Kiwon Lafiya

Motsa Jiki Sau Ɗaya a Wata Guda na Inganta Ƙwakwalwar Mutane – Bincike

Daga: Tasallah Yuan

Wani nazari da aka ɗauki tsawon shekaru ana gudanarwa a Ƙasar Birtaniya ya nuna cewa, ko da motsa jiki sau ɗaya kacal a wata guda Baligai suke yi, hakan zai kyautata ƙwarewar ƙwakwalwarsu ta fannonin koyo, da adana muhimman abubuwa da dai sauransu, a lokacin da aka tsufa, tare da rage haɗarin kamuwa da cutar ƙarancin basira.

Masu nazari daga Kwalejin Jami’ar London ta Birtaniya, sun ƙaddamar da rahoton nazarinsu da ke nuna cewa, a cikin gomman shekaru da suka gabata, sun gudanar da nazari kan Mutane 1417 har sau biyar, ciki har da wasu Mata da yawansu ya kai kashi 53 cikin ɗari. Dukkan waɗannan mutane an haife su ne a mako guda a shekarar 1946.

An gudanar da nazarin ne yayin da shekarunsu suka kai 36, 43, 53, 60, 64 da 69 a Duniya, dangane da yadda suke Motsa Jiki a lokacin hutu, sa’an nan an binciki ƙwarewarsu ta koyo da adana muhimman abubuwa.

Masu nazarin sun binciki yadda waɗannan Mutane sukan Motsa Jiki kullum cikin wata guda kafin a yi binciken, kamar yin Rawa, da yin wasan Yoga, da Hawan Dutse, da yin wasan Ƙwallon Raga, da wasan Ninƙaya, da wasan Kwallon Kafa, da Sassarfa, da motsa jiki na kwanciya ruf da ciki, da dai makamantansu.

Masu nazarin sun raba mutanen zuwa rukuni uku, wato rukunin marasa Motsa Jiki, da na masu Motsa Jiki sau ɗaya zuwa huɗu a cikin Wata guda, da na masu Motsa Jiki har sau aƙalla biyar a Wata guda.

An jarraba ƙwarewar waɗannan Mutane, dangane da ƙwarewarsu ta koyo da adana muhimman abubuwa, da koyon sabbin kalmomi, da daidaita bayanai ta Idanu.

Masu nazarin sun gano cewa, duk waɗanda suka Motsa Jiki a mabambantan shekarunsu guda biyar da aka bincika, ya fi samun ƙwarewar koyo, da adana muhimman abubuwa, da ilimi da kuma daidaita bayanai yayin da shekarunsa suka kai 69 a Duniya.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, yadda aka fara Motsa Jiki bayan da aka Balaga, wato ta hanyar riƙa Motsa Jiki kullum, ya na da muhimmanci ga kiyaye lafiyar Kwakwalwa. Duk wanda ya daɗe ya na Motsa Jiki a duk tsawon ransa, ya fi cin gajiyar kiyaye ƙwarewar koyo da adana abubuwa.

A iya cewa, idan ana tsawaita lokacin Motsa Jiki, to, an fi samun ƙwarewar koyo, da adana abubuwa a lokacin da aka tsufa.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kiwon Lafiya

Ko Kun San Ƙwaƙular Kunne na Haifar da Matsalar Ji?

Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi. Kunnuwanmu na da mahimmanci
Kiwon Lafiya

Yin Barci da Kyau Yakan Tsawaita Tsawon Rai – Bincike

A kan ce, yin barci da kyau a Dare ya na taimakawa wajen tsawaita tsawon rai. To, ko mene ne