Saniyar mai suna ‘Viatina-19 FIV Mara Movéis’ Fara ce mai launin dusar ƙanƙara, kuma ta na da nauyin kilogiram 1,100.
An sayar da Viatina-19 Saniya nau’in ‘Nelore’ daga Brazil a kan Kuɗi Dala Miliyan Huɗu (4.8M$), wanda ya sa ta zama Saniya mafi tsada a Duniya.
Viatina-19, ta na riƙe da Kundin Tarihin Duniya na Kundin Bajinta na Guinness World Record, saboda kasancewarta Saniya mafi tsada, kuma an ba ta Lambar Yabo ta ‘Miss South America’ a Gasar Zakarun Duniya.
Yanzu haka dai, Saniyar na cikin matakan tsaro na Kyamarori har da Jami’an Tsaro da Makamai da ke gadinta tare da Likitan Dabbobi na musamman.