Tarihi

Tarihin Juyin Mulki na Farko a Najeriya

A ranar 15 ga watan Janairun 1966, yayin Juyin Mulki ƙarƙashin jagorancin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Manjo Nzeogwu, da sauransu, inda aka ƙashe manyan shugabannin Siyasa da suka haɗa da; Firaministan Najeriya na farko, Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Firimiyan Jihar Arewa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, da kuma wasu jagororin Ƙasar 22.

Kamar yadda a Kudu maso Yammacin Najeriya, Kyatin Emmanuel Nwobosi ya jagoranci Juyin Mulki, a Yankin Arewa Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, haka ma a yankin Legas wanda take matsayin birnin Tarayyar Najeriya a wancan lokacin, Manjo Emmanuel Arinze Ifeajuna ne ya jagoranci Juyin Mulkin.

Tun da farko dai, Ifeajuna, Okafor da Ademoyega (Wanda Bayarbe ne) su ne Sojojin da suka shirya dukkanin dabarun yadda za a yi a kifar da Gwamnatin Farar Hula ta Jamhuriya ta Farko.

Tarihin Yadda Aka Kashe Firaministan Najeriya, Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa

Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, Firaministan Najeriya.

Tun farko, ruwayoyin Tarihi sun nuna cewar, Ministan Harkokin Cikin Gida na Jamhuriyar ta Farko, Alhaji Shehu Usman Shagari, ya sha sanarwa da Tafawa Ɓalewa shirin Sojoji na yin Juyin Mulki. Akwai ranar da ma sai da ran Firaministan ya ɓaci sosai a kan maganar, ya ce wa Shagari, ka da ya ƙara tasa masa wannan maganar idan ba ya son ganin ɓacin ransa.

Daidai misalin ƙarfe biyu da ƴan wasu Mintina, na Ranar 15 Ga Watan Junairu a shekarar 1966, wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Manjo Ifeajuna suka dira Gidan Firaminista Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke titin King George a birnin Legas. (A lokacin Legas ne Babban Birnin Ƙasa).

Zuwan nasu ya faru ne Awanni kaɗan bayan Tafawa Ɓalewa ya kammala tattaunawa da wasu daga cikin Ministocinsa waɗanda suka haɗa da K.O. Mbadiwe ministanT Harkokin Kasuwanci, Raymond Njoku Ministan Harkokin Sadarwa, da kuma Taslim Elias Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.

A lokacin da suka shiga Gidan sun fafata da Jami’an ƴan sanda da suke gadin Gidan, amma ba su kashe kowa ba cikin su ba. Bayan shigar su cikin Gidan babban abokin Tafawa Ɓalewa kuma sirikinsa Madakin Bauchi, na wancan lokacin, Alhaji Abubakar Garba, ya na cikin Gidan amma ba su gan shi ba.

Daga baya har Madakin Bauchi yake cewa, wanda ya jagoranci far ma Gidan Tafawa Ɓalewa ba Manjo Ifeajuna bane ake faɗa, Manjo Okafor ne saboda a cewar Madakin Bauchin, wadda ya kalla da idon sa wani Soja ne Fari siriri mai gashin baki, to amma dukkanin waɗannan siffofin na Manjo Ifeajuna ne. Daga baya dukkanin bincike sun tabbatar da Ifeajuna ne jagoran tafiyar ba Okafor ba.

Bayan Manjo Ifeajuna da tawagarsa sun shiga gidan sun yi barazanar harbe Hidimai na musamman ga Tafawa Ɓalewa, watau; ADCs ɗinsa guda biyu masu muƙamin Kaftin wadda ɗayansu ya kasance ɗan Arewacin Najeriya, da kuma Maxwell ɗan Ƙabilar Ibo, idan har ba su nuna musu wurin da Tafawa Ɓalewa yake ba.

Da farko sun turje sun ce, su sam ba su san inda Firaministan yake kwana ba, kuma ba su da makullan ɗakin kwanansa. Amma daga ƙarshe da kowanensu aka ɗora masa bindiga a ka ana faman matsa kunamar, sai suka wuce sama kai-tsaye wajen da Tafawa Ɓalewa yake kwana. Suka ƙwankwasa masa ƙofa. Ya na buɗe wa ya ga Manjo Ifeajuna tsaye ya shuno masa bindiga kai-tsaye.

Da ganin Manjo Ifeajuna tsaye cikin wannan yanayin, Firaministan ya tambaya shin lafiya kuwa?

