Al'amuran Yau Da Kullum

Masar za ta Buɗe Babban Gidan Tarihi na Zamani

Gidan adana kayan tarihin na zamani ya samu yabo daga ƙasashen Duniya, sannan ya lashe babban Kambin ‘Versailles’ daga hukumar UNESCO a 2024, inda ta amince da shi a matsayin waje mai kyawun tsari da gini.

Waɗanda suka shirya wajen sun ce, maziyarta za su ga kayan tsohuwar Masar da babu irin su a wani waje. Hoto: GEM

Masar ta ce, ya kamata masu sha’awar Zane-Zane da Sassaƙa a Afirka da ma sauran nahiyoyi su zo su shaida, sabuwar Duniyar adana al’adu da baje-kolinsu, a yayin da aka sanar da ranar ƙaddamar da Babban Gidan Tarihi na Zamani na Masar.

A Ranar uku ga watan Yuli, Masar a hukumance za ta ƙaddamar da Babban Gidan Adana Kayan Tarihi na Masar, wanda ke da girman sukwayamita 500,000, ninki biyun wajen da aka gina Gidan Adana Kayan Tarihi na Louvre da ke Paris kuma ninki biyu da rabi na Gidan Adana Kayan Tarihin Birtaniya, in ji masu shirya waje a wani saƙo ta shafin X.

Gidan Adana Kayan Tarihin na babban waje mai girman 500,000 sukwayamita. Hoto: GEM

Dr. Ahmed Ghoneim, Shugaban Hukumar Kula da Gidan Adana Kayan Tarihi mai girma na Masar, ya kira wajen da sunan ‘Bigiren tarihi da aka sadaukar ga saƙafar tsohuwar Masar.’

“Kwanaki 100 ke nan da na fara wannan aiki, kuma a yayin da ake tunkarar lokacin buɗe wajen, ina jin alfahari da sauke nauyi,” Ghoneim ya shaidawa manema labarai.

Ana sa ran ɗaukar kwanaki da dama ana ƙaddamar da gidan adana kayan tarihin. Hoto/ GEM

Babban Gidan Adana Kayan Tarihin na Masar, na nan a kan Tsaunukan Giza, kuma ya na kusa da Tuddan Pyramid da ke kusanci da Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Sphinx na Ƙasa da Ƙasa.

Ghoneim ya ce, bikin zai haura na kwana guda, inda akwai yiwuwar a ɗauki kwanaki ko ma makonni ana yin sa, ana kuma kashe ƙwarƙwatar idanuwa da kayayyaki na Ƙasa da Ƙasa.

“A yanzu muna shirin abubuwa da dama, kuma bikin na iya ɗaukar tsawon kwanaki – wataƙila kwanaki uku, ko ma Watanni da dama. Kamitocin manyan mutane na tattauna waɗannan tunane-tunane ƙarƙashin jagorancin Ministan Yawon Buɗe Ido da Al’adu, sannan kuma a ƙarƙashin kulawar Firaminista.” in ji Ghoneim.

An kashe Dala Biliyan 1.2 don gina gidan adana kayan tarihin. Hoto: GEM

Tun ma kafin ƙaddamar da shi, Gidan adana kayan tarihin na zamani ya samu yabo daga Ƙasashen Duniya, ya kuma lashe babban Kambin ‘Versailles‘ daga hukumar UNESCO a 2024, inda ta amince da shi a matsayin; Waje mai kyawun tsari da gini.

Gina wannan waje na tarihi na bayyana zuba jarin kuɗaɗe da yawa, inda Ghoneim ke cewa, an kashe Dala Biliyan 1.2, wanda Dala Miliyan 750 ranto su aka yi, Gwamnatin Masar kuma ta cika sauran.

A waje mai girman sukwayamita 500,000, Gidan Adana Kayan Tarihin zai zama daya daga cikin mafi girma a Duniya. Hoto: GEM

Masu kula da wajen sun kuma bayyana cewar, bikin buɗe wajen zai zama aikin Masar kawai, bayan nasarar manyan taruka irin su: Faretin Masarauta a watan Afrilun 2021, da ƙaddamar da Filin Jirgin Saman Sphinxes a Luxor, shi ma a 2021.

Girman Gidan Adana Kayan Tarihin ya kai sukwayamita 500,000, ya fi gidajen tarihi na Louvre da Birtaniya girma.

Waɗanda suka shirya wajen sun ce, maziyarta za su ga kayan tsohuwar Masar da babu irin su a wani waje, da ma kambin Sarki Tutankhamun.

Wane sashe a cikin gidan adana kayan tarihin. Hoto: Egypt Time Travel

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'amuran Yau Da Kullum

Qatar: Yawon Buɗe Ido na Bunƙasa a Gabas ta Tsakiya

Ƙasar Qatar ta sami kusan baƙi 730,000 a watan Janairu da Fabrairu na shekarar 2023, ƙaruwar kashi 347 a kowace
Al'amuran Yau Da Kullum

Mutum Mafi Tsufa a Duniya ya Mutu!

John Alfred Tinniswood ya mutu ne ranar Litinin a gidan kula da tsofaffi na Southport da ke Ƙasar Ingila. An