Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun bar tarihi a yankin Afirka.
Sai dai yanayi mai tsananin gaske da tumbatsar Teku da sauran ƙalubale da ke da alaƙa da ɗumamar yanayi na barazanar lalata muhimman al’adun Afirka kamar yadda wani bincike ya yi gargaɗi.
Wasu masu bincike daga Birtaniya da Kenya da Amurka sun ce, “Za a rasa wasu daga cikin mahimman abubuwan tarihi na Afirka sakamakon sauyin yanayi cikin gomman shekaru matuƙar ba a yi wani abu a kai ba.”
Gargaɗin na zuwa ne yayin da masu binciken kayan tarihi a Sudan ke ƙoƙarin hana ruwa daga Kogin Nilu isa wurin kayan tarihin Duniya da ke al-Bajrawiya.

Wajen da ya taɓa zama birnin Sarauta mai Daula na tsohuwar Daular Meroitic da ta yi shekaru 2,000 ta na da ɗaruruwan kayayyakin tarihi.
Duk da ambaliya na faruwa a Kogin Nilu duk shekara, mazauna wajen sun ce a wannan shekarar lamarin ya fi tsananta, ta kashe kusan mutum 100 tare da ɗaiɗaita wasu 500,000.
Wasu masana kimiyya sun ɗora laifin kan sauyin yanayi da bunƙasar birane a bakin kogin.
Nahiyar Afirka na da wuraren tarihi da UNESCO ta lissafa, idan aka haɗa da waɗanda suke tsibiri waɗanda suke wani ɓangare na ƙasashen Turai.
Ga yadda sauyin yanayi ya shafi wasu daga cikin muhimman wuraren tarihin.
Sabratha, Libya

Wasu manyan wuraren tarihi biyar a Libya na cikin haɗari saboda ɓarnar da rikici ya haifar a ƙasar.
Daga cikin su akwai birnin Phoenician na Sabratha wanda ya taka muhimmiyar rawa a cinikayya tsakanin Afirka da tekun Bahar Rum.
Sabratha, na daga cikin yankin Numidia da ke Massinissa kafin a haɗe da Daular Rome kuma sake gina ta a ƙarni na biyu da na 3 AD.

A yanzu, bincike ya nuna cewa zaizayar teku da tumbatsar teku da guguwa sun shafi Sabratha sosai.
Tashar Ruwa Da Ke Suakin
Tashar ruwa da ke tsibirin Suakin, a Arewa maso Yammacin Sudan, ta taɓa zama tashar da ke da matuƙar muhimmanci a Bahar Maliya.

Labarinta ya soma ne tun shekaru 3,000 da suka gabata lokacin da sarakunan Masar suka mayar da tashar zuwa wajen kasuwanci da haƙe-haƙe.
A tsawon tarihi, Suakin ya zama wata matattarar mahajjata da ke kan hanyar zuwa Makkah sannan ya taka muhimmiyar rawa a cinikin bayi a Bahar Maliya.
Ya kuma taɓa zama wani ɓangare na Daular Ottoman.

Sai dai wajen ya lalace tun da ya rasa martabarsa shekaru 100 da suka gabata. A yanzu, wajen na ɗauke da wasu kyawawan misalai na gidaje da Masallatai a cewar UNESCO.
A halin yanzu, Farfesa Clarke na gudanar da bincke don tantance yadda asarar ta kasance sakamakon cikar teku da kuma zaizayar Teku.
“Abin da muka sani shi ne a ƴan shekaru masu zuwa lamarin zai shafi Bahar Maliya abin da ke nufin za a rasa shi matuƙar ba kai ɗauki ba.”
A shekarar 2018, Sudan da Turkiyya sun rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 99 na sake ƙawata Suakin amma masu suka a Turkiyya su na zargin akwai wani buri na daban.
Tsohon Garin Lamu, Kenya

Yankin Lamu Old shi ne matsugunin Swahili mafi tsufa a gabashin Afirka a cewar UNESCO.
Saɓanin sauran ƙuyuka da aka yi watsi da su a gaɓr gabashin Afirka, jama’a sun ci gaba da zama a Lamu sama da shekaru 700.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara cewa wajen ya zama wata Cibiya mai mahimmanci ta nazarin Musulunci da al’adun Swahili.