Ifeajuna, ya yi masa sarawar ban girma kuma ya sanar da shi yazo ya kama shi ya tafi da shi ne.

Tafawa Ɓalewa ya ce, to kafin a tafi da shi y ana roƙon alfarma a ba shi dama ya yi Sallah kuma ya canja kayan jikinsa.

Aka ba shi dama ya yi sallah ya saka Farar Riga da Farin Wando da kuma Takalmi Silifa.

Ana ƙoƙarin fita da shi hadiminsa ɗan Arewa, Kaftan, ya roƙi su Ifeajuna cewar, su taimaka ka da su tafi da Tafawa Ɓalewa saboda shi kaɗai ne ɗan mahaifiyarsa kuma ta tsufa sosai wani abu ya na faruwa da shi zuciyarta za ta iya samun matsala. Amma duk da wannan roƙo ba su ji ba suka wuce da shi zuwa ƙasa.

Tafiya da Tafawa Ɓalewa, Kaftan ya biyo su har kan titin da suka ajiye motar su ya na ta ba su baki akan su faɗa masa dalilin tafiya da Tafawa Ɓalewa, kuma ina za su je da shi, idan sun tafi da shi me za su yi masa?

Ya ci gaba da yi musu magiya har sai da Tafawa Ɓalewa da kansa ya dakatar da shi ya kuma umarce shi cewa ya koma gida.

Suka tafi da shi zuwa kan Titi suka umarce shi da ya shiga cikin motar su ta Sojoji kuma suka tabbatar masa da cewa ba za su cutar da shi ba saboda sun san dukkanin rikice-rikicen Siyasa da suke faruwa a Ƙasar musamman a yankin Kudu maso Yamma, ba laifinsa bane. Daga nan suka bi kan titin Awolowo suka tafi.

Bayan tafiya da Firaministan, ma’aikatan gidansa sun yi gaggawar ƙiran Kwamishinan ƴan sandan birnin Legas Hamman Maiduguri, suka sanar da shi an sace Tafawa Ɓalewa. Suka sake kiran Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Manjo Janar Aguyi-Ironsi, suka sanar da shi halin da ake ciki.

Bayan kiran Hamman Maiduguri, shi kuma ya kira Shugaban Rundunar ƴan Sandan Najeriya watau; Alhaji Kam-Salim wanda shi ma yake a birnin Legas.

Daga nan, tsakanin ƙarfe 3 na Dare su biyun suka wuce ofishin mataimakin Babban Magatakardan Ma’aikatar Tsaro, watau Alhaji Ahmadu Kurfi domin su sanar da shi abin da yake faruwa.

A lokacin da abin ya faru ma’aikatar ta tsaro ta na hannun Babban Magatakardan ta Alhaji. Suke Kolo saboda Ministan Harkokin Tsaron Alh. Inuwa Wada baya nan.

Bayan labari ya fita cewar, an sace Firaminista an kuma kashe wasu daga cikin manyan Sojoji, musamman waɗanda suka fito daga Arewa, Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Manjo Janar Aguyi-Ironsi ya haɗa Bataliya ta biyu domin su shawo kan matsalar, masu Juyin Mulkin kuma a kama su.

A lokacin da suka samu labarin Aguyi-Ironsi ya na gari kuma ya shirya tsaf domin tunkarar su, daga nan sai suka fara tunanin yanda za su tsira. Tun lokacin da suka ɗauko Tafawa Ɓalewa daga cikin gidansa, ya na cikin Motar su ta Sojoji har ya zuwa wannan lokacin ana ta zagaya wa wurare da shi. A kan idonsa an kashe Sojoji da dama.

Kisan Abubakar Tafawa Ɓalewa

Su na cikin tafiya da Firaminista sai aka wuce Asibitin Sojoji na Yaba, domin a duba lafiyar Laftanan Ezedigbo, saboda raunuka da ya samu sakamakon arangamarsa da masu gadin gidan Janar Maimalari, lokacin da suka je kashe shi. Bayan Ifeajuna ya ajiye Ezedigbo a asibiti, sai suka wuce titin Abeokuta da Tafawa Ɓalewa a cikin Motar.

Lokacin da suka hau hanyar Legas zuwa Abeokuta sai Manjo Ifeajuna ya cewa Firaminista ya sauka a Motar. Ya na fita ya harbe shi ya faɗi ƙasa. Bayan faɗuwarsa sai Manjo Okafor ya je ya bincika gawar, ya tabbatar Tafawa Ɓalewa ya mutu, sai suka buɗe bayan Motar su suka fito da gawar Laftanan Kanal Largema suka jefar da ita kusa da ta Firaminista, suka wuce hanyar garin Abeokuta.

