Rana Kamar Ta Yau

Rana Kamar ta Yau: Turawa Sun ci Kano da Yaƙi

A Rana mai Kamar ta Yau, uku ga Watan Fabrairu rikicin Dakarun yankin Yammacin Afirka, a ƙarƙashin jagorancin Turawan Ingila suka ci Kano da Yaƙi.

A cikin 1899, Lord Lugard ya shelanta Mulkin Mallaka na Birtaniya a kan yawancin Daular Sakkwato. Kanar Thomas Morland (daga baya Laftanar-Janar) ya jagoranci kai wa Kano hari tare da Jami’an Burtaniya 37, Sajan Bature ɗaya, Farar Hula 16 na Turawa da kuma Sojoji 1,060 na Sojojin Yammacin Afirka, daga sansanin su da ke Zariya

A hanyar su ta zuwa Kano, Morland (wanda ake yi wa laƙabi da mai madubi) ya fuskanci turjiya a Bebeji amma Sojojinsa suka ci ƙarfin Bebeji, inda suka kashe Sarki Jibir da wasu daga cikin Hakimansa.

A Ranar Talata uku ga Fabrairu, 1903, Sojojin Morland suka isa Kano, sun ci gaba da yin luguden-wuta na sa’o’i kafin su kutsa cikin Ƙofar Kano. Aƙalla Mutane 300 ne suka faɗa hannun mayaƙan Morland a lokacin da suke kare Kano a fafatawar.

Sojojin Dawaki na Morland da ke kan Dawaki da na ƙafa suka shiga cikin birnin zuwa Fadar Sarki.

An shaida musu cewa, Sarki Aliyu Babba (Mai Sango) ya bar Kano da Mahayan Dawaki kimanin 1,000 a Ranar biyu ga watan Fabrairu.

Bayan faɗuwar Sakkwato a Ranar 15 ga watan Maris, 1903, jami’an kan iyakar Ingila da Faransa sun kama Sarkin Kano Alu a kusa da Illela, Sakkwato, ya na ƙoƙarin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

An kai shi Zungeru (babban birnin Arewacin Najeriya a lokacin), a ƙarshe a Lokoja ya rasu a matsayin Fursunan Siyasa a 1926.

MADOGARA

London Daily News (Asabar 22 Agusta 1903), Aberdeen Press and Journal (Alhamis 28 ga Mayu 1903)

Illustrated London News (Asabar 01 Agusta 1903), London Evening Standard (Talata 31 Maris 1903)

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani