Jiya Da Yau

Shaka Zulu: Tushen al’ummar Zulu

Shaka kaSenzangakhona, shi ne Sarkin Masarautar Zulu daga 1816 zuwa 1828. Ɗaya daga cikin mafi tasiri na Monalu Zulu, ya ba da umarnin yin gyare-gyare mai fa’ida wanda ya sake tsara sojojinsa suka zama gagarabadau.

Sunan Shaka Zulu na da Nasaba da Yaƙi

Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi hira da masanin tarihi Maxwell Shamase wanda yake ganin an gurɓata tarihin Shaka.

An faɗi abubuwa da dama game da Shaka Zulu. Idan ana batun bambance gaskiya da ƙagaggen labari, Maxwell Zakhele Shamase mashahuri ne. Shi da Mthandeni Patrick Mbatha, masanin tarihi daga Jami’ar Zululand a yanzu haka su na rubuta wani Littafi a kan mutumin da ke zama Gwarzon tarihi.

Me Ya Sa Za Ku Rubuta Tarihi Game da Shaka Zulu?

Maxwell Shamase: Ba a yi wani rubutu mai yawa a game da Sarki Shaka ba musamman daga mahanga ta Afrika ba. Wasu daga cikin abubuwa waɗanda mutanen da ba ƴan Afirka ba suka rubuta, an gurɓata gaskiyar lamura a cikinsu. Muna so mu bayar da labarin daga mahanga ta ƴan Afrika.

Ya Ya Za Ka Bayyana Sarki Shaka?

Kafin a haifi Shaka, wata Bokanya mai suna Sithayi, ta ba da labarin cewa za a haifi wani yaro wanda zai kawo sabon sauyi da kuma sabuwar Ƙasa. Ya kasance Soja ɗanbaiwa a Afirka. Mutum ne wanda ya gina Ƙasa ba mai son kisa da zubar da jini ba. Kuma ba mutum ne mara tausayi ɗan ina da da kisa ba.

Yaushe ne Kuma a Ina aka Haifi Shaka?

An haife shi a watan Juli na shekarar 1787 a cikin al’ummar Langeni inda mahaifiyarsa ta fito.

Ina Shaka Zulu Ya Samo Sunansa?

Mahaifinsa mutum ne mai aiki da hankali (Senzangakhona). Mahaifiyarsa ƴar Sarkin Nandi ce a Gidan Sarautar Mhlongo wanda ya rayu a wurin da ake kira ‘Langeni.’

Sunan Shaka, ya samo asali ne daga wata cuta da ake kira ‘Ishaka.’ Wannan cuta na sanya jikin Mata ya riƙa ciwo da kasala da kuma kumburi. A lokacin da mahaifiyarsa wacce a wancan lokaci ba ta yi aure ba ta samu ciki, mutane sun yi tsammanin ta na fama ne da cutar Ishaka; yadda Shaka ya sami wannan sunan ke nan.

Saboda haka ya kasance Shaka ɗan Senzangakhona. A wancan lokaci sunan mahaifinka shi ne sunanka na biyu. Kuma sunan kakan Shaka shi ne Zulu.

Lokacin da Zulu ya zama Sarki, sai Shaka ya ce, ya kamata mu sami al’adarmu mu kira kanmu mutanen Zulu. Shi ne na farko da ya kira jama’arsa mutanen Zulu, shi ya sa aka san shi a matsayin wanda ya kafa Ƙasar Zulu duk da cewa ya gaji Sarautar da ta daɗe tsawon zamani.

Shin Mahaifin Shaka, Senzangakhona, ya Amince Ɗansa ne?

Ya yi ta ƙoƙarin musantawa saboda ya na tsaron mahaifinsa, Sarki Zulu. Ga Yarima mai jiran Gadon Sarauta kamar Senzangakhona ya yi wa yarinya ciki kafin aure abin kunya ne wanda ka iya kai wa ga hukunci mai tsanani, ciki har da yiwuwar rasa damar yin Sarauta.

Daga baya iyayensa suka amince kuma Senzangakhona ya biya kuɗin Sadaki wanda ya bai wa Nandi damar tare wa cikin iyalan Senzangakhona. Daga baya, an fitar da Nandi da Shaka daga Gidan Senzangakhona,

Shin Ya Ya Aka Yi Haka ta Faru?