A kan hanyarsu ta zuwa Abeokuta suka tsaya, wasu Sojoji guda biyu suka sauka suka koma Legas. Shi kuma Manjo Ifeajuna da abokin aikinsa Okafor suka wuce garin Enugu.

Su na isa garin suka je suka samu Firimiyan yankin Inyamurai watau Dr. Michael Okpara, suka yi wata ƙwarya-ƙwayar tattaunawa da shi, wanda daga nan ne suka tafi suka ɓuya.

Daga baya Manjo Ifeajuna a hankali da taimakon abokinsa Christopher Okigbo ya sulale ya gudu Ƙasar Ghana, kuma ya samu tarba ta musamman daga Shugaban Ƙasar Ghana na wancan lokacin Kwame Nkurumah.

Nkurumah, ya ba shi gida sun zauna tare da Samuel Ikoku tsohon Magatakardan Jam’iyyar AG ta Yarbawa, wanda ya gudu Ƙasar Ghana lokacin da aka yi shari’ar Awolowo bisa laifin yunƙurin Juyin Mulki a shekarar 1962.

Gano Gawar Tafawa Ɓalewa

Har bayan kwana uku da kashe Tafawa Ɓalewa ba a samu gawarsa da na wasu manyan Sojoji ba, hakan ya sa Aguyi Ironsi ya sanar wa ƴan Ƙasa cewar; har yanzu ba a san in da Firaminista yake ba, amma ana nan ana duba wa.

Bayan kwana biyu da yin wannan sanarwar, wani Ɗansandan Arewa mai suna Ibrahim Babankowa mai matakin Mataimakin Sufartanda, ya je asibiti domin ganin Likita. Ya na zaune sai ya ji wasu mutane su na magana a kan wani irin mummunar wari mai ƙarfin gaske da suke ji a kusa da inda suke rayuwa.

Babankowa, ya tambaye su suka sanar masa wajen, shi ma kuma sai ya tuna akwai lokacin da ya na bakin aiki Rundunar Sojoji sun zo sun wuce ta inda yake zuwa can wajen.

Babankowa ya ɗauki Rundunar ƴan sanda suka tafi wajen domin duba abin da yake faruwa, wanda isar su ke da wuya suka tarar da gawarwakin mutane guda biyu har sun fara zagwanye wa.

Ɗaya da kayan Sojoji wanda aka tabbatar da ko shakka babu Laftanan Kanel Largema ne; wanda aka jefar da gawarsa kusa da ta Firaministan, lokacin da aka kashe shi.

Ɗaya gawar kuma ta Tafawa Ɓalewa ne, amma idan ba domin kayan da suke jikinsa ba wanda aka tabbatar su ne a jikinsa lokacin da aka tafi da shi, to da babu wanda zai iya gane gawarsa saboda yadda ta ɓaci.

Daga nan Babankowa ya umarci ƴan sandan da suke wajen cewar, su tsaya su kula da wajen zai je ya dawo. Lokacin da Babankowa ya tafi ya sanarwa da duk wani mai ruwa da tsaki cikin harkar tsaron Najeriya cewar an gano gawar Firaminista.

Kafin ya sanarwa Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya, Ironsi kam shi ne ma ya kira shi yake tambayar sa cikin Harshen Hausa, shin da gaske ya gano gawar Tafawa Ɓalewa? Ya ce, tabbas haka ne.

Nan take suka nufo zuwa wajen da gawar take, suka samu waɗannan ƴan sandan da Babankowa ya bari a wajen su na jira.

Bayan sun iso wajen, aka fara maganar jana’izar Firaministan amma babban abokinsa Madakin Bauchi ya ce, lallai Bauchi za a dawo da gawar domin a yi masa sutura.

Jana’izar Tafawa Ɓalewa

Haka kuwa aka yi, Madakin Bauchi ya bai wa Kaftan umarnin cewa, ya je ya sanarwa matan Tafawa Ɓalewa; Haj. Jummai da Haj. Laraba, abin da yake faruwa kuma su shirya tafiya Bauchi.

