya, ka da mu bari tsoro da fargaba su mamaye mu, maimakon haka, gara mu kwantar da hankali mu ci gajiyar rayuwar fasaha da muke fuskanta inda mutum da Na’ura za su shaidi wani yanayi mai ban mamaki.

Mawallafin ra’ayin Mathew Chan-Piu, marubuci ne kuma mai shirya Fina-finan da ke zaune a birnin Kampala na Uganda.

Togaciya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra’ayoyi da mahangar editocin Taskar Nasaba.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa Daga: Amina Xu An gudanar