Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa

Daga: Amina Xu

An gudanar da taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na shekarar 2024, a jiya Lahadi a birnin Wenzhou na lardin Zhejiang da ke gabashin Ƙasar Sin, inda masana kimiyya kimanin 800, daga ƙungiyoyin Kimiyya da Fasaha 63, na Ƙasashe ko yankuna 71 suka yi cuɗanya da koyi da juna a yayin taron.

A yayin jawabinsa, mataimakin babban Daraktan Majalisar Ɗinkin Duniya, kana shugaban Jami’ar MDD Tshilidzi Marwala, ya bayyana cewa, matasa masana Kimiyya na taka muhimminyar rawar gani, a fannin ingiza Kimiyya, da ke iya ba da jagoranci ga bunƙasuwar fasahohi da nazarin da ake yi, da kafa tsarin ƙirƙire-ƙirƙire a wasu yankuna, har ma da ƙara azama ga haɗin guiwar ƙasa da ƙasa.

A wajen taron, masana Kimiyya huɗu daga Ƙasashen Amurka, da Birtaniya, da Faransa da kuma Sin, sun samu lambar yabo ta matasa masu hazaƙar Kimiyya, da ke ba da gudunmowa ga samun ci gaba mai ɗorewa karo na biyu.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Yadda aka Gudanar da Babban Taron Intanet na Duniya

Daga: Abdulrazaq Yahuza Jere A rabar Larabar da ta gabata ne shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping ya miƙa saƙon taya