Dabbobi

Raƙumin Dawa: Abin da Ya Kamata Ku Sani Game da Wannan Dabbar

Raƙumin Dawa, shi ne Dabba mai shayarwa da ya fi tsawo a Duniya kuma jaririn Raƙumin Dawa ya fi baligin Mutum tsawo.

Raƙumin Dawa ba ya yawan shan ruwa. Hoto: AP

Daga: Nuri Aden

An ware ranar 21 ga Watan Yuni a matsayin Ranar Raƙumin Dawa ta Duniya, saboda wayar da kan jama’a kan muhimmancin dabbar da yadda za a kare ta musamman daga masu farautar su.

Akwai aƙalla Raƙumin Dawa 117,000 a Duniya a bara, idan aka kwatanta da 155,000 da ake da su a shekarun 1980, kamar yadda Gidauniyar Kare Raƙuman Dawa ta Giraffe Conservation Foundation (GCF) ta bayyana.

”Adadin ya na nuna raguwa da kaso 30 cikin 100, sai dai kuma adadin ya ɗan yi sama idan aka kwatanta da hasashen da wata ƙungiyar kare muhalli ta International Union for the Conservation of Nature (IUCN) ta yi a 2016, inda ta ce akwai ƙasa da Raƙuman Dawa 100,000 a faɗin Duniya,” kamar yadda Gidauniyar GCF ta bayyana a shafinta na intanet.

Raƙumin Dawa shi ne Dabba mai shayarwa da ya fi tsawo a Duniya. Hoto: AP

”Ko da yake bayanai na baya-bayan nan sun dogara ne a kan alƙaluma maimakon ainihin adadinsu. Amma a wasu wurare da Raƙumin Dawa ya fi zama, adadinsu ya ragu da kaso 95 cikin 100 a tsawon wancan lokacin,” in ji shafin.

Raguwar Raƙumin Dawa

”Ana farautar Raƙumin Dawa ne saboda namansa, kuma ya na ƙauracewa muhallin da aka san sa saboda yadda ake sare Itatuwa da kuma aikace-aikacen Noma,” in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.

Wannan ya yi tasiri sosai a ɓangaren Yawon buɗe ido da tattalin arzikin ƙasashen Afirka da dama waɗanda suke da Raƙumin Dawa da yawa. Saboda haka, wasu Ƙasashe suka haramta farautar Raƙuman Dawa.

Rakumin Dawa ya na rayuwa ne tsakanin ya na rayuwa ne tskanin shekara 25 zuwa 28 a duniya. Hoto: Reuters

Duk da cewa, ana samun Raƙumin Dawa a fiye da Ƙasashe 20 a Afirka, sai ya fara ɓacewa a bakwai daga cikinsu: Burkina Faso da Eritrea da Guinea da Mali da Nijeriya da Mauritaniya da kuma Senegal.

”Abubuwan da suke jawo barazana ga rayuwar sauran Raƙuman Dawa suka rage su ne; rarraba muhallinsu da gurɓatarsa da ƙaruwar yawan Jama’a da Farauta ba bisa ƙa’ida ba da Cututtuka da yaƙe-yaƙe da sauransu,” in ji gidauniyar GCF.

Raƙuman Dawa su na ƙara rage yawa. Hoto: AP

Raƙumin Dawan Kudu shi ne, nau’in Raƙumin Dawa da aka fi samu a nahiyar, adadinsa ya kai 49,867. Kuma 29,675 daga cikinsu ana samunsu ne a Afirka ta Kudu, sai 20,192 da ake samu a Angola, kamar yadda ƙungiyar Kare Muhalli da Halittu ta International Union for the Conservation of Nature ta bayyana.

Barcin Raƙumin Dawa

An fi samun Raƙumin Dawa a yankin Gabashin Afirka, inda suke da fiye da kaso 50 cikin 100 na gaba ɗaya adadin da ke Afirka. Kenya ta na da nau’uka da dama na Raƙuman Dawa.

