Ƙamusun Turancin Ingilishi na Oxford ya faɗaɗa yawan kalmomin da ke ƙunshe a littafin inda ya ƙara yawan su da wasu sabbin kalmomi da aka fi yawan amfani da su a Najeriya.
Daga cikin kalmomin da aka ƙara akwai wasu fitattun kalmomi kamar “Japa”, da “Agbero “, da “Eba”, da “419”, da kuma “Abi.”
Waɗannan kalmomi, da suka yi fice a tsakanin ƴan Najeriya, na nuna yadda Harshen Pidgin ke ƙara samun karɓuwa a Duniya.
An saka kalmomi kamar; “Japa,” da “Jand” a cikin ƙamusun a matsayin Suna da Aikatau, abin da ke bayyana yadda ake amfani da kalmomin ta hanyoyi da dama.
Kuma bisa al’adar ƙamusun, su ma waɗannan sabbin kalmomin, an bayyana yadda mutum zai furta su, daidai da wani abu da zai taimaka wa waɗanda ba ƴan Najeriya ba su iya faɗar su.
Kingsley Ugwuanyi, Jami’i na ƙamusun Oxford a Najeriya, ya wallafa sanarwar ƙarin wasu kalmomin Najeriya cikin ƙamusun a shafinsa na LinkedIn, inda ya yi alfahari da yadda ya bayar da gudunmowa a ƙamusun Oxford na baya-bayan nan da aka sabunta.
“Ina farin cikin sanar da cewa, Ƙamusun Oxford English Oxford Languages ya buga sabon babi da ya ƙunshi wasu kalmomi da aka ƙirƙira a Najeriya da suke bayyana kyawun al’adun Ƙasar da kuma fikirar al’ummarta da kuma yadda muke iya sarrafa Harshe wajen furta kalamai a matsayinmu na ƴan Najeriya,” kamar yadda Ugwuanyi ya rubuta.
Ya ƙara da cewa, “A wannan karon, ba iya gabatar da galibin kalmomin na tsaya ba, har da samun dama ta musamman ta bayar da yadda za a furta su! Don haka, idan kuka karanta Ƙamusu a intanet, kuma kuka latsa yadda ake furta kalmomi, za ku ji muryata, ina koya yadda ake faɗin su.”
Ga Jerin Sunayen da Aka Ƙara Cikin Ƙamusun na Oxford
Japa, kalma ce da ke nufin “Kwararar ƴan Najeriya zuwa wasu ƙasashe (musamman waɗanda ke Turai ko Arewacin Amurka) don ƙaro kaaratu, da samun aiki, ko ma samun damarmaki da suka shafi yadda za su bunƙasa samunsu.”
Agbero: “Mutum (yaro ko matashi) ɗan tasha a tashoshin Mota inda suke karɓar kuɗaɗe daga fasinjoji da direbobi kuma suke yi wa Fasinjoji iso a Mota.”
Yahoo: Zamba da ake aikatawa a intanet galibi ta shafi yaudarar mutane su biya wani kaso na kuɗin wasu kayayyaki waɗanda a ƙarshe ba za a samar ba. Akasari ana ninka kalmar ta zama yaho yahoo.
Ga Ƙarin Wasu Kalmomin da Kuma Ma’anarsu
- 419 – Damfara.
- Abi – Haka ne.
- Adire – Kalar Yadi da ake samar wa a Kudu maso Yammacin Najeriya.
- Area Boy – Mutumin da ke tatsar Kuɗi a hannun Jama’a ko sace-sace da ta’amali da Ƙwaya.
- Cross-carpet – Ɗansiyasa ya sauya sheƙa, misali; fitattun ƴansiyasa sun sauya sheƙa.
- Cross-carpeting – Aikatau na sauya sheƙa, misali; Ƴansiyasa na yawan sauya sheƙa.
- Eba – Aau’in Abinci ne da ake yi da Garin Kwaki.
- Edo – Mutanen da suka fito daga Benin, a Kudancin Najeriya.
- Gele – Mayafi.
- Jand (Suna, Aikatau) – Ƙasar waje.
- Janded (Lamirin lokaci) – Mutumin da yake tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashen.
- Kanuri – Ƙabila ce a Arewa maso Gabashin Najeriya.
- Kobo – Sulalla.
- Naija – Takaitaccen sunan Najeriya.
- Suya – Tsire.
- Yahoo Boy – Mai damfarar mutane a intanet.
- Yarn Dust – Soki burutsu.