Sai dai Lamu ta sha fuskantar koma-baya, ma’ana ta rasa kariya daga ƙasa da kuma Itace.
“Wannan ya na da nasaba da ginin Tashar Ruwan Lamu, wanda ke lalata dajin Mangrove da ke kare tsibirin daga ambaliya,” in ji Farfesa Clarke.
“Don haka yawancin abin da za mu kira kayan gado su na kariya ne ga al’adun gargajiyar. Kuma yayin da muke lalata al’adun gargajiyar, muna kuma yi wa wuraren al’adun gargajiyar illa.”
Yankunan Teku, Tsibirin Comoros

Gamayyar tsibirai da ake kira The Union of Comoros da ke kan gaɓar tekun gabashin Afirka a mashigin Mozambique, ba shi da Tarihi a Duniya, amma guda huɗu ƙasar ke son mamayewa.
Ya na da wata ingantacciyar Fada ta ƙarni na 13 da kuma sauran gine-ginen tun a ƙarni na 16.

Amma Comoros ta na daga cikin wurare “da suka fi fuskantar barazana” daga tumbatsar Teku, a cewar Farfesa Clarke.
A wani yanayi na matsakaiciyar iska mai guba, “muhimman sassa na yankin a gaɓar teku na Afirka za su shafe zuwa 2100“, a cewar wani sabon bincike.
“Daga 2050, Guinea, Gambia, Najeriya, Togo, Benin, Congo, Tunisia, Tanzaniya (haɗi da Zanzibar) da kuma Comoros za su kasance cikin barazanar zaizaya da tumbatsar Teku.”
Tasoshin Ruwa, Ghana

Tekun Ghana ya na cike da wuraren kasuwanci masu ƙarfi da ginin zamanin da, waɗanda suka kafu tsakanin 1482 da 1786, da ke da girman kilomita 500 tsakanin Keta da Beyin.
Ƴan kasuwa daga ƙasashen Portugal da Spain da Denmark da Sweden da Netherland da Jamus da kuma Birtaniya ne suke zaune a gidajen na Ghana. Gine-ginen sun taka rawa a kasuwancin Zinariya har zuwa lokacin Cinikin Bayi tsakani tsakanin Afrika da Amurka.

Amma gine-ginen su na wurare ne da ke da cunkosun jama’a wanda matsalar Sauyin Yanayi ke yi wa barazana (kamar goguwa da tumbatsar teku. Farfesa Clarke ya ce, misalan ire-iren waɗannan gine-ginen kamar na Prinzenstein a Keta “teku ta shafe su.” “Muna da hotuna na 1970 kuma muna da na yanzu, duka wurin ya shafe,” kamar yadda ta shaida wa kafar yaɗa labarai ta BBC.
Tsohon Garin Djenné a Mali
Gidajen laka 2,000 a Djenne su na cikin hotuna kyawawa a Mali da suka samo asali tun 250 kafin haihuwar Annabi Isa (AS).
Djenne garin kasuwanci ne kuma mahaɗar cinikin Zinariya a tsakanin ƙasashen da ke Sahara. A wajajen ƙarni ma 15 zuwa 16 ya kasance Cibiya ta yaɗa addinin Islama.

“Wurare Masu Ban Mamaki”
Barazana ga al’adun Afirka ba game da Sauyin Yanayi ba ne kawai, har ma da ikon ƙasashe na rage tasirinsa.

Akwai ƙasashe kamar Masar, da ke zaune a wani yanayi mai ‘babban hatsari na ambaliyar ruwa a cikin shekaru masu zuwa’ amma kuma a shirye take ta tunkari wasu ƙalubale. Ƙasa kamar Somalia da ke fama da yaƙi hakan ya hana bayyana wasu wurarenta cikin wuraren tarihi na Duniya.
A tarihance, mun san akwai wurare da yawa na tarihi a Arewacin Somalia, a cewar Farfesa Clarke.
Manufar bincikenta shi ne bayar da haske ga ire iren wadannan wuraren waɗanda ba a sani ba a Duniya, kuma ta na tsoron “za su ɓata babu wanda zai san su.”