Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan lamurran yau da kullum. Ra’ayin da ke cikin maƙalar na wanda ya rubuta ta ne, ba na Taskar Nasaba ba.
Lefe wata al’ada ce da al’ummar Hausawa suke gunanarwa a lokacin da ake shirye-shiyen yin aure musamman auren fari tsakanin saurayi da budurwa.
Gidan saurayi da danginsa da abokansa sukan hada karfi da karfe su samar da kaya kala-kala na zamani kuma na alatu masu tsada wadanda suka hada da kayan sawa irin su atamfa da leshi da dogayen riguna da kayan kwalliya da takalma da akwatuna da makamantansu domin kai wa gidan su budurwa wacce za ta zama amarya.
Wannan al’ada dadaddiya ce da ke gudana a cikin al’ummar Hausawa da ma sauran kabilu da Hausawa ke mu’amala da su a yankin Arewacin Najeriya da ma wadansu kasashe, musamman kabilun Fulani da Kanuri wato Bare-bari da Shuwa da makamantansu.
Wadansu mutane suna ganin cewa wannan dadaddiyar al’ada ta lefe tana da amfani kuma kyakkyawa ce, saboda haka ya kamata a habbaka ta, a inganta ta, a kuma rike ta da muhimmanci.
A wani bangaren, wadansu mutanen suna ganin wannan al’ada a matsayin mummuna wadda take cutar da al’umma musamman samari da ma ‘yan mata da rayuwar aure.
Saboda haka ya kamata a yi watsi da ita musamman a wannan zamanin.
Sai dai abin la’akari da shi a nan shi ne, yanke hukunci kai-tsaye ba tare da nazarin hujjoji da kalaman kowane bangare ba, zai iya haifar da mummunar fahimta wadda ba za ta zama alheri ba ga al’adun Hausawa a wannan zamani.
Idan muka kalli bangaren farko za mu iya fahimtar cewa wannan al’ada ta lefe ta na samar da kayan sawa ga yarinya da danginta da ma ƙawayenta.
Waɗannan kayan wani lokacin ba a iya samarwa mace irin su bayan an yi aure domin wahalhalun yau da gobe.
Lefe wata dama ce da ake samarwa mata kaya da za su taimaka musu su yi wata rayuwa ta ‘yan shekaru a cikin aure ba tare da bukatar sutura da kayan kwalliya da takalma ba wajen miji.
Wannan za su ragewa namiji wani nauyi. Amma lefen bai ɗauke nauyin yin sitira gaba daya ba.
Sannan yunƙuri da samar da kayan lefe lokacin aure yana tunatar da samari da shirya su domin su kara gane cewa ita rayuwar aure tana bukatar jajircewa da ƙwazo musamman wajen namiji.
Wannan al’ada tana nuna mana cewa rayuwar aure da za a shiga ta bambanta da rayuwar dandali wacce take cike da soyayya da kwalisa da kyawawan kalamai amma da karancin wahala wajen sayen kayan sawa.
Ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron wani tsohon shirin Adikon Zamani da aka yi hira da Dr Zahra’u Umar kan matsayin lefe a Musulunci:
Haka kuma kayan lefe suna koyawa saurayi cewa kayan sawa da kwalliya da kwalisa domin amfanin amarya da ma danginta wani nauyin ne a kan namiji bayan an yi aure. Ma’ana lefe zai nuna cewa, tufatarwa hakki ne a kan namiji ba na mace ba ne domin mace ba ta yi wa saurayi kayan lefe.
Wannan al’ada tana kara fito da irin kayan ado da alatu da al’ummar Hausawa suke da su kuma, ta ka girmama a zamunna da dama.
Mu lura da cewa, bayanan da suka gabata, ba sa nuna rayiwar aure ta dogara kacokan a kan lefe, amma tana da muhimmanci ga rayuwar aure ta kuma nuna hakurin da mutane suke da shi wajen auren ta hanyar samar da kayan lefe.
Har ila yau, lefe yana taimakawa rayuwar aure, yana da tasiri wajen kara dankon soyayyar aure da kara kima da kauran miji a bangaren mata da danginsu.
Lefe ‘Kan Hana Aure‘
A bangaren masu gani cewa lefe wata al’ada ce mummuna suna la’akari da yadda wadansu iyaye da ‘yan mata suke tsangwamawa samari kan abubuwan da za a saka a cikin lefe. Sukan kalli lefe a matsayin wata dama da za a tatse aljihun saurayi kafina aure.
Wannan yakan sa samari ba za suyi aure ba. Yakan kawo lalata ‘yan mata da kuma jefe rayuwar aure cikin garari musamman idan namiji ya je ya ciyo ba shi domin samar da kayan lefe.
Namiji zai dauki wani lokaci mai tsawo yana kokarin biyan bashi kudin ko kaya da yaka ciyo bashi domin sayen kayan lefe.
Ma’ana lefe wata hanya ce ta takurawa da tatse tattalin arzikin samari da danginsa da jefa maza je ciki gararumin bashi da tashin hankali.
Lefe yakan kawo sanadiyyar fasa aure da saki da rashin zaman lafiya a auren da aka tsawwala wajen lefe. Lefe wata hanyar kasuwanci ce da gidan mata suke amfani da ita domin takurawa samari.
Har ila yau ana ganin lefe a matsayi al’ada maras kyau domin tana kawo rashin fahimta tsakinin dangin amarya da ango. Rashin fahimtar takan shafi ‘ya’ya da jikoki da ma wadansu mutanen har bayan a yi aure.
Kallon wadannan hujjoji daga bangarne lefe a matsayin kyakkyawa da mummunar al’ada, zai bayyana mana cewa lefe ya fi zama al’ada mai kyau a kan akasin hakan.
Idan har al’ummar Hausawa za ta ci gaba ta wannan al’ada da kuma gyara kura-kuren da suke cikin ta, lefe zai taimaka matuka wajen samar da rayuwar aure mai inganci da haifar da zaman lafiya a cikin al’umma.