Rai Dangin Goro

Tatsuniya: Ƙarya Fure take ba Ƴaƴa

Ga ta nan, ga ta nanku!

An ce wata mata a wani ƙaramin Ƙauye ta jima tare da mijinta amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan buƙata ba, sai suka yi haƙuri.

Ana nan, wata rana matar ta je Gona ta na Noma, sai ta ji kukan Yaro a gindin wata Bishiya. Da ta matsa kusa, sai ta ga wani Jariri a cikin tsumma. Sai ta ɗauke shi ta goya, ta kuma ɗauki Fartanyarta, ta koma Gida.

Da mijinta ya dawo sai ta ɗauko Jariri ta kawo masa, ta ce da shi: “Da ma ina da kwantaccen ciki, shi ne yanzu ka ga na haihu a Gona.”

Mijin ya yi shiru, ya na tunani, sai ya ce: “An ya kuwa ke ce kika haifi jaririn nan?” Ta dage cewa ita ce ta haife shi. Sai ya ce: “To mun gode wa Allah.”

Suka ci gaba da renon Yaro, amma duk sanda suka je Gona da shi sai ya yi kuka ya hana su aiki. Da matar ta ga haka na faruwa kullum, sai ta je cikin danginta ta ɗauko ƙanwarta domin ta riƙa renonsa idan sun tafi Gona ita da mijinta.

Wata rana mai gida da matar suka tafi Gona suka bar yaro a hannun mai reno, mai renon ta ga yaron ya rikiɗa, ya zama babban mutum, sai ya yi aman ƴan mata 12. Ya buɗe Rumbu, kuma ya fito da Hatsi suka sussuka suka niƙa, sai ya kwashe garin ya barbaza shi a tsakar gidan; sai kuma ya haɗiye ƴan matan, ya rikiɗa ya koma ƙaramin Yaro.

Can da mai gida da matar suka dawo, suka ga ɓarnar da aka yi musu, sai matar ta kama ƙanwarta da duka wai ta yi mata ɓarna. Yarinya ta ce ba ita ba ce, yaron ne. Sai yayarta ta ce: “Ta ya ya wannan ƙaramin yaro zai buɗe Rumbu, ya ɗebo Hatsi, ya sussuka shi, ya niƙe ya zubar?” Ba su dai yarda da bayanin yarinyar ba.

Haka dai, kullum idan sun fita sai ya yi wata ɓarna, kuma sai matar nan ta doka ƙanwarta.

Wata rana matar ta kama ƙanwarta ta na duka a kan ɓarnar da yaron ya yi, sai wata tsohuwa ta kira ta ta ce mata: “Wannan duka da kike yi wa ƙanwarki fa ba ta da laifi. Wannan yaron da yake gidanku ba ki sani ba tsohon Aljani ne kika kawo gidan.”

Mamaki da tsoro suka kama matar, amma sai tsohuwar ta ci gaba da bayaninta ta na cewa: “Idan kina so ki tabbatar, gobe ka da ku je Gona; bayan gari ya waye ku fita ku ce za ku je Gona; sai ku zo ku ɓuya a gidana, za ku ga komai da idanunku.”

Sai ta ce: “To. Allah ya nuna mana goben.”

Da gari ya waye mijin da matar suka shirya, kamar za su je gona. Da suka fita sai suka ɓuya a gidan tsohuwa. Bayan wani ɗan lokaci sai suka ga yaron ya rikiɗa, ya zama babba, su na gani ya buɗe bakinsa ya yi aman ƴan mata 10, nan da nan ya hau Rumbu ya buɗe ya ɗebo Hatsi, nan take ƴan matan suka sussuka hatsin, suka niƙe shi, suka shiga watsar da garin a cikin Gida, su na yi su na Waƙa.

Da matar ta ga abin da yaron ya yi sai ta gaya wa mijinta gaskiya da cewa, ai da ma ba ɗanta ba ne, kuma a Gona ta tsince shi. Sai mijin ya ce: “Tun farko da ma na yi shakka, ga shi ta tabbata ƙarya kika yi mini.”

Sai ta faɗi ta na kuka, ta shiga hurwa ta na ba shi haƙuri, ta ce: “Ai da wannan a, gara mu zauna babu.”

Da tsohuwa ta ga abin da ke gudana tsakanin mijin da matar, sai ta ce: “Yanzu abin da za ku yi domin ku rabu da wannan masifa shi ne, ku samo Akuya da Ƙwayaye guda bakwai, sai ku ce za ku je ganin Gida. Bayan kun kama hanya kun shiga Daji, sai ku sami gindin Tsamiya ku ce za ku huta. Idan kun shimfiɗe yaron sai ku ajiye Ƙwayaye nan bakwai a gefensa ku ɗaure Akuyar a jikin tsamiyar. Can sai ku ce kun yi mantuwa.” Ta ce da su: “Ku na jin abin da nake faɗa?”

Suka ce: “Muna ji sarai.”

Ta ci gaba da ce wa matar: “Ki ce za ki koma Gida ki ɗauko abin da kika manta. Daga nan ka da ki dawo. Jim kaɗan shi ma mijinki sai ya ce zai bi sawunki saboda kin jima. To idan kun tafi ka da ku koma; da zarar kun jima zai tashi ya tafi abinsa.” Sai suka yi wa tsohuwa godiya suka koma Gida.

Da gari ya waye sai matar nan da mijinta suka ce za su je ganin gida, sai suka samo duk abubuwan da tsohuwa ta ce su nemo. Da lokacin tafiya ya yi sai suka kama hanya har suka isa gindin wata tsamiya, sai mijin ya ce ya kamata su huta a nan; suka ɗaure Akuya a gindin Bishiya suka zauna, can sai mijin ya ce: “Kash!, mun yi mantuwa.”

Sai matar ta ce: “To bari in je in ɗauko.”

Mijin ya ce: “To gara ki yi sauri.”

Bayan matar ta tafi, sai ya ce ta daɗe, bari ya bi sawunta. Shi ma ya tashi ya bar wurin. Da ya yi nisa sai ya ɓuya. Ya na nan ya na kallon gindin Tsamiya, can sai ya ga Yaro ya rikiɗa ya zama Tsoho tukuf da sanda; sai ya sunce Akuyar, ya riƙe a hannunsa; kuma ya ga ya ɗebi Ƙwayayen nan bakwai ya kama hanya ya shiga ƙungurmin daji. Da mijin nan ya ga haka sai shi ma ya juya, ya kama hanyar Gida.

Kurunkus!

Abubuwan da Labarin Yake Koyarwa

  • Karya da ha’inci: masifu ne da ke iya ɓata zaman da aka daɗe cikin amana.
  • Neman afuwa da lafiya: su ne kaɗai ke iya magance matsala a zaman amana.
  • Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa:
  • Karya fure take, ba ta ƴaƴa.
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rai Dangin Goro

Tarko: Labarin Ɓera da Sauran Ƴan’uwansa Dabbobi

Daga cikin raminsa, Ɓera na kallon sa’adda maigida ke ta cuku-cukun haɗa masa tarko. Da ya gama sai Ɓera ya
Rai Dangin Goro

Dar Gnawa: Mawaƙan Maroko Sun Zama Jakadun Yankin Maghreb

Gidan tarihi na Dar Gnawa Museum da ke birnin Marrakech na Maroko ya na cike da tarin abubuwa da suka