Kiwon Lafiya

Yin Barci da Kyau Yakan Tsawaita Tsawon Rai – Bincike

A kan ce, yin barci da kyau a Dare ya na taimakawa wajen tsawaita tsawon rai. To, ko mene ne ma’anar yin barci da kyau?

Daga; Tasallah Yuan

Masu nazari daga Kwalejin Ilimin Likitanci i na Jami’ar Harvard sun ƙaddamar da rahoton nazari a kwanan baya, wanda ke cewa yin barci da kyau ya haɗa fannoni guda biyar, wato tsawon lokacin barci ya kai Awanni bakwa zuwa takwas a kowane Dare.

A kan shiga barci ba tare da wata matsala ba a lokacin Dare a kowane mako aƙalla sau biyar. Yawan farkawa daga barci a tsakar lokacin barci ba ya wuce sau biyu a kowane mako. Ba a sha maganin barci don shiga barci.

A kan ji kuzari bayan tashi daga barci da Safiya aƙalla kwanaki biyar a kowane mako.
Masu nazarin sun tantance bayanai daga takardun tambayoyi da mutane fiye da dubu 172 suka rubuta, waɗanda suka shiga binciken lafiyar Amurkawa daga shekarar 2013 zuwa ta 2018.

Matsakacin shekarun waɗannan mutane ya kai 50 a Duniya, an ɗauki shekaru fiye da huɗu ana bibiyarsu, inda wasu fiye da 8600 suka mutu, ciki har da wasu fiye da 2600 da suka rasu sakamakon cutar magudanar jini a Zuciya, yayin da wasu kusan 2100 suka rasu sakamakon ciwon kansa.

Masu nazarin su na ganin cewa, an danganta mutuwar kashi 8 cikin kashi 100 na waɗannan matattu da rashin yin barci da kyau.

Ta la’akari da cututtukan da suka sha fama da su, masu nazarin sun gano cewa, mutanen da suka cika waɗannan fannoni biyar na yin barci da kyau da muka ambata a baya, haɗarin mutuwa da suke fuskanta ya fi ƙanƙanta da har kaso 30 bisa ɗari, ƙasa da na waɗanda ba su cika sharuɗɗan ko ɗaya ba, ko kuma suka cika sharaɗi ɗaya kacal.

Masu nazarin sun yi ƙarin bayani da cewa, idan mutane sun kyautata yin barci da kyau da Dare, to, za su samu raguwar barazanar mutuwa. Ba za a samu tsawon rai ba, har sai an yi barci isashshe, a yi barci da kyau, a shiga barci ba tare da wata matsala ba, kana a kiyaye yin barci a duk Dare ba tare da farkawa ba.

Dangane da lamarin, Madam Zhang Chuji, Likita da ke aiki a Asibitin Tiantan na Beijing ta yi bayani da cewa, ya fi dacewa kowa da kowa ya fito da kyakkyawar al’adar yin barci tun daga lokacin ƙuruciya, kana a gano matsalar barci tun da wuri, da samun jinya tun da wuri, a ƙoƙarin rage haɗarin mutuwar wuri. Ga matasa kuma, abu mai muhimmanci gare su shi ne su fahimci cewa, a fito da wasu kyawawan ɗabi’un Kiwon Lafiya a kwana a tashi.

A kan ce, ba a makara da fara motsa jiki. Haka lamarin yake, ba a yin sammako wajen fara ɗabi’ar samun barci mai kyau.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kiwon Lafiya

Ko Kun San Ƙwaƙular Kunne na Haifar da Matsalar Ji?

Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi. Kunnuwanmu na da mahimmanci
Kiwon Lafiya

Motsa Jiki Sau Ɗaya a Wata Guda na Inganta Ƙwakwalwar Mutane – Bincike

Daga: Tasallah Yuan Wani nazari da aka ɗauki tsawon shekaru ana gudanarwa a Ƙasar Birtaniya ya nuna cewa, ko da