Rai Dangin Goro

Tarko: Labarin Ɓera da Sauran Ƴan’uwansa Dabbobi

Daga cikin raminsa, Ɓera na kallon sa’adda maigida ke ta cuku-cukun haɗa masa tarko. Da ya gama sai Ɓera ya fito ya nufi wajen Zakara a firgice ya ce, “Abokina ka taimake ni, an sanya mini tarko a gidan nan.”

Zakara ya kaɗa fiffike ya yi shewa ya ce, “Ina ruwan maza da wankan jego? Me ya sha mini kai da tarkon da aka sa maka, ɓarnarka ce ta jawo maka.”

Ɓera ya wuce wurin Zomo ransa a ɓace ya ce, “Dan’uwana ka taimake ni, an ɗana mini tarko a gidan nan.”

Zomo, ya harare shi ya ce, “Wane ne ɗan’uwan naka? Kai dai nemi su Jaɓa da Gafiya.”

Ɓera ya ce, “Ko da ba jinsinmu ɗaya ba, ai dukkanmu dabbobi ne, ya kamata mu haɗa kai mu tunkari matsalar da ta doso ɗaya daga cikinmu.”

Zomo ya ce, “Wuce ka ba ni wuri! Maganinka ke nan ai, ɓuruntunka ne ya janyo. Idan jifa ta wuce kaina, to ta faɗa kan kowa ma.”

Cikin takaici Ɓera ya nufi wajen Rago ya ce masa, “Dan’uwa ka taimake ni, an haƙa mini tarko.”

Rago ya yi dariya ya ce, “Af, to me ya haɗa Kifi da Kaska kuma? Kai, ni raba ni da zancen kawai, in ka ƙi ko yanzu ina murje ka! Tafi ba ni wuri.”

Ɗanɓeran nan ya koma cikin raminsa cike da taikaicin yadda sauran dabbobi suka baɗa masa ƙasa a ido.

Can cikin Dare sai aka ji kararaf! Tarko ya kama.

Ɗan maigidan ya zabura da sauri ya fita don ya cire gawar Ɓera daga tarkon. Ashe Maciji ne ya jefa wutsiyarsa ciki. Yaro na zuwa Maciji ya sare shi, aka ɗauke shi kamar tsumma sai Asibiti. Ɗan nan kuwa shi ke nan, ƙwallin ƙwal, ga uban.

Da safiya ta yi, maigida ya sa aka kama Zakara aka yi wa yaro dabge.

Bayan kwana biyu kuma aka yi farfesun Zomo, aka kai wa yaro ya sha lagwada.

Da aka sallami yaro daga asibiti, saboda farin ciki, uban ya sa aka murƙushe Rago aka yanka, aka yi abinci aka raba wa maƙota sadaka.

Duk wannan kicimilli da aka yi a gidan, Danɓeran nan na cikin raminsa kwance ya na kallon ikon Allah.

Ya ce a ransa, “Da sun taimake ni mun kawar da tarkon, da abin da ya faru duka bai faru ba. Matsalar da ta doshi ɗaya, za ta iya game duka.”

Ƙurungus………!

Shin wani darasi kuka ɗauka cikin wannan labarin?

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rai Dangin Goro

Tatsuniya: Ƙarya Fure take ba Ƴaƴa

Ga ta nan, ga ta nanku! An ce wata mata a wani ƙaramin Ƙauye ta jima tare da mijinta amma
Rai Dangin Goro

Dar Gnawa: Mawaƙan Maroko Sun Zama Jakadun Yankin Maghreb

Gidan tarihi na Dar Gnawa Museum da ke birnin Marrakech na Maroko ya na cike da tarin abubuwa da suka