Al'amuran Yau Da Kullum

Netherlands za ta Mayar wa Najeriya Kayan Tarihi da Turawa Suka Sace

Ƙasar Netherlands za ta mayar wa Najeriya mutum-mutumin Tagulla 113 da Turawan Mulkin Mallaka suka sace.

An sace su ne a shekarar 1897, daga Masarautar Benin wadda yanzu take a Najeriya, inda aka rarraba su a Gidajen Ajiyar Kayan Tarihi a Netherlands.

Yayin da za a rattaba hannu a yarjejeniyar mayar da kayan tarihin zuwa Najeriya a yau, wani babban jami’in hukumar ajiyar kayan tarihi a Najeriya Olugbile Holloway ya ce, su na fatan ɗaukar wannan mataki za ta zama misali ga sauran Ƙasashe.

Ministan Al’adu na Netherlands ya ce, mayarwar ta haifar da matsin lamba ga Gidajen Ajiyar Kayan Tarihi na ƙasashen ƙetare.

Mutum-mutumin tagullan ya zama ma’aunin gwaji ko ƙasashen Turai za su mayar da kayan tarihin da aka sace.

Jamus ma ta fara mayar da tagullar zuwa Benin amma Gidan Ajiyar Kayan Tarihi na London ya ce, doka ta hana shi mayarwa.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An