Kimiyya Da Fasaha

Me Kuka Sani Game da Fasahar Binne Gawa ta Zamani?

Yanzu za a iya Binne Gawar Mutum a cikin Ruwa ta zagwanye a maimakon binne wa a cikin Ƙasa ko ƙonawa.

Binne Gawar Mutum da aka sani tun fil-azal ko kuma a gargajiyance ya kasance hanya ɗaya tilo wurin rabuwa da Gawar Mutane ko Dabbobi.

A cikin ƴan shekarun nan binne Gawa cikin Ruwa da ake kira “Aquamation” ya fara jan hankalin jama’a.

A ta wani hanyar ana kiran wannan tsarin binne Gawar da “Alkaline Hydrolysis” ko “Water Cremation.”

Aquamation, tsarin binne Gawa ne da ya ƙunshi sanya Gawa a cikin Akwati (Vessel) da aka matse da Iska (pressurised) cike da gaurayen Ruwan Zafi da sinadarin ‘Potassium hydroxide.’

Ana dafa Gawar ne bisa zafin ma’aunin Degree Celsius 90 zuwa 150 ta yanda zai zagwanyar da duk wata Tsoka ta jikin Mutum cikin awanni, ya bar zallar ƙasusuwa.

Sai sauran ƙasusuwan a busar da su, a niƙe su zama garin hoda.

Kamar yadda binciken masana ya fitar, ya nuna cewar, Aquamation ba ya fitar da sinadaran da suke lalata muhalli.

Har ila yau, binciken ya nuna cewa, wannan tsarin binne Gawar ita ce mafi dacewa da muhallin mutane ta hanyar amfani da Ruwa da Sinadarin Alkaline Solution don zagwanyar da jikin Gawa ya bar zallar Ƙasusuwa.

Ruwan da aka yi amfani da shi wurin dafa Gawar za a iya amfani da shi a Gonaki a matsayin Taki na ruwa.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Kimiyya Da Fasaha

Yadda Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial Intelligence za ta Shafi Ayyuka a Afirka

Bankin ci gaban Afirka (Africa Development Bank) ya yi hasashen cewa kimanin Matasa Miliyan 100 da ke Nahiyar ba za
Kimiyya Da Fasaha

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙirar Matasa

Taron Ƙolin Masana Kimiyya na Ƙasa da Ƙasa na 2024 na Haɓaka Ƙarfin Ƙirƙire-ƙirƙiren Matasa Daga: Amina Xu An gudanar