Daga nan aka ɗauki gawar aka wuce da ita Filin Jirgin Sama na Ikeja. Kwamishinan ƴan sandan Legas, Shugaban Rundunar ƴan sandan Ƙasa, Mataimakin Shugaban Rundunar ƴan sanda, Ministan Harkokin Tsaro, Madakin Bauchi da Ministan Albarkatun Ƙasa da Makamashi Alh. Yusuf Maitama Sule, su ne suka raka gawar Tafawa Ɓalewa zuwa birnin Bauchi kuma sun isa ne Ranar Bikin Sallar Azumi, saboda duk abubuwan da suka faru lokacin Juyin Mulkin, sun faru ne cikin Azumin watan Ramadan.

Daga nan aka yi wa gawar sutura kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Wane Irin Kisa aka Yi Wa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa?

Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa.

Kisan da aka yi wa Sardauna a Gidan Gwamnatin Jihar Arewa da ke Kaduna; da yawan Mutane sun yi maganganu, wasu maganganun ma ba su da kan-gado, babu ilimi ko ɗaya a ciki. Da yawan labaran da Mutane suke yaɗawa hankali ba zai ɗauka ba.

Hakan ya sa muka zurfafa bincike sosai don mu gane shin wane irin kisa aka yi wa Sardauna? Wasu Mawaƙan Hausa da wasu Mutane makusantar Sardauna, sun bada wasu labarai waɗanda hankali ba zai ɗauke su ba.

Bincike ya tabbatar da cewa, shi wanda ya jagoranci, kisan su Sardauna Manjo Patrick Chukuma Kaduna Nzeogwu, ya daɗe da ƙullantar Sardaunan a Ransa, hakan ya sa ya fara horar da wasu Sojoji wanda mafi yawancinsu ƴan Arewa ne.

Nzeogwu Ya Ƙaddamar da Samame

Ya ƙaddamar da samame (Operations) masu sunaye kamar haka

Damusa
Zaki
Giwa

Irin wannan samamen shi Nzeogwu ya yi ta ba wa sojojin horo a kai. Su kansu Sojojin ba su san dalilin da ya sa yake ba su wannan horon ba.

Kullun Dare yakan tara su, su dinga yin wannan Atisayen har Asuba. Duk da cewa, manyan Sojoji na kallon sa, su kansu ba su da masaniyar dalilin da ya sa yake ba su wannan horon ba, ya fake da cewar ya kamata a ce Sojoji na cikin shiri, kuma su riƙa jiran ko-ta-kwana.

Ranar 15 ga watan Janairun Daren Juma’a wurin ƙarfe 12 na Dare, Nzeogwu ya kwaso wasu Kuratan Sojoji su 45, wasu ma suka ce su 50, ƴan Arewacin Najeriya.

Hoton Sir. Ahmadu Bello Sardauna na Karshe.

Firimiya Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato tare da ma’aikatansa A Lemu da kuma M. Attah. Wannan ne hoto na ƙarshe da aka ɗauke shi kafin a kashe shi. A Ranar Juma’a 14 Ga Watan Junairu 1966. Hoto: National Achieves

Nzeogwu, ya kai su wani wuri inda a yanzu wata Makarantar Aikin Noma take a Mando. A wancan lokacin wurin ƙurmumin daji ne. Daga nan ne suka taso suka nufo Gidan Sardauna.

Bincike ya tabbatar da cewar, ya kashe wani Soja ɗaya da ya nemi ya yi masa taurin Kai. Kamar yadda abun ya faru wannan Sojan ya tsananta da tambayar cewa, wane irin aiki na musamnan za su yi? A ina ne kuma za su yi wannan aikin na musamman? Kuma ya ya yanayin aikin yake?

Bayan isowarsu Ƙofar Gidan Sardauna, Nzeogwu, ya nuna wa waɗannan Sojojin da ya kwaso cewar, kun san ko nan Gidan waye? Suka amsa masa da cewar, Gidan Baban duk wani ɗan Arewa ne Sardauna.

Nzeogwu ya ce musu, to mai Gidan nan shi muka fito kashe wa. Nan take wani Sargeant Bayaraben Ilori, Sajen Duru, ya ce Allah ya kiyaye shi ya sa hannu a kashe Baban shi. Bincike ya tabbatar da cewa Sajen Duru ya yi yunƙurin tsalake Titi ya gudu, amma nan take Nzeogwu, ya harbe shi.

