Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na Jamhuriyar Nijar.
Wasu samari ne sanye da kayan kwalliya na gargajiya za su taru cikin sahu su na raye-raye da rera waƙa, don fafatawa a ƙoƙarin ɗaukar hankalin ƴan mata.

Guérewol, na faruwa a kowace shekara yayin da makiyayan Wodaabe ke taruwa a kudancin Hamadar Sahara kafin su yi ƙaura zuwa Kudu a wuraren kiwonsu na rani.

Shahararriyar wurin haɗuwar ita ce Ingall, da ke Arewa maso Yammacin Nijar, in da ake gudanar da gagarumin bikin al’ada, da harkar kasuwanci, da tarurrukan dangi na ƙabilar Wodaabe da na Abzinawa makiyaya.

Ana kiran ainihin taron raye-rayen da “Yaake,” yayin da sauran abubuwan da ba a san su ba kamar; Yin cinikin sadaki, gasa ko tseren Raƙuma a tsakanin masu neman aure suke zama a cikin bukukuwan Guérewol na tsawon mako guda da ake gudanarwa.

Ana gudanar da bikin Guérewol a duk in da ƴan ƙabilar Wodaabe suka yi zango, tun daga birnin Niamey (babban birnin ƙasar), har zuwa wasu wurare. Wodaabe sun fantsama har zuwa arewacin Kamaru da Najeriya.

Kaɗe-Kaɗe da raye-rayen da ake yi na al’adun Fulani ne, waɗanda galibi suka shuɗe a tsakanin ɗimbin al’ummar Fulani, waɗanda yawancinsu masu ilimi ne da koyar da kyawawan al’adun Musulunci.

Ana gudanar da wannan raye-raye da waƙe-waƙe a cikin rukuni, tare da tafawa, takawa da doka ƙararrawa.

Bikin Wodaabe Guérewol, ya na ɗaya daga cikin mashahuran misalan wannan salo na ɗabi’a, da al’adun waƙa, tare da raye-raye, in da maza suke haɗa hannu da tashi da faɗuwa a kan yatsunsu domin nuna bajinta.
Bikin Guérewol ya ƙunshi samari abokai yayin da suke aiwatar da rawar “Yaake” a cikin layi, yayin da suke fuskantar budurwa, wani lokaci kuma ana maimaitawa tsawon kwanaki bakwai, kuma na tsawon sa’o’i a ƙarshen ranar a cikin Sahara.

Masu neman aure su na zuwa sansanin matar don tabbatar da buƙatarsu, jarumtarsu, da amincinsu.

Masu raye-raye sukan sha wani ruwan tsumi don ba su damar yin rawa na tsawon lokaci ba tare da jin kasala ba.
Al’adar Guérewol ta zama abin sha’awar yawon buɗe ido na ƙasashen waje tun daga fina-finan yamma, kuma mujallu irin su “National Geographic” sun fito da hotuna masu salo-salo na wannan ƙayataccen biki.