Akwai aikace-aikace da ake yi a Afirka don kare Raƙuman Dawa. Hoto: AP

Saboda zubin halittarsu wanda ya fita daban da sauran Dabbobi ya sa Mutane da dama su na ƙaunarsa kuma wannan ya sa ake samun ƴan Yawon buɗe ido sosai a wurin da suke.

Raƙumin Dawa ya na buƙatar minti biyar zuwa 30 kawai na Barci, kamar yadda masana suka bayyana. Su na samun haka ne ta yin gajeran barci wanda a wasu lokuta bai wuce tsawon minti ɗaya ko biyu.

Masana sun ce, babu wasu Raƙuman Dawa biyu da suke da zanen jikin fatarsu iri ɗaya, kamar yadda babu wasu Mutum biyu da suke da tambarin yatsa iri guda (Thumb).

Da wuya a samu Raƙuman Dawa da suke da zane da ya yi kama da juna idan aka tara Raƙuman Dawa aƙalla 450, kamar yadda masana suka bayyana.

Mace Rakumar Dawa ta na rainon abin da take haifa har tsawon shekara biyu. Hoto: AFP

Kamar yadda masana suka bayyana, zuciyar Raƙumin Dawa ta kai nauyin kilogram 11 kuma ta na bugawa sau 40 zuwa 90 a kowane minti saɓanin da mutane da yawa suke tunanin – cewa, Raƙumin Dawa ya na da zuciya da ta fi ta sauran Dabbobi masu shayarwa wacce take harba jini a sassan jikinsa.

Kodayake, fatar zuciyarsa daga ɓangaren hagu, ta na da kauri saboda hakan ya na taimaka masa daga faɗuwa (fight gravity), kamar yadda Gidauniyar GCF ta bayyana.

Haihuwa

Wani abu kuma game da Raƙumin Dawa shi ne, ya na shan wahala idan zai sha ruwa da ke ƙasa saboda yadda wuyansa yake gajere idan aka kwatanta da tsawon sauran jikinsa.

Zanen jikin fatar kowane Raƙumin Dawa ya bambanta da na saura. Hoto: Reuters

Sai dai abin sha’awar shi ne, ba sa buƙatar shan Ruwa sosai saboda yawancin ruwan da suke buƙata ya na zuwa da ganyen da itatuwar da suke ci.

Raƙumar Dawa ta na yin tsawon wata 15 daga ɗaukar ciki zuwa haihuwa, bayan jaririn Raƙumin Dawa ya fito daga ciki, wato daga nisan mita biyu, ya na tsayawa da ƙafarsa cikin awa ɗaya bayan haihuwarsa. Raƙumin Dawa Maza da Mata duka su na da Ƙawo bayan haihuwarsu.

Rakumar Dawa ta na haihuwar ɗa ɗaya ne kuma mahaifiyarsa ta na rainon abin da ta haifa har tsawon wata 22, kamar yadda masana suka bayyana.

Yawan Raƙuman Dawa ya ragu a cikin shekaru 10 da suka gabata. Hoto: AP

”A wasu wuraren kaso 50 cikin 100 na jariran Raƙuman Dawa ba sa wuce shekara ɗaya suke mutuwa,” in ji gidauniyar GCF.

Gaba ɗaya Raƙumin Dawa zai iya rayuwa har tsawon shekaru 25 a Dawa ko kuma shekaru 28 idan a tsare yake.

Kodayake, yawancin Raƙuman Dawa ba sa rayuwa har tsawon wannan lokaci saboda barazanar da suke fuskanta daga mafarauta da aikace-aikacen ɗan’adam ko kuma tasirin sauyin yanayi.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Dabbobi

Ɗankunya: Ɗaya Daga Cikin Dabbobi Mafi Muhimmanci a Duniya

Wannan dabbar ita ake kira a Hausa da Batoyi, wasu kuma su na kiranta da Ɗankunya (Pengolin). Bugu da ƙari,
Dabbobi

Gwaggon Biri Mafi Tsufa a Duniya ta Cika Shekaru 67

Gwaggon birin da ta fi tsufa a duniya, Fatou, ta cika shekaru 67 a Duniya a yayin da take tsare.