Ƙasashen Afirka Da Ke Gefen Sahara Sun Yi Asarar Dala Biliyan 1.56 Sakamakon Katsewar Intanet A 2024.
Ƙasashen da ke gefen Sahara sun yi asarar Dala Biliyan 1.56 sakamakon katsewar Intanet a shekarar 2024, a cewar wani sabon rahoto na ‘Top10vpn’, wani shafin Intanet da ke leƙe a tsakanin Ƙasa da Ƙasa.
Hakan shi ne kashi 19 cikin 100 na jimillar Dala Biliyan 7.69 da aka yi asara sakamakon katsewar Intanet a duk Duniya, wanda kuma hakan ya nuna cewa, an samu ragowa da kashi 10 cikin 100 daga Dala Biliyan 1.74 da aka samu a shekarar 2023.
A cewar rahoton, an samu katsewar Intanet sau 28 a Ƙasashe 28. Daga cikin Ƙasashen da lamarin ya shafa, 13 Ƙasashen Afirka ne: Sudan, Habasha, Kenya, Aljeriya, Guinea, Mauritania, Senegal, Mozambique, Chadi, Mauritius, Tanzania, Papua New Guinea, da Equatorial Guinea.