Nandi, Mace ce mai ɗagawa da saurin fushi da so a kullum ta riƙa bai wa mutane umarni. A saboda haka, dangantakarsu ta kasance cike da rigingimu. Shi kuwa Senzangakhona, ba zai iya jurewa ba. Ya kore ta tare da Shaka. Sun yi ta watangaririya.

Nandi ta haɗu da Ngwati. Suka fara soyayya su ka ci gaba da zama tare inda ta haifi ƙanwar Shaka. Bayan da aka kashe Ngwati, Sarkin Mthethwa Dingiswayo ya karɓi ƴaƴanta biyu.

Ya Ya aka Yi Shaka ya Shiga Cikin Rundunar Sojin Mthethewa?

Ya zama babban yaron Sarki Dingiswayo a lokacin da ya ke ɗan shekaru 16 da haihuwa. Wannan kuwa ya kasance ne saboda basirarsa da kuma ƙarfin zuciya. Ba a jima ba aka ɗauke shi a matsayin mayaƙi aka sa shi cikin Rundunar Izicwe.

Wane Tasiri Shaka Zulu Ya Yi a Rundunar Sojin Mthethwa?

A matsayin Kwamanda, ya hana mayaƙan sanya Takalmi Fade, ya kuma umarce su, su riƙa tafiya babu Takalmi. Haka kuma, ya hana amfani da dogon Mashi wanda mayaƙa za su harbi abokin-gaba da shi.

Maimakon haka, ya ɓullo da gajeren Mashi ‘Iklwa’ domin faɗa dab da dab da abokin-gaba. Wannan ya tilasta wa mayaƙansa su matso kusa su sari abokin-gaba sannan su juya su sari wani da makami ɗaya. Ya kuma ɓullo da dabarar raba mayaƙa dama da hagu domin yi wa abokan gaba ƙofar rago.

Tsarin ya yi kama da yanayin kahuna biyu na Karkanda. Ya zama mutumin da ake matuƙar jin tsoronsa wanda kuma ya yi fice hatta a sauran ƙabilu da Masarautu, a kan haka ne ma ya sami sunan ‘Nodumehleli’ (wanda daga zaune ya ke sa Duniyata girgiza).

Mayaƙin Mthethwa shi ne wanda a ƙarshe Shaka ya damƙa wa Sarautar Senzangakhona.

Shin Babu Wanda Ya Ƙalubalanci Wannan Mataki?

A lokacin da mahaifinsa Senzangakhona ya rasu, Sarki Dingiswayo ya taimaka masa dawo wa wajen al’ummar mahaifinsa, inda ya ba shi mayaƙa biyu su taimaka masa karɓe ragamar mulki. Sai dai Senzangakhona ya faɗa wa babban Wazirinsa cewa, ɗayan ɗan nasa Sigujana shi ne Yarimansu mai jiran gado amma ba Shaka ba.

Da isarsa sai ya kashe Sigujana kuma ya ƙarɓi Karagar Mulki a shekarar 1816 a matsayin Sarki. Bayan mutuwar Sarki Dingiswayo, Shaka Ya shigar da mutanen Mthethwa ƙarƙashin Daularsa, sannan ya sa ƙabilar da Dingiswayo ya ci da yaƙi cikin sojojin da ke ƙarƙashin jagorancin Shaka. Ya kuma ci gaba da cin sauran ƙabilu da yaƙi ya kuma mulke su.

Shaka Na da Mummuna Tunani Kan Aure, Inda Har ta Kai Wasu Mutane na Cewa Mai Yiwuwa Ɗanluwaɗi ne shi. Mene ne Dalilin Haka?

Mummunan tunaninsa ga Aure ya faru ne sakamakon yadda ya ga aka yi wa mahaifiyarsa. Sannan an ci zalinsa matuƙa sakamakon tasowa da ya yi ba cikin danginsa ba kuma ba tare da mahaifinsa ba. Babu shakka ya na yin Jima’i da Mata to amma da zarar sun sami ciki sai ya miƙa su ga ɗan’uwansa, Mpande wanda ake gani a matsayin rauni.

Gaskiya ne Cewa, Shaka Zulu Ya na Kashe Matan da Ya Yi wa Ciki, Kamar Yadda Aka Yi Ta Raɗe-raɗi?

