Garin Ségou na Mali ya karɓi baƙuncin Bikin Al’adu na Ségou karo na 21, mai taken “Yalwar Al’adu, Zaman Lafiya da Haɗin-kai.”

Bikin Ségou na gudana ne a Kudu maso Tsakiyar Mali.
Daga: Firmain Eric Mbadinga da Franck Noudofinin a Ségou
Bikin Ségou, ɗaya ne cikin mafi girman bukukuwan Al’adu a Mali, ya na gudana a karo na 21 a bakin Kogin Niger, don karrama al’adun Kaɗe-Kaɗe da fasahohi na Afirka.
Masu sha’awar Zane-Zane da masoya Al’adun Afirka sun hallara a garin Ségou, a Kudu maso Tsakiyar Mali, don bikin na tsawon kwanaki biyar, wanda aka fara ranar Litinin.
Garin ya na da mazauna 150,000, kuma an ƙawata shi. Wurin bikin ya sha ado da kaloli masu jan hankali, don birge baƙi da ƴan kallo da maziyarta.
A duk faɗin garin, an yi wa gidaje fenti an kuma rubuta saƙonnin maraba cikin harsunan gida da kuma Faransanci.
Wani saƙon Faransancin na cewa “Ségou Art 2025. Semaine de l’africanité de l’AES.”

Masu buga ganga sun nuna bajintarsu a wajen Bikin Ségou.
Taken bikin na wannan shekarar shi ne “Yalwar al’adu, zaman lafiya da haɗin-kai.”
Ya na gudana ne da haɗin guiwar Semaine de la fraternité (Brotherhood Week) wadda ƙungiyar Alliance of Sahel States (AES) ta shirya.
Bikin wannan shekarar ya gayyato Mawaƙa, masu ƙere-ƙere, masu zayyana, masu sassaƙa, da masu alkinta ayyukan Fasaha daga Burkina Faso, Nijar, Mali da sauran ƙasashen Afirka.
Za su yi bikin ɗaukaka al’adun Afirka mabambanta ta hanyar fasaha don ƙarfafa danƙon zaman lafiya haɗin-kai da yake riƙe al’ummomi a yankin Sahel tsawon ƙarnoni.

An gudanar da bikin mutum-mutumi a wani ɓangare na bikin na Ségou.
A Ranar farko ta bikin a yi rawar Matum-Mutumi ana kaɗa Ganga a layukan Rue El Hadj Oumar Tall, wata Gunduma da a nan ne Hedikwatar Festival sur le Niger Foundation take.
Yacouba Magassouba wani Mamba ne na kamfanin Nama daga Mali. Mai shekaru 30, ya ce ya na alfahari da haɓaka al’adun ƙasarsa a gida.
Ya na cike da gamsuwa da yadda bikin ya gudana.
“Aikinmu shi ne mu sarrafa waɗannan manya-manyan mutum-mutumin. Kafin bikin ya fara, mun yi kamfe don gayyato mutane,” in ji Yacouba da yake magana da Kafafen Yaɗa Labarai.
Wata ƴar rawa Kadidja Tiemanta daga Burkina Faso ta na fatan cewa yunƙurin wayar da kai na Yacouba da sauran masu shirya bikin zai janyo hankalin mutane da dama zuwa halartar bikin.
Ta na da shirin taka rawa na zaratan ƴan rawa wanda ita kaɗai ta san su.
Shi ma Yacouba ya na da fatan cewa bikin zai samar da kyakkyawar alaƙar mutane da bikin.
Ta shaida cewa, “Ganin cewa wannan shekara an saka al’adu a batun wannan bikin, ina fatan hakan zai yi tasiri gare mu.”

Bikin Ségou
Djibril Guissé, Babban Jakadan Bikin Ségou’Art – da kuma hukumomin Mali su na fatan karɓar baƙuncin dubban maziyarta a bikin wannan shekarar.
Maziyarta su na da zaɓin su nemi kalar abincin da suke so, kamar as Mafé du Mali ko su sha shayi a tantin Buzaye.
Baya ga waɗannan, mahalarta bikin za su shiga taron maƙaloli da aka shirya kamar kan batun ‘Gina haɗaɗɗiyar Ƙasar Sahel: damarmaki da ƙalubale.’
Ga masoya kaɗe-kaɗe, sun ri ga sun ga yadda Mawaƙa kamar su Mamar Kassey daga Nijar, Salif Keita daga Mali, Alif Naaba daga Burkina Faso da Lamine Diabaté daga Guinea, masu salon ƙida kala-kala irin na balafon, ganga, da Kora.
An ƙirƙiri Ségou’Art – a 2004 don nuna mawaƙan Mali, sannan a wannan shekarar an haɗa shi da lamuran ƙawancen makon AES don amfanar da al’uammar mawaƙa, masu sassaƙa, da sauran ƙwararru da ke nuna tsantsar Afirka.