Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.

Ana amfani da ranar ce domin wayar da kan jama’a game da illar rashawa a matakai daban-daban na rayuwa. Har ila yau, ya na ƙarfafa jama’a su yi aiki da sababbin hanyoyin magance da nufin samun nasara a yaƙin da cin hanci da rashawa.

Ana kuma bayyana Cin Hanci da rashawa a matsayin rashin gaskiya ko zamba. Wasu kuma ana bayyana Cin Hanci da Rashawa a matsayin Cin Zarafi da Cin Amanar Mulki don cimma wata manufa ta sirri.

Galibi masu riƙe da madafun iko na amfani da Cin Hanci da Rashawa domin cimma burinsu. Cin hanci da rashawa na zuwa ta fuskoki da dama.

Cin Hanci da Rashawa da almubazzaranci kaɗan ne daga cikin laifukan da ke da alaƙa da Cin Hanci da Rashawa.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, ana biyan Dala Tiriliyan ɗaya a matsayin Cin Hanci a duk shekara. Waɗannan laifuka sun Haɗa da satar kusan Dala Tiriliyan 2.6 a duk shekara ta hanyar Cin Hanci da rashawa.

Waɗannan ƙididdiga sun kai sama da kashi 5 na GDP na Duniya gaba ɗaya.

Ƙasashen da suka fi cin hanci da rashawa a Duniya sun haɗa da;

  • Libya
  • Afghanistan
  • Guinea-Bissau
  • Sudan
  • Koriya ta Arewa
  • Yemen
  • Siriya
  • Somaliya.

Tarihin Ranar Yaƙi da Cin Hanci na Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da yarjejeniyar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a ranar 31 ga Oktoba, 2003.

A yayin taron, Majalisar ta ware ranar 9 ga watan Disamba a matsayin ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa da Ƙasa.

Taken Ranar ta Bana

Taken na bana shi ne “Haɗin Guiwa Tare da Matasa don Gyara Gobe.”

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Rasuwar Sarkin Kano Alh. Abdullahi Bayero

A Rana mai kamar ta yau 23 ga Disambar 1953, Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, ya rasu, wanda shi ne