Makaman da Nzeogwu ya zo da su Gidan Sardauna sun fi ƙarfin na Juyin Mulki, sai dai na Yaƙi da wata Ƙasa. Nan take Nzeogwu ya umarci wani kurtun Soja ɗan asalin Jihar Kebbi Musa Manga, ya ce ya harba bindigar da ake amfani da ita wurin kakkaɓo Jirgin Saman Yaƙi MM 400× a saman rufin ɗakin da Sardauna yake.

Ƙarar wannan bindigar ta tada hankalin duk wani mutumin da ke Unguwar Shanu, da Unguwar Sarki.

Wannan bindigar ita ce tasa rufin ɗakin ya kama da wuta. Sardauna da matansa da yaran da yake riƙe da su na ƴan’uwa da abokan arziki da duk ma’aikatan da ke gidan sun taru a farfadiyar da ake aje Mota na Gidan.

Sardauna, ya tsinci kansa a wani hali na ba shi da wani mataimaki sai Allah. Ba shi da makamin da zai kare kansi balle ma ya kare iyalansa da su. Bincike ya tabbatar da cewar, a nan farfajiyar ajiye Motocin ne Nzeogwu ya samu Sardauna da matansa guda uku da Larai matar Ali Odilin Sardauna, da Ali Odili.

A nan an samu mabambantan maganannu, matan Sardauna Jabbo da Goggon Bichi sun bada labari iri ɗaya, duk da cewar ba lokaci ɗaya aka yi hirar da su ba.

Jabbo

Ta ce, duk kanmu muna cikin fargaba mun ruɗe saboda matsanancin ƙarar harbe-harbe da muke ji, a wannan lokacin Sardauna na tsaye ne ya na jan Carbi, Hafsat uwargidansa ta na rungume da shi, dukkanmu muna kuka mun rasa inda za mu saka kanmu.

Da abubuwa suka yi tsanani shi Sardauna ya ce mana, ni tawa ta ƙare ku nake ma addu’ar Allah ya kare ku daga sharin wayannan mutanan.

Hafsat, ta riƙe Sardauna da ƙarfin-tsiya, nima ina manne da jinkinsa haka Goggon Bichi. Larai matar Ali Odali na kusa da ni.

Lokacin da Nzeogwu ya zo, ya zo ne da wata Fitila mai Haske irin ta Mafarauta a goshinsa, da yake Gidan akwai Duhu, babu wuta, da farin Hankici a wuyansa. Da yake muna da yawa da yara da mu matanshi mun kewaye shi a wannan lokacin.

Nzeogwu, ya yi ta mana barazanar cewa idan ba mu kauce ba zai harbe mu ya kashe mu dukkan mu. Amma muka yi burus da shi. Bayan ƙoƙarin sa mana ƙarfi da ya yi, mu ka yi masa tirjya, ya sa kan bindiga ya buge ni a Goshi, Jini na ya yi tsartuwa na faɗi sumammiya. Ta ce kamar yadda abubuwa suka faru, a nan ne dai Nzeogwu ya harbi Sardauna a Goshi da zuciyarsa.

Goggon Bichi

Ta ce, lokacin da Nzeogwu ya zo da Fitila mai Haske a goshinsa, da farin Hankici a wuyansa. Mu kuma dukkanmu mun kewaye Sardauna, Hafsat ta riƙe shi ƙam-ƙam. Jabbo ma na riƙe da shi, ni ma ina manne da shi. Nzegowu ya yi barazanar zai harbe mu amma mu da yara kuka kawai muke muna Salati. Goggon Bichi ta ce ta na da yaƙinin cewa, kafin ma shi Nzeogwu ya harbi Sardauna Allah ya amsa ran Sardaunan. Ta kawo dalilai ƙwarara guda biyu da yake tabbatar da abun da take faɗa.

Abu na farko ta ce, babu yadda zaa a sa kan bindiga a bugi ɗaya daga cikin Matansa har ta faɗi ta suma ba, a ce Sardaunan bai yi magana ba, ta ce abu ne wanda ba mai yi wu ba.

Goggon Bichi, ta ce ko da mai zai faru da shi kuwa, wallahi Sardauna sai ya yi magana kai sai dai bayan ransa wallahi, ba zai taɓa ganin ya na raye a wulaƙanta Matarsa ba.

Dalilinta na biyu kuwa, Nzeogwu ya harbi Hafsat kafin ya harbi Sardauna, nan ma ta ce daga nan ne ma na tabbatar da cewa Sardauna ba shi da rai, wallahi ya na dai tsaye ne kawai amma Allah ya zare ransa. Ta ce har Nzeogwu ya harbe shi ba a ji ihunsa, ko ƙara, ko wata magana ba. Hakan ma ya ƙara tabbatar mana da cewa ya rasu.

Jabbo da Goggon Bichi, da Larai Matar Ali Odilin Sardauna, wacce ita ma ganau ce, sun tabbatar da cewar, in ma da wani Namiji a sanda abun ya faru to Ali Odili ne.

Matan na Sardauna guda biyu da Larai Matar Ali Odili sun ce, duk Mazajen da ke Gidan sun gudu. Suka ce duk wani mutum yau da ya tara ƴan Jaridu ya ce ya san yadda aka kashe Sardauna, ko a gabansa aka kashe Sardauna ƙarya ya ke yi.

Marigayi Sheikh Abubakar Gumi, shi ne ya yi wa Sardauna wanka ya tabbatar da cewar tabbas akwai harsashi a goshin Sardauna, a Goshi aka harbe shi.

Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna, tare da Sheikh Abubakar Gumi, mai taimaka masa a harkokin Addini. Hoto: Wikipedia

Ƙarin Bayani: Ba za mu iya kawo dukkan Hikayoyin a nan ba amma za a iya neman Littafi mai suna; ‘Jarumar da Ba’a Rubuta ba Hafsat Ahmadu Bello,’ wanda Ladi S. Adamu ta rubuta.

Yadda Muka Yi da Nzeogwu Bayan Ya Kashe Sardauna – Sheikh Abubakar Gumi

Sheikh Abubakar Gumi, mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi Addinin Musulunci. Hoto: Wikipedia.

Kamar ƙarfe huɗu na Asuba, Ranar Juma’a aka bugo mun Waya, bayan na ɗauka sai na ji Ministan Ilimi na Arewa Alhaji Isa Kaita, ya ce min, Sojoji fa sun yi Juyin Mulki, har an kai ma Gidan Sardauna hari, kamar yadda ya ce min, duk Manyan Jami’an Gwamnati sun ɓuya.

Ya ce min, ya yi magana da Hassan Usman Katsina, amma Hassan dai a lokacin ya ce masa babu abin da zai iya yi. Hassan ya ce masa a wannan lokacin ma, ya na ganawa ne da bijirarrun Sojojin.

Isa Kaita ya ce, ya kamata ni in je Gidan Sardauna in gane ma Idanuna abin da ke faruwa.

Bayan na kimtsa na yi Sallar Subahi, na kuma kama hanya na nufi Gidan Sardauna, na je na iske Gidan an yi kacha-kacha da shi, alamu sun nuna an yi amfani da manyan Makamai wurin lalata Gidan. Har lokacin da na isa Gidan hayaƙi ne a turnuƙe. Sai wasu tsirarun Sojoji ne a tsaye da Bindigogi a hannunsu, ko ina tsit.

Haka na wuce su na kutsa kaina cikin Gidan, ina shiga na ci karo da Gawar Firimiya a kwance a filin da ake aje Motoci na Gidan.

Nan da nan, na ce a ɗauki Gawar a kai ta Gidan Sarkin Musulmi, da ke Unguwar Sarki, Sardauna, da shi da Uwargidansa Hafsat aka kashe su.

Bayan mun gama kimtsa shi, Rana ta fara ɗagowa, ni ne na sallaci duka gawarwakin.

Ina sa ne kuma da cewar, an yi babban rashin da nan kurkusa abu ne mawuyace a samu kamarsa.

A kan hanyata ta dawowa gida daga wurin jana’izar Sadauna, na wuce gun-gun mutane sun taru suna ta alhinin abin da ya faru. Bayan na samu natsuwa abubuwa sun koma kamar yadda suke, Ranar komawa aiki na shirya kamar kullum na tafi wurin aikina.

Ina cikin ofishina da Safe sai ga Motar Sojoji, cike da Sojoji, ta shigo harabar wurin aikina. Wasu daga cikin Sojojin suka sauko a Mota suka tambayi inda ofishina yake.

Bayan sun shigo ofishina suka yi min gaisuwa irinta ta girmamawa, suka ce an turo ne su tafi da ni Maigidansu Nzeogwu, ya na son ganina.

Kuma zan shiga motarsu ne, tilas su tafi da ni amma zan iya sa wani cikin ma’aikatana ya bi mu a baya shi sai ya dawo da ni.

Na ta shi na bi su ban yi musu ba, na umarci Direba na ya bi ni da Mota, bayan mun gama ganawa ya dawo da ni.

Bayan mun isa Bariki Sojan, in da shi Nzeogwu yake. Na ga Sojoji da yawa su na gadin Barikin, ko wane Soja saɓe yake da Bindigarsa.

Bayan mun yi fakin muka sauko daga Mota muka shiga cikin ofishin, cikinmu ba wanda ya yi ma wani magana tsakanina da wayannan Sojojin.

Bayan sun kaini inda Nzeogwu yake, ya kuma tare ni cikin fara’arsa na kuma zauna akan kujera, sai ya fara magana cikin tattausar murya.

Abin da yake son sani shi ne; ina muka ɓoye makaman da muka sayo?

Wannan tambayar tasa taba ni matuƙar mamaki, na ga ni dai a rayuwata ban ma taɓa ganin Nzeogwu ba, ban kuma taɓa wata alaƙa ta rayuwa da shi ba. Ni a tunani ma shi ne ya kira ni ya yi mun ta’aziyyar rashin Sardauna, da na yi ko kuma ya nuna danasani a kan abin da ya aikata.

Dama ban yi tsammanin kalamai na ba ni haƙuri daga gare shi ko nadama a kan abin da ya aikata ba, tun da na lura ya na al’afari da abin da ya aikatan.

Abin da kuma ya ƙara ba ni mamaki, wanda suka saɓi Makamai suka yi Juyin mulki wai a lokacin ne suke ƙoƙarin tattara hujjojinsu ko kuma dalilan hamɓarar da wannan gwamnatin?

Sai na gama kafin in ba shi amsar tambayarsa yakamata in nemi ƙarin bayani daga gare shi.

Sai ya ce min a irin labaran da ya samu an ce masa, mun siyo Makamai masu tarin yawa, mun shigo da su cikin Ƙasa, kuma mun siyo makaman ne daga Ƙasashen Gabas ta Tsakiya. Kuma, niyyarmu ita ce; mu ƙaddamar da Jihadi a kan waɗanda ba Musulmi ba, shi ya sa yake so in faɗa masa inda muka ɓoye makaman.

Lokacin da na zo ba shi amsar tambayarsa, na tabbatar masa cewar ni a wurinsa ma na fara jin wannan maganar, na kuma tabbatar ina magana ne a matsayina na mashawarcin Sardauna, akan harkokin da suka shafi Addinin Musulunci. Kuma na tabbatar masa da cewa Sardauna, bai taɓa zuwa wata Kasar Larabawa a matsayinsa na Firimiya ba tare da dani ba. Kuma ban taɓa ji ya yi maganar Makamai ba a wata Ƙasar Larabawa, balle ma har mu siyo mu shigo da su Najeriya, da sunan wai za mu yaƙi waɗanda da ba Musulmai ba.

Wane ne Ifeajuna wanda Ya kashe Firimiyan Najeriya?

Emmanuel Arinze Ifeajuna, wadda ya kashe Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, Firaministan Najeriya. Hoto: Muhammad Cisse

Daga wanda ya lashe Lambar Zinariya na Commonwealth na farko a Afirka zuwa Fuskantar hukuncin kisa a Ranar 25 ga watan Satumba na 1967.

Emmanuel Arinze Ifeajuna (1935-1967) Hafsan Sojan Najeriya ne kuma ɗaya daga cikin manyan jigo a Juyin Mulkin da Sojoji suka yi a Ranar 15 ga watan Janairun 1966 a Najeriya.

An haife shi a Ranar 1 ga Disamba, 1935 a Onitsha, yankin Gabashin Najeriya (yanzu jihar Anambra). Ifeajuna, ya halarci Kwalejin Gwamnati da ke Umuahia daga baya kuma ya halarci Kwalejin Jami’ar Ibadan, inda ya kasance Memba na Fitacciyar Ƙungiyar Wasan Kwaikwayo ta Jami’ar Ibadan (IUC).

Ya kuma kasance ƙwararren ɗan wasa, kuma ya wakilci Najeriya a Gasar Guje-Guje da Tsalle-Tsalle a Gasar Daular Birtaniya da ta Commonwealth a shekarar 1954.

Bayan kammala karatunsa a Makarantar Kimiyya, a Kwalejin Jami’ar Ibadan kuma ya shiga harkar Siyasa.

