Masu shirya taron sun bayyana cewa, Kalankuwar ta na nuna muhimmancin waƙoƙin Jazz wajen wanzar da zaman lafiya da adana al’adu da mutunta ɗan’Adam.

Fitaccen mawaƙin Jazz na Najeriya, Femi Kuti da takwaransa na Amurka, Herbert Hancock su na cikin manyan baƙi a taron raƙashewar. Hoto: Femi Kuti
Daga: Charles Mgbolu
Nau’in waƙar Jazz, wadda ɗaya ce daga cikin fitattu na’ukan Waƙoƙi, na ƙara samun karɓuwa bayan Mawaƙan ɓangaren sun shirya taron Kalankuwar Waƙoƙin na Duniya, wato; Ranar Waƙar Jazz ta Duniya.
Domin karrama ɓangaren Waƙar, UNESCO ta shirya tarukan Kaɗe-Kaɗe da Raye-Raye daga Ranar 27 zuwa 30 ga watan Afrilu a birnin Tangier da ke Arewa maso Yammacin Maroko.
Darakta-Janar na UNESCO, Audrey Azoulay ya ce, ana murnar Ranar Waƙen Jazz ta Duniya a Ƙasashe sama da 190, amma a Ƙasar Maroko aka shirya taron na bana a madadin Kasashen Duniya.
Taron ya ƙara “Bayyana tarihin waƙoƙin Jazz a birnin, sannan ya ƙara fito da alaƙar al’adu da ke tsakanin Maroko da Turai da Afrika,” kamar yadda sanarwar UNESCO ta bayyana.
Taron, wanda ya samu haɗin guiwar Ma’aikatar Al’adu ta Maroko, ya kuma ƙunshi tarukan ƙara wa juna sani ga ɗalibai, inda aka gabatar da maƙalu a kan muhimmancin Waƙen Gnawa na Maroko da kuma alaƙarta da Waƙar Jazz.

Fitattun Mawaƙan Jazz na Afrika sun nishaɗantar da mahalarta taron. Hoto: Others
Gnawa, fitaccen nau’in Waƙa ce a Maroko da ke haɗa Waƙoƙin Baka da Waƙoƙi da Raye-Rayen al’adu.
Babban abin da ya fi ƙayatarwa a taron shi ne, yadda dukkan fitattun Mawaƙan ɓangaren na Duniya, irin fitaccen Mawaƙin Gnawa, Abdellah El Gourd daga Maroko, da Richard Bona daga Kamaru, da Moreira Chonguiça daga Mozambique, suka raƙashe a tare.
Waƙar Jazz na ƙara samun karɓuwa a faɗin nahiyar Afrika, inda ake ƙara samun Ƙasashen da suke shirya taron Kalankuwar Waƙar.
A shekarar 2022, an shirya babban taron Kalankuwar Waƙar a birnin Legas da ke Najeriya, inda Mawaƙan bangaren na Afrika da Duniya suka taru a Legas domin bikin Ranar Waƙar ta Duniya.
Ghana da Afirka ta Kudu ma sun taɓa shirya tarukan nishaɗin, inda dubban mutane suka halarta.
Ranar Waƙar Jazz ta Duniya da UNESCO ta assasa a shekarar 2011, ya shiga cikin Kundin Ranakun da Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ke sane da su.

Hugh Ramapolo Masekela, fitaccen Mawaƙin Jazz ne daga Afirka ta Kudu. Hoto: Getty Images
Masu shirya taron sun bayyana cewa, Kalankuwar ta na nuna muhimmancin waƙoƙin Jazz wajen wanzar da zaman lafiya da adana al’adu da mutunta ɗan’Adam.
A cewar UNESCO, Ranar Waƙar Jazz ta Duniya ta samu karɓuwa a Duniya, inda sama da Mutum Biliyan biyu, suke shiga taron duk shekara ta hanyar shirya tarukan nishaɗi a zahiri da kuma a Gidajen Rediyo, da Talabijin da sauran Kafofin Sadarwa, da Ayyukan Gayya da sauransu.
Ƙungiyar Waƙoƙin Jazz ta Herbie Hancock Institute of Jazz ce UNESCO ta ɗaura wa alhakin tsarawa da shirya Ranar Waƙar Jazz ta Duniya duk shekara.