A Rana Mai Kamar ta Yau, 11 ga Watan Fabrairu na shekarar 1977, aka fitar da sabon takardar Kuɗi na Naira Ashirin (N20).
Gabatarwa a lokacin ya zama dole a sakamakon ƙaruwar kuɗaɗen shiga a cikin Kasar; da fifiko ga tsabar Kuɗin ma’amaloli da kuma buƙatar sauƙaƙawa, ita ce mafi girman daraja da aka gabatar a lokacin.
Kuɗin N20 ta zama Takardar Kuɗi na farko a Najeriya mai ɗauke da hoton ɗan Najeriya.