Wannan ba gaskiya ba ne. Mun dai san cewar, akwai wani lokaci da wasu ƴan kasuwa farar fata suka farfaɗo da wata Mata da ta suma saboda zazzaɓi mai zafi. Shaka da mutanensa sun yi tsammanin ta mutu. Sun ba ta magani su ka farfaɗo da ita. Shaka ya zaƙu ya na so ya tabbatar ko da gaske ne ƴan kasuwar sun tayar da matacce.

Ya bada umarnin a kashe wata Mata sannan ya umarci ƴan kasuwar su nuna ikonsu su tayar da ita wanda ko shakka babu ba su iya yin hakan ba. A wasu lokuta saboda son ganin ƙwaƙwaf, an shaida mana cewa, ya feɗe cikin wata Mace mai ciki domin ganin yadda jariri ya ke girma a cikin ciki.

Mun ji Cewa, Shaka ya Kashe Mutane Kusan Miliyan Ɗaya, Wasu Daga Cikinsu Haka Kawai ko Kuma Wai Saboda Sun yi Gajarta. Shin Gaskiya ne?

Wannan tunani ne na Ƙasashen Yamma, kuma ba gaskiya ba ne. Ku tuna mutane Miliyan 50 suka mutu a Yaƙin Duniya na biyu baya ga wasu Miliyoyi da suka rasa rayukansu a Yaƙin Duniya na ɗaya. A saboda haka, wane ne ya fi rashin imani tsakanin Shaka da waɗannan Turawa da suka haddasa Yaƙin Duniya na ɗaya da na biyu? To amma ya kamata a ɗauki kisan da aka aikata a wannan hali a yanayi na lokaci. Abu ne da mutane s ka saba da shi a wancan lokaci.

Zai ba da dalilai da su ka sa aka aikata kisan. Alal misali, waɗanda aka tabbatar da cewa Mayu ne an kashe su. Sarakuna a wancan zamani sun ɗore ta hanyar kashe abokan hamayyarsu.

Wata Hanya aka Kashe Shaka Zulu?

An kashe shi a cikin watan Satumba na shekarar 1828. Akwai wani makirci da aka shirya bisa jagorancin goggonsa. Babban dalili shi ne bayan mutuwar mahaifiyarsa Nandi, Shaka ya samu taɓin hankali inda ya kashe mutane da dama ba tare da yin tunani ba, inda ya fake da jimamin mutuwar mahaifiyarsa.

Wasu ya kashe su ne saboda sun ci zalinsa a lokacin da yake ɗan yaro, yayin da wasu kuma aka kashe su saboda ba su nuna alhini sosai game da rasuwar mahaifisarsa ba.

Shin Matsala ce a Kira Shaka ‘Baƙi ko kuma Napoleon ɗin Afirka?

Gwarzon Soja ne ɗanbaiwa na Afirka ba baƙin Napoleon ba.

Me ya sa Ba Za a Ce da Napoleon Farin Shaka Ba?

Bai taɓa zuwa Turai ba kuma babu wani Bature da ya koyar da shi abubuwan da ya yi a fagen yaƙi. Sun fito ne daga baiwar da yake da ita.

Ko har Yanzu Shaka Zulu Ya na da Tasiri a Yau?

Shi ne jigon haɗin kan Zulu. Jam’iyyar Inkatha Freedom Party, wadda ta mamaye Kwazulu Natal ta danganta kanta da Sarki Shaka a matsayin tushenta. Sarakunan Zulu da al’ummarsu su na yin mubaya’a ga Sarautar Sarki Shaka har zuwa yau.

Maxwell Zakhele Shamase, ƙwararren masanin tarihin Zulu ya na da digirin-digirgir a tarihi da siyasar wannan zamani da kuma tarihin al’ummar Zulu. A yanzu haka ya na rubuta wani Littafi a kan Sarki Shaka. H Shamase shi ma Malami ne kuma Shugaban Tsangayar Koyar da Tarihi a Jami’ar Zululand wanda har ila yau ake kira ‘Unizulu.’

MADOGARA

Shawarwari da suka danganci kimiyya a wannan ƙasidar, an same su ne daga masana tarihi Farfesa Doulaye Konaté, da Dr. Lily Mafela, da Farfesa Christopher Ogbogbo, da DW, da kuma Gidauniyar Gerda Henkel.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen