Rana Kamar Ta Yau

Fara Ambatar Sunan Najeriya a Karon Farko a Duniya, 1897

A Rana mai kamar ta yau, takwas ga watan Janairun 1897, Flora Shaw, wadda ta kasance ƴar jarida daga Birtaniya, kuma wace ke kula da yankunan da Birtaniya ke yi wa Mulkin Mallaka, ta raɗawa Ƙasar suna ‘Nijeriya,’ a yayin da ta ambaci sunan a cikin Jaridar The Times London.

Yankin Arewa da na Kudanci waɗanda daga baya Lord Lugard ya haɗe su a Ranar ɗaya ga watan Junairu 1914, saboda dalilai na tattalin arziki kawai Gwamnatin Turawan Mulkin Mallaka ta Birtaniya ta yi wa laƙabi da Najeriya a shekarar 1900.

Haɗewar Kudu da Arewacin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sir, Lord Fredrick Lugard da aka fi sani da Gwamna Lugga, lokacin da ake ƙarƙashin Mulkin Mallakar Ingila, shi ya kawo samuwar Ƙasar Najeriya a shekarar 1914.

Matar Gwamna Lugga Lady Flora Louise Shaw, wadda ƴar jarida ce, ita ta sanya wa Ƙasar suna Najeriya, aka tabbatar da shi a shekarar 1914.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani