Al'ada

Bikin Ranar Masoya ta Duniya

Ranar Masoya, wadda kuma ake kira ‘Saint Valentine’s Day’ ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a Ranar 14 ga Watan Fabrairu. Al’adar, ta zama gagarumar Bikin al’adu, addini, da kasuwanci da kuma soyayya a yankuna da dama na Duniya.

Akwai wata al’adar cewa, Paparoma Gelasius I, ya kafa ta a shekara ta 496AD don yin bikin Ranar 14 ga Fabrairu, don girmama Saint Valentine na Rome, wanda ya rasu a wannan Ranar, a AD 269.

Ranar Masoya ba Ranar hutu ce ta jama’a a kowace Ƙasa ba, kodayake, Ranar Biki ce a hukumance a cikin haɗin guiwar Anglican da Cocin Lutheran.

Yawancin sassan Cocin Orthodox na Gabas kuma su na bikin Ranar Valentine a Ranar shida ga watan Yuli, don girmama shugaban Roman Saint Valentine, da kuma Ranar 30 ga Yuli don girmama Hieromartyr Valentine, Bishop na Interamna (Terni ta zamani).

Asalin Bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke kan Addinin Maguzanci fiye da Ƙarni 17 da suka gabta. Haka nan, bikin ya samo asali ne daga aƙidar Romawa, cewa; wai wata Macen Kyarkeci ta taɓa shayar da Romulus, wanda ya assasa Garin Rome, Nono, kuma hakan ya ba shi ƙarfin gaske da kuma Hikima ta musamman.

Romawa sun riƙa yin gagarumin bikin murnar zagayowar wannan Rana a tsakiyar Watan Fabrairun kowace shekara.

A lokacin bikin, ana yanka Kare da Akuya, a inda ƙartin Matasa (majiya ƙarfi) za su shafe jikinsu da jinin, sannan, su wanke jinin da Madara. Daga nan, sai su jagoranci faretin zagaya Gari a kan tituna, su na riƙe da fatun da za su bugi duk wanda ya faɗo masu. Matan Romawa su na afkawa waɗannan Matasa don a buge su, kuma hakan ya na faranta masu rai saboda imanin da suka yi cewa, ya na maganin matsalar rashin haihuwa.

An ce, Valentine sunan wani malamin Kiristoci ne wanda ya mutu a dalilin cutarwar Claudius, shugaban Gothic a shekarar 296 CE.

Saint Valentine. Hoto: Brittanca

A shekarar 350 CE, an gina Coci a wurin da ya mutu, domin a riƙa tunawa da shi. Da Romawa suka shiga cikin Kiristanci, sun ci gaba da bikin Soyayya, illa iyaka, sun canja shi daga bikin Soyayyar Ruhi irin na Muguzanci zuwa bikin Shahidan Soyayya don tunawa da Valentine, kasancewar a cewar su, ya yaɗa ƙauna da Soyayya da da zaman lafiya, abin da kuma ya kai shi ga rasa ransa.

A wani ƙaulin kuma, an ce Bikin Ranar Valentine ya samo asali ne daga lokacin da Romawa suka shiga cikin Kiristanci. Sarkin Rome, Claudius II ya sanya dokar hana Sojoji yin Aure a ƙarni na uku bisa hujjar cewa, aure zai shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga yaƙi.

Valentine ya bijire wa wannan doka, kuma ya ci gaba da ɗaurawa Sojoji aure a ɓoye. Da Sarkin ya gano, sai ya jefa shi cikin Kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa. Ya na cikin Kurkuku ne ya kamu da ciwon son ƴar-sarkin, amma a ɓoye, duk da cewa haramun ne ya so wata Mace ko kuma ya yi Aure, a matsayinsa na babban malamin Kirista, kasancewar dokokin Kiristanci sun hana.

An ce, daga baya Sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar Kiristanci, ya bauta wa Gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi ɗaya daga cikin makusantansa kuma ya aurar masa da ƴarsa.

Kasancewar Valentine ya ƙi yarda da haka, an kashe shi a Ranar 14 ga Fabrairun 270 CE, a Daren 15 ga watan Fabrairu da aka saba yin bikin ‘Lupercalis.’

Daga nan aka canja sunan bikin ya koma Ranar tunawa da Valentine, ko dai saboda dagewar da ya yi a kan Kiristanci, ko kuma saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka faɗa cikin soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.

Daga nan, sai Pope, Shugaban Kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da Ranar 14 ga Fabrairun 270 CE a matsayin Ranar Bikin Soyayya, kuma ya shar’anta wa dukkan Kiristoci murnar zagayowar wannan Rana a kowace shekara.

Da ma Allah (Maɗaukaki) Ya ba da labarin yadda Kiristoci ke ɗaukar malamansu a matsayin abin bauta, da yadda su ke bin abubuwan da suka halarta ko suka haramta masu sau da kafa, ba tare da neman dalili a cikin littafinsu ba.

Abubuwan Lura Dangane da Ranar Valentine

Asalin Bikin Ranar Valentine daga Romawa ne waɗanda ke bin aƙidar Maguzanci. A wajensu, biki ne da ke nuna soyayyar da su ke wa gunkinsu mai suna ‘Ubangijin Soyayya.’

Tarihin wannan biki a wajen Romawa ya ƙunshi Tatsuniya da Surkullen da duk wani mai hankali zai ƙaryata, ballantana kuma Musulmin da ya san abin da ya ke yi. Hatta ma a wajen Kiristoci, akwai saɓani mai yawan gaske a tsakanin malamansu dangane da gaskiyar alaƙar Valentine da wannan biki.

Biki ne da ya ƙunshi kamanceceniya da mushirikan Romawa da kuma tarayya da kiristoci. Yin kamanceceniya da Kafirai ko tarayya da su a cikin addininsu ko aƙidarsu ko ibadarsu ko wata al’ada da ta keɓanta da su, haramun ne kamar yadda manyan malaman Musulunci suka bayyana.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan