Kiristocin Orthodox na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sauran shagulgula da ake gudanarwa a ƙasashe da dama, wasu ma a Afirka.

Kiristocin Orthodox na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sauran shagulgula da ake gudanarwa a Ƙasashe da dama, wasu ma a Afirka. Hoto / AFP
Daga: Staff Reporter
Kiristocin Orthodox na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sauran shagulgula da ake gudanarwa a Ƙasashe da dama, wasu ma a Afirka.
A Ƙasar Habasha, an gudanar da tsayuwar Dare a jajibirin Kirsimeti na Ranar Litinin kuma mabiya addinin Kirista sun halarci taron Coci a Ranar Talata.
Kiristocin Orthodox su na bikin Kirsimeti a Ranar 7 ga Janairu, bisa ga lissafin Kalandar Julian.

Sauran ƙungiyoyin Kirista su na bin Kalandar Gregorian, su na bikin Kirsimeti a Ranar 25 ga Disamban kowace shekara.



A Addis Ababa, masu ibadar sun kunna Kyandir kuma su na bin jagorancin limamai, waɗanda suka rera waƙoƙin Ruhaniya.

Jama’a sun sanya fararen Tufafi, alamar tsarki da kariya daga mugayen abubuwa. kamar yadda yake a al’adarsu.

A Addis Ababa, masu ibadar sun kunna Kyandir kuma su na bin jagorancin limamai, waɗanda suka rera waƙoƙin Ruhaniya.
“Ya na da kyau sosai kasancewa cikin wannan al’ummar Kirista. Ina fata dukkan matasan su zo nan su yi murna tare da mu,” in ji Kibir Girma, wata mata ‘yar shekara 23, kamar yadda ta shaida wa manema labarai a lokacin taron ibadar a Addis Ababa.

Kiristocin na Orthodox su na bikin Kirsimeti ta hanyar haɗuwa tare da danginsu da abokansu don yin Liyafa.
Kiristocin na Orthodox su na bikin Kirsimeti ta hanyar haɗuwa tare da danginsu da abokansu don yin liyafa.

An gudanar da irin wannan bukuwan a Masar da Eritriya, waɗanda ke da Kiristocin Orthodox masu yawa.

Kiristocin Masar su na bikin Kirsimeti na Orthodox.
A Ƙasar Masar, an gudanar da wani taron majami’a na bikin jajibirin Kirsimeti a Cocin Arch Michael Coptic da ke babban birnin Alƙahira.




Shagulgulan biki sun yi kyau a tsakanin mahalartan da suka taru a Majami’u a faɗin Masar.
