Amfanin Makani, ko Gwaza, ko kamar yadda ake kiransa da Harshen Larabci ‘Kulkas,’ ko Kunnen Giwa, kamar
yadda wasu suke ambata a wasu Ƙasashen na Larabawa.
Makani, ya na daga cikin Tsirrai masu muhimmanci sosai a cikin mafi yawa daga cikin rayuwar wasu Mutanen, kuma ya na daga cikin Abinci wanda Mutane suka sani tsawon lokaci, wanda ake amfani da shi wajen Abinci mai gina jiki.
Kamar yadda yake ɗauke da Vitamins, da kuma ma’adanai, waɗanda jikin ɗan’Adam yake buƙatarsa, kamar a keɓance.
Jikin ɗan’Adam ya na buƙatar Vitamin (G), da Vitamin (D), da kuma Vitamin (B6).
Ana haɗa ta, ta wasu nau’ukan Abinci a ci, ko kuma a yi amfani da shi kaɗai tare da Tumatur, da sauran kayan
haɗi ko da miya, domin ƙara mata kima wajen gina jiki, da kuma amfani ga lafiyar ɗan’Adam.
Wannan ƴaƴan Makani, ko Kulkas kamar yadda ake kira da Harshen Larabci, to ya na da Sinadarai masu muhimmanci.
Daga cikin muhimman Sinadaran da yake ɗauke da su. Domin akwai 21% Carbohydrates da kuma 2.4 Protein. Bayan haka, akwai kuma kamar su: Calcium, da Gishiri, da Aion, da Siyamin, da Ukaribuk Asid, shi ma wannan Makani ya na daga cikin abin da yake sauƙaƙa raɗaɗi a cikin jikin mutum, sakamakon Vitamin, da kuma Sinadarai waɗanda ke ɗauke a cikinta, sannan ya na taimakawa wajen cikakken aikin Bacteria mai amfani a jikin ɗan’Adam, wanda ake ce ma DNA wanda ke taimakawa wajen ayyukan wasu gaɓɓan a cikin jikin ɗan’adam.
Ya na daidai da Cholesterol a jikin ɗan’Adam. Haka nan, ya na ƙara ƙarfin Haƙora da kuma Ɓargo (Ƙashi), kamar yadda Calcium, da Posfur, da Magnesium suke taimaka wa Haƙora
wajen samun Lafiya cikakkiyar. Har ila yau, ya na da amfani ga lafiyar uwar Hanji.