Kiwon Lafiya

Ko Kun San Ƙwaƙular Kunne na Haifar da Matsalar Ji?

Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi.

Kunnuwanmu na da mahimmanci ga lafiyarmu, amma duk da haka, galibi ba mu kula yadda ya kamata.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar uku ga watan Maris a matsayin “Ranar ji ta Duniya” don faɗakar da al’umma muhimmancin kula da jinsu.

Taken bikin ranar ta bana shi ne “sauya tunanin mutane game da matsalar ji” – domin an gano akwai wani tunanin da mutane suke da shi wanda ke ƙara haifar da matsala ga jinsu.

Wata ƙididdiga ta Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna cewa; Aƙalla Mutum Miliyan 430 ne a faɗin Duniya ke fama da matsalar da ta shafi rashin ji, inda kuma a Najeriya fiye da mutum Miliyan 20 ke fama da wannan matsalar.

Alƙalumman sun nuna cewar, yawan mutanen da ke da matsalar ji a Duniya ya na ƙaruwa kusan kullum.

Kuma masana sun ce, galibi mutane ne ke yi wa kunnuwansu illa ba tare da sun sani ba ta hanyar bin wasu hanyoyi da ba su dace ba musamman ƙoƙarin cire dattin kunne ko idan sun ji sauyi ko ƙaiƙayi a kunnen.

Bisa shawarar Likita, ka da ka taɓa koƙarin tsaftace cikin kunnenka ta hanyar amfani da auduga ko yatsa ko cusa wani abu – domin ya na da hatsarin haifar da matsalolin ji ko ma fasa dodon kunne.

SHIN AKWAI DATTIN KUNNE?

Galibin Mutane kan yi amfani da wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.

Ana amfani da Audugar Kunne da murfin Biro da karen Ashana ko Tsintsiya wajen cire dattin kunne.

Amma a cewar Dr. Mustapha Sa’idu ƙwararren Likitan Kunne da Hanci da kuma Maƙogaro a Asibitin Murtala da ke Kano a Najeriya, “Allah ya halicci kunne ne yadda zai dinga goge kansa da kansa saboda haka ba a buƙatar mutum ya riƙa saka wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.”

Ya ce, kunne ya na da wani maiƙo wanda ke halittar kansa da ke taimakawa lafiyar kunnen.

“Abin da ake gani kamar datti idan an saka auduga ko wani tsinke –maiƙo ne ba datti ba ne wanda ke ba da kariya ga kunne da ke kare datti da hana ƙura zuwa ga dodon kunne.”

“Maiƙon ya na sa kunnen yin daɗi. Kunne yakan yi ƙaiƙayiyi saboda wata kwayar cuta amma kuskure ne saka wani abu a kunne da nufin cire datti,” in ji likitan.

Likitan ya ce ƙoƙarin cire maiƙon a lokacin da yake aikinsa na ƙara lafiyar kunnen zai iya haifar da matsala.

ILLAR SAKACEN KUNNE

Mutane da dama na gani kamar amfani da abin audugar sakacen kunne ba ya da matsala amma kuma ya na da illa da har zai shafi jin mutum, a cewar Dr. Muhammad Sani, shugaban kwamitin gangami kan ranar ji ta Duniya a Najeriya, kuma ƙwararre a Babban Asibitin Kunne da Hanci da Maƙogoro a Kaduna.

Ya ce, babbar matsala ce da kan iya faruwa ga yara da kuma manya.

“Cusa auduga ko tsinke a kunne kan iya huje gangan kunnen ya sa jin mutum ya ragu,” in ji likitan.

Dr. Mustapha Sa’idu na Asibitin Murtala a Kano ya ce, cusa audugar kunne ko marfin biro suna da hatsari da ke lahani domin suna iya fasa dodon kunne.

Ya kuma ce, datti na iya fitowa da kansa amma amfani da audugu da nufin goge kunne kan iya tura dattin can cikin kunnen.

A cewar likitan goge maiƙon ya na da matuƙar illa a Kunne.

“Idan aka daɗe ana ƙwaƙular Kunne zai sa ya bushe domin maiƙon da ke cikin Kunne ya na da amfani ya na kare fatar kunnen daga bushewa kuma kariya ne ga kwayoyin cuta.”

“Ko wanka mutum ya fito ba daidai ba ne ya dinga sa audugar kunne ya na ta goge Kunne domin ya na illata kunnensa ne,” in ji shi.

A cewarsa, ana iya saka yatsa idan ma kumfa ne a kunnen zai fito amma ba a saka tsinke ba ko auduga domin kunne ya na wanke kansa da kansa.

Likitan ya ce kunne na yin ƙaiƙayi ne saboda wata kwayar cuta amma kuskure ne cusa wani abu a kunne.

Masana na ganin idan har kunnen mutum ya na ciwo ko yawan ƙaiƙayi abin da ya fi dacewa shi ne ya gaggauta zuwa Asibiti a duba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kiwon Lafiya

Yin Barci da Kyau Yakan Tsawaita Tsawon Rai – Bincike

A kan ce, yin barci da kyau a Dare ya na taimakawa wajen tsawaita tsawon rai. To, ko mene ne
Kiwon Lafiya

Motsa Jiki Sau Ɗaya a Wata Guda na Inganta Ƙwakwalwar Mutane – Bincike

Daga: Tasallah Yuan Wani nazari da aka ɗauki tsawon shekaru ana gudanarwa a Ƙasar Birtaniya ya nuna cewa, ko da