Ifeajuna ya shiga Aikin Sojan Najeriya a shekarar 1959, kuma ya sami horon Aikin Soja a Najeriya da Ingila. Ya ƙara samun horo a Makarantar Soji ta Royal Military Academy da ke Sandhurst a Ƙasar Ingila, kuma an ba shi muƙamin Hafsa a Rundunar Sojin Najeriya.

Cikin ƙanƙanin lokaci Ifeajuna ya haye muƙami kuma ya zama Manjo a Sojojin Najeriya.

A Ranar 15 ga watan Janairun 1966, wasu gungun Matasa Hafsoshin Soja ciki har da Emmanuel Ifeajuna, suka yi Juyin Mulki a Najeriya.

Wani ɓangare na Sojojin Najeriya ne suka shirya Juyin Mulkin, wanda bai gamsu da yadda Gwamnatin Ƙasar ke zargin cin hanci da rashawa da kuma rikicin yankin Jihar Yamma da ake fama da shi a Ƙasar ba. Juyin Mulkin dai, ya yi sanadiyar kifar da Gwamnatin Firaministan Najeriya, Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa da kuma wasu shugabannin Siyasa da Sojoji, da ma kashe su.

Sai dai, Juyin Mulkin bai cimma burin da aka sa a gaba ba, ya kuma haifar da wasu abubuwa da suka jefa Najeriya cikin wani yanayi na taɓarɓarewar Siyasa.

Ifeajuna, ya tsere zuwa Ghana, sanye da kayan mata. Bayan watanni 20 ya dawo, ya fafata a Yaƙin Basasar Najeriya, inda ya shiga ɓangaren Sojojin Biyafara.

Ojukwu ya zargi Ifeajuna da wasu Jami’ai uku da laifin ƙulla maƙarƙashiya da Cin Amanar Ƙasa da fuskar taimakawa Najeriya, zargin da suka musanta, sun ce su na ƙoƙarin ceto rayuka da Ƙasarsu ta hanyar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya da kuma sake haɗe Najeriya.

Ojuwku ya sa an harbe su duka, a Ranar 25 ga watan Satumbar 1967.

Ƙarin Bayani: Idan ka taɓa amfani da wannan littafin tun kana yaro a makaranta a Najeriya, lura cewa hoton da ke kan bangon littafin Ifeajuna ne a lokacin a lokacin da yake wasan da ya sami lambar Zinariya da ya yi nasara a gasar Commonwealth a shekarar 1954.

Jerin Sunayen Jagororin Sojojin da Suka yi Juyin Mulki na Farko a Najeriya

  1. Emmanuel Ifeajuna
  2. Manjo Chukuma Nzeogwu (Kaduna Nzeogwu)
  3. Timothy Onwuatuegwu
  4. Adewale Ademoyega
  5. Chris Anuforo
  6. Humphrey Chukwuka
  7. Don Okafor

Sunayen Waɗanda aka Kashe a Juyin Mulki da Nzeogwu Kaduna Ya Jagoranta

Manjo Chukuma Nzeogwu, wadda ya jagoranci kashe Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardauna da sauran wasu jigajigan ƴan Siyasa. Hoto: African Pan Achieves

Farar Hula

  1. Firaminista Abubakar Tafawa Ɓalewa
  2. Firimiya Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
  3. Firimiya Samuel Ladoke Akintola
  4. Ministan Kuɗi Festus Okotie-Eboh
  5. Ahmed Ben Musa (Babban Mataimakin Sakataren Tsaro na Sardauna Ahmadu Bello)
  6. Hafsatu Bello (Matar Sardauna Ƴar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku)
  7. Madam Latifat Ademulegun
  8. Zarumi Sardauna,
  9. Ahmed Fatigi (Direban Sardauna Ahmadu Bello)

Sojoji da Ƴansanda

  1. Brig. Samuel Ademulegun
  2. Brig. Zakariya Maimalari
  3. Col. Ralph Shodeinde
  4. Col. Kur Mohammed
  5. Laftanar Kanal Abogo Largema
  6. Lt. Col. James Pam
  7. Lt. Col. Arthur Unegbe
  8. Sajan Daramola Oyegoke (Ya taimaka wa Nzeogwu a harin da aka kai Gidan Sardauna kuma a cewar rahoton ƴan sanda, Nzeogwu ne ya kashe shi)
  9. PC Yohanna Garkawa
  10. Lance Kofur Musa Nimzo
  11. PC Akpan Anduka
  12. PC Hagai Lai
  13. Philip Lewande.
Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da
Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun